← Book details Dr Sultan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 54

Sashe 33

Dr Sultan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

komai. Duk da akwai gajiya tattare dasu haka suka wuce massallaci sukai isha'i da asham. Kafin su dawo kowa ya nema makwanci... Washe garima haka suke tafiyar da rayuwarsu. Cikin tsari da kuma samun damar hutu da ibada dan ribatar watan Ramadan ɗin. A hankali aka fara nisawa cikin watan Ramadan, kwanaki suna suka ci gaba da shuɗewa da kaɗan-kaɗan. Yau wunin azumi na 20 kenan. Da safe duk su Daddy sun wuce masallaci wajen tabsir, Sultan Ya dawo daga sallar Azahar ya shiga gida sai ya ji ƙanshin abinci. Abinci a watan Ramadan? Ya juya inda ya ke jin ƙaran sokali . Ta barraje a ƙasa tana cin jollof ɗin taliya da daffen kwai. Ɗago ido ta yi ta kalleshi hannunta ɗauke da sokali totse da abinci. Zuwa yai ya zauna bai ƙara cewa komai ba. Lokaci zuwa lokaci yana ɗaga ido ya kalleta. Shi mamakin yadda ta ke cin uban abincin nan da gani Zaiyi taji sosai ke. Ko za a matse shi ba zai iya cinye abincin nan. dai dai lokacin Kuma Meena ta shigo Palon riƙe da wayar Sultana,"Anty Sultana Jidda ta kira Video call," Ya Sultan Sannu da zuwa , " Lafiya lau ya bata amsa fuska a sake, a hankali mike tare da barin Palon, "Anty Sultana kiran zai katse fa, "idon na kammala zan kirata, haka ko akayi bayan ta kammala ta kirata bayan sun gaisa daga can ɓangaren Jidda tace,"Daughter wlh Asbitin nan ba daɗi Dr Sultan baya nan ke ma baki nan duk dai Dr Aryan na iya ƙoƙarinsa da Dr Nasir! Gaban Sultan ne ya yi mugun tsinkewa," Nasir kuma? "Daughter Lafiya kin san shi Hlm?" A'a ta faɗa da ɗan sauri. "Sabon Dr ne bayan ta fiyar ku da kwana biyu ya fara aiki a Asbitin nan.." Toh" daga suka ci gaba da hira, sun jima suna waya. Bayan sunyi sallama Sultana ta kira Mami Video call bayan sun gaida Mami ta miƙa ma Kaka wayar suka ci gaba da hiya cike da kewar Juna.... Ana idar da salla suka fito, kitchen suka nufa ita da Meena da Sultana Suka fara aikin buɗa baki sunayi suna kimtsa komai. Kafin shida ta cikama sun gama komai... Haka dai komai yaketa wakana cikin aminci da tsari. A wurin al'ummar Annabi kowa ya nitsu ya maida hankali kan ibada domin neman rabauta. Ƙarfe takwas dai-dai suka shiga kitchen dan yin aikin sahur. A kwana a tashi Babu wahala wajen Allah , dan gashi yau saura kwana biyu kacal sallah, kowanne yanki na musulmi suna cikin shirye-shiryen ta da yin bankwana da azumin watan ramadhan Yayinda su Sultana keta shirin dawowa suma a ranar sallah. Bayan Isha'i tana zauna a palon tana waya da Jidda Konciya tayi bisa 3 str tana kallo wayarta na hannunta. Tana ba Jidda Labarin NAS dake Turo mata massage duk safiyar Allah.. A haka bacci yayi awon gaba da ita. Can Cikin bacci take jin alamun kamar mutun na tsaye a kanta, cikin magagin baccin ta buɗe idonta. Gabann Tv ta ganshi ya kashe TV kana ya juyo ya kalleta a fizge yace. "Ba Aiki sai kallo da bacci". Jin haka yasa ta gyara kwanciyar tare da murguɗa baki. Shi kuma tuni ya wuce ɗikinsa... Can kuma ta miƙa ta nufi ɗaki ta ɗan kwanta kafin lokaci sallah tuhajju tayi.... Washegari Mommy ta tamusu ƙunshi jan lalle irin na larabawa.. Washegari haka suka niyi suna aiki tuƙuru .. Washe gari aka tashi da azumi na talatin. Allah cikin ikonshi aka kaishi lafiya.Watan Shawwal ya baiyana Ramadan ya tafi kuma sai mai nisan kwana, Ana idar da sallan isha'i da yawa suka fara ɗawafi.A nitse bisa tsari suke ɗawafin sunje ƙafa biyu ana uku sun isa dai-dai. Maƙama Ibrahim. Sultan ya juyo kanshi ya kalli gefen damanshi da sauri cikin tarin mamaki al'ajabin Fuskar mutumin da ya ga ya wulgawa a idonshisa. Zuciyarsa tayi mugun buguwa da ƙarfin gaske. A hankali ya dai dai ta natsuwarsa kana ya ci gaba da ɗawafi Yana mai bin bayan tawagar mutanen da yaga fuskar wannan mutumin a cikinsu. Idonshi yaketa karkasawa amman ina ya kasa sake ganinshi. Zuciyarshi nike da mamaki.Haka yaci gaba da ɗawafin.Saida sukayi. Kana suka wuce gida gabaki ɗayan su. Washe gari da safiya.Duk kan al'amur musulmai na duniya suna farin ciki da ranar salla.Manya da yara duk anata shirin zuwa idi. A dukkan ƙasashen duniya. A gaggauce sukayi wonka kowa yayi shirin idi.ko waccesu sanye cikin Aba mai matsifar kyau, Ƙarfe tara saura kwata duk suka fito falo. Tuni lokacin kuma liman har ya fara huɗuba.Suna fita su mata sukayi gefen mata su kuwa maza sukayi gefen maza. Lokaci da aka kammala salla sosai Sultan ke baza ido ko zai sake ganin wancan mutumin amman ina.. (Shiko wannan waye?) Kai tsaye suka wuce gida, suka ci Abinci cikin kwanciyar hankali, "Kuyi sauri mu kammala ƙarfe 1:30 jirginmu zai ɗaga, cewar Daddy. Dai dai lokacin muka massage ya shigo a wayar Sultana.. *Aminci Allah ya tabbata a gareki yake farin ciki raina! Ina fatan kinyi Salla lafiya, Allah ya mai mai ta Muna, Allah kuma ya ƙarɓi ibadar mu. daga NAS!!.* A karon farko Sultana ta saki Murmushi lokacin da ta kammala karanta saƙon, a karo na farko ta maida mai da Amsa. *Amin Na gode!* (Haba Sultana daga ganin Sarkin fawa sai miya tai daɗi😉🧐🤣🤣🤸,) Nan suka soma shiri.karfe ɗaya dai dai suka wuce Airport..Bayan duk matafiya sun shiga, jirgin ƙasar Nigeria wanda zai sauƙa a kano.A hankali ya zauna. Ya Meena na gefenshi. Riƙe da hannunsa Kasan cewar yana kusa da window ne, ya ɗan juya yana kallon mutanen daketa hada-hadar nufar inda jiragan ƙasar su jihohinsu suke. Can cikin wasu ayarin mutane maza da mata ya hango wannan fuskar da ya gani. Sun nufi can ciki suna tafiya yankin da jiragen ƙasarsu. A hankali yake jin zuciyarsa na harbawa da sauri-sauri. Hannu Meena ya damƙe sosai. Kana ya sauƙe Nannauyan Ajiyar kana, Cikin tarin mamaki ya bishi da kallo tabbas badon jirginsu ya fara ƙugin tashiba da ya fita yaje ya tabbatar da fuskar dattijon da yake hangowa. A haka dai suka ɓacewa ganinshi. Kana jirginsu ya ɗaga zuwa Kano..... ______________ *Najeriya* Ƙarfe 7:20 jirginsu ya sauƙa, a hankali suka fara fotowa kai tsaye wajen motocin suka nufa, A tsanake suka fice daga Airport. Mommy da taga a canza hanya zuwa gida ta Kalli Daddy,"Lafiya?" Kai kwai ya ɗaya mata. Abban tuni sun kama hanya gida.. Anguwace da bata da maraba da a cikin turai saboda rashin hayaniya da haɗuwarta. Ko ina ƙwanyar yake da wutar nepa tamkar rana. Dai dai lokacin kuma suka iso wani tantsamem gida mai matsifar kyau.Dogon building ne mai matukar kyau da tsaruwa...sannan yanada girman sosai kusan part biyu.. Mommy ta saki baki tana Kallo cike da mamaki, "Abban Sultan ina ne nan?" tayi maganar cike da damuwa, "Sabon gidan mu ne!" da sauri Mommy ta ware manyan idanunta ta kalli Daddy,"Sabon gida kuma?" Kai ya gyada mata, "Abban Sultan Amman Ai.... Ya isa. Mommy ta sauke sassanyan Nunfashi tare da faɗin,"shike nan, Tsarin ginin gidan tsarine, wanda ko a ƙasashen turawa na musamman ne, Ƙaton gidane sosai an ƙawatashi da shuke shuken ƴan ƴan itatuwa kala kala ga ƙasansu kuma, wasu tsirran fulawowi ne masu masifar kyau da sanyi masu collor's Pink da yellow. da wajen shan iska na musamman mai masifar kyau da ɗaukar hankali.. Salma da Salim ko sai tsalle tsalle suke a farfajiyar gidan, A ɓangaren Sultan ma sosai gidan ya masa kyau, kai tsaye suka wuce gidan cikin gida Cikin Part ɗin nasa kuwa, wani tamfatsetsen parlour ne mai kyan tsarin ƙasaitattun kujeru da labulaye da kayan wuta, komai na ciki farine. Numfashi Mommy ta sauƙe lokacin da ta gama ƙarewa gidan da lukkunan gidan kallo, (Hmm sabuwar duniya sabuwar rayuwa🥂🙌💃🥰 ) Ɗaki Ukku ne a cikin palon, ɗakin Salma da komai naci pink color ne ya yi Masifar kyau, sai ɗakin dake liƙe dashi ɗakin Salim komi blue da kayan wasan shi, daga gefe kuma ɗakin Ihsan ne,suka ƙarasa madaidaicin falon daya gama haɗuwa, yanata wani tattausan ƙamshi mai daɗin shaƙa da kwantar da zuciya. zuwa wata ƙofa dake a cikin falon. ɗaki ne mai matsifar da tsaruwa komai na cikin ɗafin fari ne ," Masha Allah shine Abinda Mommy ta furta. Sultan tsab ya ƙare wa ɗakin Kallo dai lokacin kuma idanunsa suka sauka kan wani makeken hotonsa dake manne yana sanye da Fararen kaya na likitoci da wata na'ura sarkafe a kafaɗarsa daga kasan hoton An rubuta *DR SULTAN*. a hankali suka fice daga ɗakin kai tsaye suka haura sama. Nan ma Wani haɗaɗɗen Palo ne da ɗaki Ukku. Ko'ina ya yi Masifar kyau... Sultan ya kalli Daddy cikin sanyi Murya yace ,"Daddy Allah ya ƙara Azziki mai Albarka, Allah ya ƙarama tsawon rai mai Albarka!" "Amin my Boy!" Sultan ya gargaɗi ƙannen nasa zuwa palon ƙasa.. aiki Mommy kaman jira take su bar wajen, ta wa Daddy kyakkyawar ruguma tare da manta mishi kiss. A hankali ya Lumshe idanunsa kana ya buɗe a tsakiyar idanunta. Cikin tsantsan farin ciki Mommy tace ,"Na rasa dame zan saka ma Abban Sultan kamin komi A rayuwa, ka ilimarta dani! Ka ciyar dani! Ka suturtani ka min muhalli! Kamin gata! Abban Sultan, ina rokon Allah ya saka ma da gidan Aljana, Allah ya jikan iyayenmu Allah ya ƙarama Azziki mai Albarka ina roƙan Allah ya shayar da kai ruwan Aljana!" ta karasa maganar cikin raunin Murya, a karon farko a rayuwarta tun zaman da shi ya Amsa da "Amin!" A hankali ta sake lafewa a jikinsa tana shaƙar dadɗan khamshi mai daɗi. Ɗaukar yayi Cak zuwa ɗakinsa cike da so da kyau da kewar Juna suka faɗa duniyar ma'aurata.... ____________ Wannan littafi DR SULTAN na kuɗine, yana ɗaya daga TITAN'S OF TALENT WRITER'S, idan kana buƙata kaima waɗanan numbers ɗin magana Zaku biya kudinku acikin wannan asusun na banki👇👇 1490318334 Sadiya Attahiru kaoje Access bank ,sai a turo shaidar biya ta wannan number 08149979652. Nagode🤗..... ★★★....... Tunda suka fito daga Airport ɗin kai tsaye suka wuce gida, da mamaki ya Abba ya riƙa kallon gidan sa daka sauyawa fenti mai kyau, koda suka shiga cikin cikin gidan ko'ina tsab Motorsu na gama tsayawa Sultana bata tsaya
Chapter 33 · 0% Book details