Sashe 26
Dr Sultan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*(T .O.T)* *Breathe in courage, breathe outfear, together we stand* *Alkalaminmu abin alfaharn mu* https://chat.whatsapp.com/CuNxneQ0ONc6x9yn9a16Jj *The beginning* *Page 19-20* _____Da mamaki ya ɗan kalleta ta gefen idonsa, kana ya tsuke fuska yaci gaba da tafiya, kai tsaye ya wuce Office ɗinsa ya fara aikin da ya kawoshi. Sultana da har yanzu ke ta faman jan tsakin takaici ta nufin cikin Asbitin, Nurse's sake tsake a wajen sai faman kwallonta suke cike da mamaki, Jidda tayi sauri riƙo hannuta, tana faɗin,"Daughter Lafiya?" da saurin Sultana ta juyo tana kallon Jidda fuska a tsuke ta ce, "Ba komi Mommy na!" salin halin kawar ta ta, yasa ta yi shiru, Jidda ƙawar Sultana ta re suka yi school of nursing. Kasan cewar tana da sunan haifiyar ya sa take Sultana take kiranta da Mommy. Sosai suke mutunci, "Daughter me a ka Miki Hlm?" Kafin Sultana ta samu damar bata Amsa sai gashi ya fito daga Office ɗinsa Dr Aryan ta biye da shi a baya, taku yake cike da natauwa irin ta zakaran Samari masuji da lokacin ƙuruciya da kwanciyar hankali har yanzu fusakar a tsuke take, ƙoƙarin janye idanunta take daga kallon nasa Karab idanunta suka sauka kan Sunan da ke rubuce a jikin rigarsa DR SULTAN da manyan Rubutu, Cikin suɓutar Halshe ta ce, "don yana Asbitin sa yasa zaiyi wa Mutane tsaye a tsakiyar Hanya" Karaf wannan Maganar ta sauka a hunnensa. ta gefensu ya raɓa ya barta da kamshin turaren sa mai sanyi da daɗin shaƙa. Ko kallon ida take baiyi ba, zaka fahimci da wahala ma ace yaji Abin da ta faɗa.taɓe baki ta yi tare da jan tsaki Jidda ko sai kallon ikon Allah ta ke, dai dai lokacin tawagar Nurse's suka i so wajen Jidda ta ce ina zuwa haka," Dr ne ke son ganinmu ga baki ɗaya, Sultana Uffan bata ce ba. Dan ita takaici yake bata... (Hmm Sultana kenan bari dai nayi shuru 🤣🤣🤸) Nan take kuwa, duk Nurse's suka fara haurawa sama suka shiga babban Hall ɗin nasu, maza gefe ɗaya Mata gefe ɗaya. Sultana da Jidda zaune a waje ɗaya, Cike da natsuwa da sanin darajar kansa ya gyara samansa saman Kujera Dr Aryan na zauna a gefensa, a hankali ya gyara microphone tare da hura Iska a hankali kana ya yi gyara murya," “Bismillahir Rahmanir Rahim!.. Sai kuma ya Lumshe idanunsa tare da sauke sassanyan Ajiyar zuciya cikin sanyi Muryar ya ci gaba da cewa. "Ina mai farin cikin wannan rana mai dinbin Tarihi a Rayuwata! duk yabo da godiya sun tabbatar da ga Allah ma ɗokakin sarki. Ina mai farin cikin zuwan ku Asbitin nan mai Albarka.daga nan yaci gaba da bayanai masu ɗinbin mahimmanci da zasu taimake su gaba ki ɗaya. Gaba ki ɗaya wajen ya yi shiru kowa ya maida hankalinsa ga Sultan dake magana, yan matan wajen ke jin ina a ce su mullake sa a matsayin mijin. Sultan ya sauke sanyayyar Ajiyar zuciy, Kana ya ce,"a kwai mai magana?" Nan wasu suka soma tambayoyi, Shiko yana basu Amsa cikin natsuwa, Kana ya mai da sauran kallonsa ga Dr Aryan dake gefensa cikin sanyi Muryar yace ,"A kwai mai magana a cikin ku?" Duk kan ninsu suka girkiza kai. Dr Aryan ya nuna Jidda tare da fadin ki rufe muna taro da Addu'a,da saurin Jidda ta sunkuyar da kai kaman bata ji me yace ba, tsawon mintu na Ukku, kana ya Kalli Sultana Kai ta juya tare da taɓe baki, "Sultana!Dr Aryan ya kira sunanta,a hankali ta ɗago da kai tana kallonsa dai dai lokacin na kansa, a tsanake ta mike tare da neman dukan natsuwarta ta amshi microphone ta fara Addu'a cikin zazzaƙar Muryar mai cike da natsuwa.. Kana aka tashi kowa ya wuce wajen aikin sa, Sultan kai tsaye office ɗin sa daya amsa sunan Office ya nufa, baka jin komi sai Dadɗan khamshi turaren dana Ac mai sanyi dake tashi, ya zauna saman lallausar kujerar yana sauke sassanyan Nunfashi, dai dai lokacin Dr Aryan ya shigo Office ɗin fuskarsa dauke da murmushi cikin sanyin murya ya ce,"Sir kwai wanda zaka duba yanzu ya yi maganar tare da aje mishi files a gaban sa, kana ya fice daga Office ɗin, files ɗin ya duba kana ya fice daga Office ɗin... ★★★ Bayan Awa Ukku, Fitowarsa kenan ɗakin theater a gajiye.yanda yake tafiya kwai zai tabbatar ma yanayin da yake ciki.tare da Doctors Biyu da suka tayasa Aiki, da Nurse Biyu rike da kayan Aiki.a dai dai lokacin suka ƙaraso Office ɗinsa hand gloves ɗin hannunsa ya cire kana ya jefa a tasar dake hannu Nurse. Hannu ya ɗaga musu alamar su daga ta daga anan a hankali ya tura ƙofar ya shige. Bayan mintuna goma Dr Aryan ya shigo Office ɗin, "Sannu da hutawa Sir ya faɗa cike da kulawa, "Sir ga wasu files" Kansa ya ɗaga masa fuska a ya mutse na Almar gajiya,kana ya ƙara sa kusa da Sultan ya aje mishi wasu files ya fara singing, a hankali Dr Aryan ya mike murmushi na ƙara faɗaɗa akan fuskarsa kana ya ce," Kwai mutun biyu da zaka Duba yanzu kafin kaje Hutun awa biyu,Da sauri Sultan ya ɗago yana kallon Dr Aryan fuska a marairaice kaman Zaiyi Kuka. Dr Aryan ya yi saurin sunkuyar da kai ƙasa yana haɗiye dauriyar dake neman kubce masa dan yasan shima da gaske Sultan ɗin ya kai iyakar gajiya, amma sai ya fiske yace,"Da gaske nake Sir, gama files nasu na kammala dubawa" "Aryan Please, wallahi na gaji, sai dai kai ka dubasu” ya faɗa yana sauke numfashi da miƙewa ya nufi wata ƙofa. Murmushi Aryan yayi yana binsa da kallo harya shige. Ya ɗan girgiza kansa da kwasar files ɗin ya fice daga office ɗin zuwa nashi shima. Ɗan madaidaicin ɗakin dake cikin Office ɗinsa ya nufa dake ɗauke da kayan daɗi compiled, shima sai kamshi yake mai daɗi.kamar ba'a cikin asibiti ba. Kai tsaye toilet ya nufa yana faman lullumshe idanu dan barci yake matuƙar ji. Bayan wasu mintuna ya fito daga toilet ɗin sanye da rigar wanka Fara, sai hular wanka data kare gashinsa daga jiƙewa, da alama dai baya buƙatar jiƙawar. A bakin gadon ya zauna yana mai furzar da iskar daya cika bakinsa da ita, yajawo wayarsa dake a drowar gefen gadon a jiye ya cireta a silent. Dan ya sakata a silent ɗinne tun lokacin dazai shiga theatre room. Aziz ya kira, sai akai rashin sa'a ya samu wayarsa a busy. Kume fuska ya sakeyi alamar baiso hakanba, ya ajiye wayar. ɗayar ya ɗauka itama ya cireta a plane mode daya sakata. Kamar jira ake ya cire ɗin sai ga kira ya shigo, kafin ya amsa kuma akai knocking ƙofar. Rasa wanne zai farayi yayi. Ɗaga wayar? Kokuwa buɗe ƙofar?. “Sir" ya tsinkayi muryar Dr Aryan na kiransa. Duk da yayi tunanin akan maganar patients ɗin da Dr ɗin ya yi maganar zai dubane hakan bai hanashi tashi ya buɗe masa ƙofaba, sai dai ya sake haɗe fuska alamar da gaske ya gaji baison takura. Yana buɗe ƙofar yace, “Aryan plea.....” Saurin katsesa Aryan yayi da faɗin, “Yi haƙuri ba wancan maganar bane, akwai damuwa Sir ɗaya daga cikin Nurse ɗin nan ta yiwa Yaro Allura ta kare a jikinsa. “What?!” ya faɗa hankali tashe. Shima Aryan da hankalin nasa ke a tashe ya shiga jinjina masa kai. Juyawa cikin ɗakin ya yida sauri, yama manta da wata gajiyarsa. A Gurguje ya shiya ya fice daga ɗakin Dr Aryan zauna a Office ɗinsa tare suka fice daga Office ɗin, tun kafin su ƙaraso suke juyo Murya yaro na kuka, sauri sauri gugu gudu suka ƙasaso wajen, Sultana nabaki ɗaya a ruɗe take jikinta har karkarwa ya ke, Cikin tsananin tashin hankali da tsagwaron damuwa yace, " ta yaya hakan ta faru? Ince duk yanda ya kamata a ba mara lafiya kulawa na sanar muku. Miyasa kuke da sakaci akan rayukan mutane!!?” ya ƙare maganar da ɗan raunin murya. Sultana da maganar Dr Sultan tai mata zafi ya buɗe baki zaiyi magana cikin ƙoƙarin danne fushinsa, amma sai Sultan ɗin ya kuma dakatar da ita ta hanyar faɗin, “Bana buƙatar jin komai please" yaron ko sai kuka yake kaman Ranshi zai fita, cikin dubara Sultan ya cire Allurar wajen harya kumbura, kana ya shika lallaɓa yaro har Saida yayi Barci ya bar wajen Sultana ta rakashi da Harara. Dai dai lokacin Jidda ta ƙara so wajen tana faɗin ,"Daughter Lafiya Sultana ta sauke Nannauyan Ajiyar zuciyar kana,"tace ni da ɗan renin hankali,bai ko tsaya jin bahasi ba zai rufeni da faɗa ta ƙara sa maganar cike da tsiwa, "kimin baya Meya faru Daughter, "wai yaron nan ne fa ya ƙi tsayi nayi mishi Allura garin mutsu mutsun sa Allura ta kare a jikinsa, da sauri Jidda ta ware mayan idanunsa kana yace," nashiga ukku Ni Kuluwa!" "Haka kwai zai hauni da faɗa kaman wani ubana" "Daughter gaskiya ne Dr ya faɗa ki riƙa kula Allah ya tsare gaba" Ƙala Sultana bata ce mata ba. Kana sukaci gaba da aikin su. A bangaren Sultan yana komawa office yayi wonke hanneyensa sannan ya fada kan sofa ya zauna yana jin haushin abunda ya faru...gaba daya bacin ranshi sai ya karu fiyeda wanda yake ciki already...tunda yake bai taɓa ganin sangartacciyar yarinya kaman wannan yarinyar ba...maida kanshi ya lafe jikin kujera tareda lumshe ido.. a hankali ya mike yaci gaba da aikin da ke gabansa, Wuraren ƙarfe 5:40 ya kira Direba, bayan mintuna 20 ya iso, bayan ya kammala a binda yake ya fice daga Office ɗin kai tsaye ya wuce Parking space, dai dai lokacin Sultana ta iso wajen tattausan sumar ƙeyansa dake kwance lib-lib ta zubawa harara. Numfashi mai sanyi taja tare da shaƙa daddaɗan ƙamshin turarensa mai sanyi. Sai kuma tayi ƙasa da kwayar idanunta,baki ta ɗan tura sama ta da liƙa ƙeyarshi wani sabon harara tare da zan tsaki hankali ya ɗan juyo gefen damansa, jin inda sautin tsaki yake ɗan tashi ya kauda kai gefe kaman bai jita ba ya shige mota, motar na ɗagawa Jidda ta iso wajen tana faɗin ," Daughter tsaya ki rage min hanya, ba musu ta tsaya jidda ta shiga kana suka fice daga Asibiti, cikin mota kuwa Jidda sai labarin Sultan take,har suka iso