← Book details Dr Sultan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 54

Sashe 40

Dr Sultan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ash!!" ya faɗa da sauri yana janye hannunsa da ya toshe mata baki da shi, dan kuwa daddagewa tayi ta gasa masa cizo a tafin hannun. Yaja da baya yana yarfe hannun nasa da faɗin, "Witch girl" Sultana da har yanzu jikinta bai bar rawa ba ta galla masa harara tana share hawayenta. “Allah ya tsare da maita, Kuma wallahi ka sake gigin taɓani saina karye hanneyenka, danni ba ƴar iska baceba!”. " Waye ɗan iskan?"ya faɗa yana galla mata harara tare da cafkota, iya ƙarfinsa ya fisgota tayo baya ta sake faɗawa jikinsa. Mannata jikin bangon ya sakeyi, ya toshe mata baki da ɗayan hannunsa. kafin ya ɗago ɗayan hannun ya kalli inda ta cije sa, yamutse fuska yayi ganin yanda shatin haƙoranta suka fito masa Sultana hankalinta ya yi ƙololuwar tashi,ta rikice iyakar rikicewa yanzun kam, dan ta yarda a ranta da gaske Sultan son cutar da ita yake. Ƙilama abinda ya kawosa gidan kenan. Sake kaima ɗayan hannun cizo tayi. Yayi saurin janyewa , ba zato ba tsammani taji saukar lallausar labɓansa a bakinta. Shi kansa baisan yaya akai hakan ta faru ba, ya tsinci kansa ne kawai da haɗe bakin nasa da nata ya shiga kissing ɗinta. Atake wani matsananci tsoro ya sake lulluɓe Sultana yayin da jikinta yashiga rawa tamkar mazari. Wani irin masifaffen tsuma jikin Sultana keyi yayin da numfashinta ke fusga saboda tsananin tsoron Abinda Sultan ya aikata mata yasa ta sake ƙanƙamesa tamkar zata tsaga jikinsa. wani irin rungumeta yayi da masifar ƙarfi yana mai sakin Nannauyan Ajiyar zuciya Daƙyar ya iya ɗaga hannunsa tare da dafe kansa da yake jin wani irin jiri na fizgarsa tare da sarawa, da sauri ya sake sunkuyar da kansa akan wuyanta kana ya sake rungumeta da ƙarfi baki ɗaya ya rasa wani irin yanayi yake ciki.. dai dai kuma a ka ɗauke wutar nepa. hakan yasa ta sake rungume Sultan da ƙarfi,Jin yadda take liƙewa a jikinsa ne, yasa shima ya saƙe yi mata wani irin rugguma tare da sauke Nannauyan numfashin yana shaƙan Daddaɗan ƙamshin jikinta. Itama sake rungumesa tayi cikin mawuyacin hali tana neman numfashi domin numfashinta na ƙoƙarin ɗauke wa gaba daya tsananin tsoro da tashin hankali ya bayyana asaman fuskarta, a tarihin rayuwar hakan bai taɓa faruwa da ita ba, Cikin wani irin yanayi mai wuyar fassarawa da ficewar hayyaci Sultan ya sake rungumeta yana jin ɗumin jikinta. A hankali yasa Lallausan tafin hannunsa ya tallabo fuskarta tare buɗe manyan idanunsa da ƙyar dan har yanzu dishi-dushi yake gani, idanu ya tsirawa kan goshinta , yalwataccen sumar kanta da yasha gyara, kallonsa ya mayar kan fuskarta jin, yanda numfashinta ke fita da sauri sauri. Idanunsa ya mayar kan ƙirjinta da sauri ya lumshe idanun, a hankali ɗaura lips ɗinsa a kan kunnenta ya hura mata iska mai ɗumi..Wani irin dogon numfashi taja mai nauyi tare da fesar dashi da ƙarfi, cikin ƙanƙanen lokaci numfashinta ya soma dai-dai kana duk abinda ke faruwa idanunta na lumshe.. Sultan sannu ahankali ya fara dawowa hayyacinsa da nitsuwarsa. Sake lafewa Sultana tayi ajikinsa tare da lumshe Idanunta. lumshe idanunsa yayi jin jikinsa babu kuzari kona kaɗan, ji yake tamkar an zare masa lakar jikinsa cikin sanyi da rashin kuzari dake tare dashi. A hankali ya janyeta daga jikisa.Shiru bata motsaba, hakan yasa ya sake ɗan fizgo muryasa tare da faɗin."Sultana!" Karon farko A rayuwarsa da yafara kiran sunanta. Cikin raunatattiyar Murya yaci gaba da kiran Sunanta, "Sultana! Sultana!! Sultana!!!" Sultana har yanzu idanunta na lumshe take Jin sautin muryar Sultan na kiran sunanta kamar amafarki, Lumshe Idanunsa yayi akaro na barkatai tare da kai bakinsa cikin kunnenta kana cikin raunan'nanyar murya mai taushi yace.,"Sultana!!" Cikin tsananin tsoro Sultana ta janye jikinta, Cikin mawuyacin hali ya dafe kansa da hannunsa na hagu murya narawa yace." Astagfirullah wa,atubu ilaik Ya Allah!!" "Allah ya isa ban yafeba mugu kwai Azzalumi, Yanzun kam da kansa ma ya matsa ya bata hanya, da gudu tabar wajen kuwa tana kukanta har yanzun. Cike da takaicin kansa ya rumtse idanusa da ƙarfi, tare da ɗora hannunsa a goshi yana murzawa da abaton “Ya rabb!" gudu ta shiga palon ta nufi ɗakin su, tana shiga ɗaki ta lumshe Idanunta tare da manna bayanta da jikin ƙofa. Hawaye masu ɗumi suka zubo mata har zuwa yanzu jikinta baibar rawa ba, sai faman waige-waige take tamjar ance mata Sultan ɗin biyota yayi. Ta ƙanƙame jikinta lokacin da abinda ya farun ya sake dawo mata a rai, yanda gashin jikinta ke wani mimmiƙewa zai tabbatar maka da tsigar jikinta tashi takeyi. Da sauri ta saka hannu tana share hawayenta saboda jin tahowar mutum. ‘Na shiga uku ya biyo ni’ ta faɗa a fili zuciyarta na wani irin bugawa tamkar zata faso ƙirjinta ta fito.. "Anty Sultana lafiya?" Duk da ganin Meena ce ba Sultan ba hakan bai hana Sultana sake rikicewa ba, ta shiga inda-inda jikinta na tsuma. "Ba Komai". da sauri ta share hawayenta ,"Ba komi Meena, "Anty Sultana kuka kike fa sannan kike ba komi?" "Kinga ya isa. Share waɗan nan hawayen idan baso, aiko kaman jira take da saurin Sultana tasake share hawayen, "gayamin me yafaru Anty Sultana!" Sultana bata ɓoyewa Meena komi ba, "Anty Sultana shi Ya Sultan ɗin da kansa ya yi haka?" Kai ta gyaɗa mata, Ƙasa Sultana ta zube tana kuka tamkar ranta zai fita, Ɗagota Meena tayi ta share mata hawayen tana murmushi, “Shikenan naji, kuma na miki alƙawarin babu maijin zancen nan a gidan nan kinji, toilet ta Wuce tare da cire kayan jikinta ta sakarwa kanta ruwan ɗumi Da ƙyar ta iya yin wankan ta fito bayan ta ɗaura alawalan tare da doguwar riga ta roba ta saka har zuwa lokacin jikinta na ƙamshin tularensa Sallaya ta shimfiɗa ta gabatar da Sallah... Har aka kira sallah Sultan bai dawo ba, kiran Sultan ɗin Daddy ya yi, nan ya sanar dashi ya wuce Asbiti an kawo wani Emacency, Sultana yana isa gida kai tsaye ya wuce ɗakinsa kayan jikinsa ya cire kai tsaye toilet ɗin sa dake cikin Bedroom ɗinsa ya nufa yana shiga ya sakarwa da kansa ruwan ɗumi batare daya cire boxer ba yana tsaye ruwan ɗumin ya cigaba da zuba akansa Sai da yay kusan mintuna ashirin a haka sannan ya kashe shower ɗin yana sauke numfashi a jajjere babu abinda ke yawo a idanunsa kamar lokacin daya rungumi Sultana ga wani Daddaɗan ƙamshinta da yake ji ajikinsa da ƙarfi ya Lumshe idanunsa. Kai kawai yake girgiza wa cike da tashin hankali mara misaltuwa daya rufe idanunsa babu abinda yake hange face yanayin da suka kasance, bayan ya gama wanka al'wala ya ɗaura tare da fitowa, ya sanya lallausar jallabiya, a hankali ya tattaro duk kan natsuwar kana ya kabbarta sallah. Har akayi Isha'i ya zauna a wajen, Babu abinda kema Sultan yawo a zuciya da ruhi sai kalaman Sultana. Kalaman sunyi masifar tasiri a ransa fiye da zaton mai karatu. Sai faman tisasu yake dalla-dalla kamar mai bitar karatu. Duk da A.c dake aiki a dakin bai hana zufa tsatstsafo masa a goshi. Kana ya sauke wani irin nannauyan numfashi yana sake tariyo kalaman Sultana ,"Allah ya isa ban yafe ba! Mugu Azzalumi!!, ɗunbin takaici da dana sanin abinda ya aikata ma yarinyar yakeyi, wanda sam ba halinsa bane yin hakan,bayan Maryama ba wata ɗiya macce da ya taɓa runguma, amma yasan ita da duk wanda zai iya ji ko ganinsu a lokacin bazai taɓa yarda da shi ba. Ya ɗan ciza leɓensa na ƙasa da ƙarfin tsiya, ƙirjinsa na sake masa zafi. Mikewa tsaye ya yi tare da zaɓewa saman gadon tare da saurin dafe kansa dake barazanar rabewa biyu, Tashi yay zaune zumbur yana huci, so yake abinda ya faru yabar ransa, amma tamkar ana ƙara kusanto masa da hotonsa ne a zuciya. Da ya rufe ido babu abinda yake gani sai fuskar Sultana da ƙirjinta, sune kwai Abinda yake gani... Su Daddy sai bayan isha'i suka dawo gida. Bayan ta fiyarsu Meena ta shigo ɗakin riƙe da 🎁 ta mikama Sultana, jiki a mace ta ƙarɓa ,..... Washegari Duk yanda Sultana taso sakewa ta kasa hakan. Gani take kamar kowa yasan abinda ya faru tsakaninta da Sultan,..ranar dai haka ta yini cikin sanyin jiki....A ɓangaren Sultan ma ranar gabaki ɗaya a ɗaki ya yini sallah da cikin Abinci kwai ke fitar dashi.. Washe gari. Cikin sanyin jiki da damuwa Sultana ta shirya cikin Uniform ɗin ta da suka sha guka baki daya ta kasa sakewa da zaran ta tuna, Sultan sai tashiga da muwa..cikin dauriya ta nufi Asbitin...tana kaffa kaffa karsu haɗu da Sultan.... À ɓangaren Sultan ma tunda yashigo Asbiti ya wuce office ɗin su ya zauna cikin zullumi da damuwa. idanunsa alumshe duk abin duniya ya Ishesa. Haka dai Sultan ya yi Ni a Office har zuwa lokacin tashi ya wuce gida.. ★★★★ Yana isa gida ya Parking ya fita Kai tsaye sashensa ya wuce cikin mutuwar jiki ya kwanta ruf da ciki tare da lumshe idanunsa yayin da ƙwaƙwalwar sa ta shiga tariyo masa yanayin da suka kasance, sam Abin ya ƙi barin ransa, Miƙewa yayi cikin rashin sanin Abinda Zaiyi, ya zaiyi da wannan jarabar tun jiya yake fama da zaran ya rufe Idanunsa yanayin da suka kasance da Sultana ne yake gani. Batare daya shirya ba yaji hawaye Masu Zafi suna bin kuncinsa shi kansa baisan meyake so ba bai san meke faruwa dashi ba yakasa sanin yana yin da yake ciki ji yayi kawai yana kuka hawaye na bin kuncinsa yana sheshsheƙa. Nan take kuma zazzaɓi ya rufeshi lips ɗin sa suka shiga rawa.. A hankali Daddy ya tura ƙofar ɗakin ya shiga, ganin Sultan kwance jikinsa na karkarwa ya nufi wajensa da sauri ya na kiran sunansa,"Sultan!! Me ke damun ka? Baka da Lafiya ne?" Sultan ko magana yake son yi Amman ya kasa, da kyar ya fisgo magana,," Daddy sanyi nake ji, Daddy ciki na ciwo kaman zai ɓalle!" da sauri Daddy ya lulluɓesa da blanket mai laushi..a hankali Daddy ya miƙe ya kashe A.c dakin kana ya gyara mishi kwanciya, kasan cewar lokacin Sallah ya yi ya wuce masallaci, ana gama Sallah ya wuce Asbitin Sultan dai dai lokacin Kuma Dr Aryan na ƙoƙarin barin Asbitin ganin motar Daddy yasa ya
Chapter 40 · 0% Book details