Sashe 47
Dr Sultan Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
nuna alamar nutsuwar jin daɗin yanda aikin ya kasance suka sanar da su zasu iya tafiya gida. Dan Doctor yace babu wanda zai iya ganin Sultana a yanzu, hasalima ba'a buƙatar kowa a gareta. Duk da ba haka suka so ba sun gamsu da bayanin Doctor Sadiq... "Kulsum mu tafi gida ko zuwa anjima sai Mudawo.... Jiki a mace suka wuce gida ... ______★★★★★★_______ Abba ya kalli Kaka Ɗan Murmushin ƙarfin hali tai masa ta duƙar da kanta. Shima sai ya ɗan murmusa cike da jarumta ya kirayi sunanta a hankali. ɗagowa tai ta sake kallonsa. Muryarsa a sanyaye yace, " an kammala Aiki cikin Nasara Mama, ki Kwantar da hankali ki!!" inason mu ɗauƙi komai matsayin jarabawa, Ƙwallar da suka cika mata idanu haɗiye da ƙyar, ta maida kanta ƙasa dan karya gani tana faɗin, “Allah ya bata lafiya!!" “Amen ya rabbi” ya amsa mata shima. Shiru ɗakin yayi kowa na nazari a zuciyarsa,. Washe gari tunda safe Sultan ya iso Asbitin ko da yaje ɗakin da Sultana take har yanzu kwance take tana bacci cikin wani irin yanayi. tsowan mintuna goma Sultan na tsaye yana kallonta... A hankali ya sauke Nannauyan Ajiyar zuciya kana ya fice daga ɗakin kai tsaye ya wuce gida... ★★★★★★★ sai Kusan ƙarfe Ukku na rana Sultana ta farfaɗo. Dr Sadiq dake tare da ita dan duty ɗin rans ne da shi yay saurin kiran Dr Sultan ya sanar dashi, Cikin ƙanƙanen lokaci ya shigo asibitin. Tsabar yanda ransa ke a jagule sai ya toshe idanu da baƙin Glasses da yay masifar sake fiddo masa ƙyawun fuskarsa da kwarjinin saTunda ya shigo asibitin baiyi magana da kowa ba. Ko gaidashi da Nurses suke da sauran ma'aikatan hannu kawai ya dinga ɗaga musu kansa a ƙasa ya rufe rabin fuskar da p-cap bayan glasess ɗin.... Ɗakin da Sultana ke a kwance ya tura a hankali ya shiga da sallama ƙasa-ƙasa. Dr Sadiq da Nurses guda biyu dake a tare da shi suka amsa suna ɗagowa. Da girmamawa Nurses ɗin suka risina suna gaishesa. Batare da ya amsa musu ba suma ɗin ya ɗaga musu hannu kawai. Kafin ya miƙama Dr Sadiq hannun suka gaisa.. A hankali ya juya kansa zuwa ga sashen da kanta Sultana ya ke. Ya ɗan ranƙwafa kanta ƙaɗan ya janye wani igiyan na'uran dake a gefen kanta gab da kunne. Yanda ƙamshin turarensa ya buga mata hancine ya saka ƙirjinta harbawa. Buɗe idanun nata tayi da ƙyar saboda bala'in nauyin ciwo da sukai mata. Dai-dai Sultan ya dubeta shima yana ƙoƙarin zare glasess ɗin idonsa. Kallon ido cikin ido sukaima juna, duk da ita ɗin dishi-dishi take ganinsa hakan baisa ta gagara ganesa ba. Wani irin juyawa kanta ke mata, daga ciki tanaji kamar ana karta mata ƙarfe, zabura tayi, ta yunƙura zata tashi Sai kuma tai saurin dafe kan nata tace, "Wayyooh kaina!’. Sultan da shima zuciyar tasa ke wani irin harbawa, da sauri ya wani ɗauke idanunsa daga kanta cike da basarwa, tamkar bai fahimci halin da take a ciki ba. Yanda jikinta ke wani irin ɗan karkarwa ga kanta data riƙe da duka hannayenta tana jujjuyawa ya saka Nurses ɗin nufarta da sauri tare da Dr Sadiq Sultan dai na tsaye baiko motsaba. Sai dai yana kallonsu ne ta ƙasan ido. Yanda duk suka so Sultana ta nutsu hakan ya gagara, dan ganin Sultan ɗin ya sake dawo mata da komai, “Live her.” ya faɗa a hankali tamkar ba shine yayi maganar ba. Baya Nurses ɗin suka ja domin cika umarninsa, amma tausayin Sultana fal ransu. Dr Sadiq ya yi ƙoƙarin riƙo hannun Sultana data riƙe kanta da shi gam ya keyi. A bazata yaji an riƙe masa hannun lokacin da yake gab da ɗorasa saman nata. Sosai mamaki ya kama Nurse's Sultan ya fiske abinsa tare da sake tsuke fuska tamkar ba shine ya aikata ba. Sai tura tattausan nasa hannun yayi ƙarƙashin kan Sultana da dogon gashinta ke a tsefe duk ya baje a saman filon. Da sauri ta sake buɗe idanunta, dan kusancin da suka samu gaba ɗayansu neman haifar da barazana yake a bugun Zucikatan su, cikin rawar ji kinta daya ƙaru ta sake buɗe baki zatai magana, sai dai kuma hakan kamar da wuya a gareta. Dan saɓanin yin maganar sai hawaye sharrrr!! Suka fara bin kumatunta. Yanda damshin ruwan hawayen nata suka sauka bisa fatar hannunsa ne ya sakashi lumshe idanu yana wani jan numfashi da sassarfa. Sai kuma a hankali ya janye hannun nasa daga cikin kanta dama jikinta gaba ɗaya ya ɗan matsa baya yana Lumshe ido.. idanu da ya zubama Sultana da jikinta ke Karkarwa a hankali, har zuwa yanzun kuma riƙe take da kan nata da duka hannayenta tana ɗan mirginashi bisa filon. Kusan mintuna biyu yana kallon nata, kamar yanda su Doctor Sadiq ke kallonsa a tsorace, kafin ya ɗauka file ɗin Sultana yaja da baya daga gaban gadon Ya shiga buɗe takardun dake a ciki file ɗin yana bin rubutun ciki daki-daki da nazari a nutse. Su Dr Halima duk sun rikice, sai dai sun kasa fahimtar wane taimako ya dace su bata ne. Dawowar da yayi gaban gadon riƙe da file ɗinne ya sakasu zuba masa idanu su duka. Ya ajiye file ɗin a saman drawer'n gefen gadon da take sannan yayi magana a ɗan kausashe yana kallon Sultana " ki nutsu" wani irin masifar zabura zata miƙe. Cikin sassarfa Dr Halima ta ƙaraso ta tareta. Da ƙyar ta iya dannata saman gadon ta kwantar, duk da hakan kuma fisge-fisge takeyi har yanzun. Batare da Sultan , razananniyar ƙara da ta amsa duka Word ɗin, Shiko yana tsaye ko gezau, duk da kuwa ƙarar tata jiyay tamkar zata tarwatse kansa. Lumshe idanu yayi ya buɗe a hankali, a hankali ya nufi wajen Sultana ya maida saman gadon, a kallo ɗaya zaka fahimci batama yin numfashi. Sai da yaja bargo ya lulluɓa mata sannan ya maida mata duka na'urorin da ke manne da kanta ɗazun. Juyawa yay yayima su Dr Sadiq alamar su fita. Suna gaba yana biye dasu riƙe da file ɗin Sultana... a ƙofar ɗakin ya tarar da Abba da Mami tsaye sunyi zugum, sosai Abba da Mami sukayi mamakin ganin sa, basuyi tunin shine Dr da aka gaiyata ba, "Abba mu tafi Office" kai tsaye suka wuce Officer...." "Sultan pls ina bukatar ganinta Sultana!!" Sultan da yake wani irin jin kunyarsu da nauyinsu ne yay musu rakkiya har ɗakin da Sultana ke kwance. Ba ƙaramin tashi hankalinsu yayiba ganin yanda aka jajjone kan Sultana da na'urori, Mami harda hawayenta. Basu wani jimaba suka fito. Office ɗin Sultan suka sake komawa. Inda ya sake musu bayanin komai dalla-dalla a nutse. “Abba Alhamdulillah ta farfaɗo, sai dai kuma.......” Sai yay shiru kuma. Cike da dauriya yace, “Sultan ! Sai dai me? Karkaji komai kai min bayani akan duk halin da Sultana take.. Abba tanama da ranta, sai dai dama bawai mun mata aikin ainahin matsalarta bane kamar yanda Dr tai maka bayani ɗazun kafin mu taɓata. Aikin da mukai mata zai bata taimakone kawai wajen hana ƙwaƙwalwarta goge komai da take barazanar yi, sannan zai sassauta mata raɗaɗin da takeji a duk lokacin da matsalar ta motsa, insha Allahu zai hana ta iya rasa hankalinta. Nayi tunanin aikin zai bata kariyar da zamu iya ɗaukar kamar watanni ai mata aikin gaba ɗaya, dan dole sai an fita da ita waje, a ƙasarnan bamu da isassun kayan aikin, hankalinsu nakan abinda ya dace suyi bane. To a yanzu dai matsalar dana fahimta dolene ai gaggawar yimata aikin koda nan da wata ɗaya ne insha Allahu, inba hakaba zata iya rasa hankalinta a koda yaushe”. Ɗan rumtse idanu Abba yayi ,cikin jarumta yace, “Shikenan Sultan , duk yanda kake ganin ya kamata akai kayi tunda aikinka ne, . Sosai suka gamsu da bayaninsa, wanda a take duk murmushi ya baibaiye fuskokinsu, suka shiga saka masa albarka da jera masa addu'oin fatan alkairi. Har wajen mota ya rakosu, sai da yaga tafiyarsu sannan ya koma ciki, dan yau a asibitin zai sake kwana saboda Sultana zata iya farkowa a kowane irin lokaci wani Abokinsa dake India ya kira Yana buƙatar a aiko masa da wasu allurai ne masu matuƙar tsada da zaima Sultana amfani da su. Kuma yana buƙatar sune da gaggawa daga nan zuwa gobe idan Allah ya kaimu. Bayan sun gama maganar Sultan ya yi mashi transfer na maƙuddan kuɗi........✍️ _More Comments and share pls_ *Sadeeya Ka'oje ce 💋✍️* *DR SULTAN* (A heart touching love story)