Sashe 50
Dr Sultan Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
ta manya, idonsa akan Sultan d'in, cikin murmushi yace Sultan anzama Ango. Alhamdulillahi munje anyi maganar aurenka da mahaifinta Sun yanke mana ranar d'aurin aure nanda wata biyu , Sun yanke sadaki naira dubu 50k kacal, dan albarka ake nema acikin auren. Sultan yakuma yin k'asa da kansa, dama can shi mutumne mai kunya, Mommy tayi murmushi kana ce Allah ya nuna muna," Amin" cewar Daddy. ★★★★★ __________★★★★ Sultana na zaune ta saka waya a gaba tana magana tana kuka," Nas ya sanyi!! Nas yanzu haka an saka ranar Aure na!!..daga can ɓangaren Nas yake ya sauke Nannauyan Numfashi kana yace ,"Bazan iya jure reshin ki ba hawaye na baza iya wonke damuwar da Zuciya zata shiga ba hawayena sunyi ƙanƙanta matuƙa su hana rayuwata gangar jikina ban taɓa sonki ƙasa da yadda zan iya rayuwa batare da ke ba ina sonki Sultana!!!.. Soyayyarki a cikin jinina take, ban taɓa tunanin zan tsinci kaina a cikin wannan yanayi ba, zan kasance cikin sonki har Abada,kin koyamin soyayya,kin koyamin farin ciki,kin koyamin dariya, Amman kin manta baki koyamin yadda zan manta dake bayan kin rabu dani💔, ki talla fawa rayuwata data tsunduma akan tsakanin kyaunar ki, ki tausayawa Zuciyata da ta shagala akan tsakanin Soyayyarki, ki taimaki idanuna da sauraren zazzaƙar Muryar fusakar ki, ina sonki Sosai Sultana!!!!!." Wani irin matsanancin kuka Sultana ta fashe dashi Zuciyarta na mata zafi kaman zata fashe. Cikin shekarar kuka tace ," Nas Bazan iya butulcema iyayena ba, Nas mesa tun lokacin baka bayyanar da kan ka a wajen iyaye ba? Nas bana son fushin iyayena Nas Nima Kai banza iya zuje reshin kaba, Amman dole zanyi haƙuri!!! ta ƙara sa maganar cikin raunin Murya, _________★★★★_____ "Ya Sultan Daddy yace ka kaini wajen Anty Sultana, "my little sis, ki bari sai gobe na kaiku ku yini a can, nan take Salma ta ɓata fuska kaman Zatayi Kuku," Ya Sultan Nidai yanzu nake so!" "Ya Babba tun ɗazu ta isheni sai an kaita wajen Anty Sultana ta ga Baby, Sultan ya sunkuyar da kai ƙasa cike da Kunyar Mahaifiyar sa, " Jeki shirya da sauri Salma ta wuce ɗakin jim kaɗan ta dawo.." Ina Salim? "Ya yi bacci,haka suka wuce, tunda suka fita Salma ke mai mai yawa Sultan mafarki har suka iso gida, a farfajiyar gidan ya yi Parking kana ya kira Haydar bai ɗaga ba har kiran ya tsinke,Khalil ya kira bugu biyu ya ɗaya, nan take sai ga Khalil ya fito fuskarsa ɗauke da Murmushi,"Ya Sultana kazo a Sa'a ko ga Anty Sultana can ta birkice muna" gaban Sultan yay matsifar tsinkewa, Amman ko kaɗan bazakace ga yanayin da yake cikiba, tare suka wuce cikin gida. __________Sultana zaune a ɗakin tun bayar gama wayarta da Nas. ta ɗora hanunta saman kai ta riƙe. Cusashi tai a tsakanin cinyoyinta jikinta na wani irin tsuma. Ga kanta ya fara sara mata sama-sama. Duk yanda taso ta daure ta kasa. Dan haka cikin ƙarfin hali ta shiga laluben wanda ke a kusa da ita. dai dai lokacin kuma Meena ta shigo ɗakin Cikin sa'a ta damƙo hanun Hankali tashe Meena ta dubeta, sai kuma yanda taga jikinta na karkarwane ya sakata ambaton ‘Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un’ da ƙarfi.da sauri Abba da Mami suka shigo ɗakin.. Sultana ta damƙi hannun Abba tana cigaba da jujjuya kanta da fisgar numfashi a wahalce. A hankali take magana wadda idan ba'a kusa da ita kakeba ma bazakajita da ƙyau ba. “Abba kaina, kaina zai fashe Abbah. Kamin addu'a kaina zai fashe, Innalillahi... Abbana zan mutu..". Bazaki mutuba Mamana kinji, daina magana kiyita addu'a a ranki insha Allah bari na kira Doctor kinji”. Ya ƙare maganar da saka ɗan yatsa ya ɗauke hawayen da suka tsatstsafo masa saman fatar ido. Meena da Mami ma hawaye sukeyi. Dai lokacin Khalil ya shigo ɗakin,"Abba ga Ya Sultan nan yazo tare da Salma, Abba ya sauke sassanyan Nunfashi tare faɗin ,"Alhamdulillahi!!... "Don Allah ayi a hankali kar a tashi da kaka daga Bacci. "In sha Allah Abba, tare suka fito da Sultana zuwa Palo. Tunda yay sallama Abba da Mami suka zuba masa idanu cike da jin daɗin isowarsa a kan lokacin da ya dace. Cikin girmamawa ya gaida su . Suma sun amsa masa da kulawa Meena harda ƴar tsokana. Kaɗan gefen bakinsa ya motsa alamar murmushi yana Lumshe ido. Abba ya nuna masa alamar ya zauna anan. Bai musaba ya zauna idanunsa akan Sultana da har yanzu take riƙe da kanta. Sai da yay mata kusan kallon minti ɗaya da wasu sakanni sannan ya ɗago. Ɗan kallonsu yayi sai kuma ya sake maida idanun nasa kan Sultana. Hannunsa da Sultana ta riƙo ne ya sakashi saurin juyawa gareta. Cikin yanayin ciwo ta sake matse lallausan tafin hanun nasa cikin nata tare da ɗorasa bisa kanta, “Abba ka riƙemin zai fashe”. A hankali Sultan ya lumshe idanunsa ya sake buɗewa a kanta. Baiyi magana ba, bai kuma janye hannunsa data ɗora akanta ba ta danne da hannunta kuma. Salma gabaki ɗaya jijinta yay sanyi ganin Halinda Sultana take ciki. "Tunda ga Shi yazo mu barshi ya yi aikin sa ko, cewar Abba Janye idanunsa yay daga kallon da yakema Sultana, sai dai kafin ma ya ɗago su duk sun fice. Meena da Haydar kawai aka bari. Baice komaiba sai hannunsa da yay ƙoƙarin janyewa daga kanta. Amma sai ta sake riƙesa da ƙyau tana faɗin, “Abba don Allah karka tafi ka barni, kaimin addu'a kaji Abba”. Sosai tausayinta ya sake lulluɓe su Meena . Sultan ya ɗan matsar da kansa kusa da nata kaɗan, a hankali yace, “Ki daina magana zan baki magani yanzu zai Dena ciwo Kinji, Sultana duk da bata cikin haiyacinta ta gane ba Muryar Abba ne, Hayda buɗe mota na ka ɗauke box a ciki, da sauri Haydar ya fice daga palon jim kaɗan ya dawo hannunsa rike da ɗan ƙaramin Akwati mai kyau , Kallon Haydar Sultan yayi, Please ko zaka iya haɗamin allurar nan?” kasan cewar shima a school of nursing yake karatu . “to ya Sultan" ya jawo box ɗin. Wata irin zabura Sultana da zancen ya shigarma kunne tayi, batare da sun fargaba suka ganta tsaye bisa ƙafafunta jikinta na rawa. “Bana son allura, Abba! Abba! banason allura...” ta faɗa a wahale tana riƙe kanta da hannu biyu duka tai baya luuuu zata zube. Cikin zafin nama Sultan ya miƙe tsayen shima, hakan yasa Sultana faɗawa jikinsa nata jikin na wani irin karkarwa. Saurin riƙota yayi shima yana faɗin, “ Please calm dawn!”