Sashe 19
Dr Sultan Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Murmushi ya sanka masa da sadda kai a kamar jin kunya, shima ya yi Murmushi, shekarar ka Nawa? Kai a sunkuye yace ," Ashirin da Biyu!" "Masha na kai ga saurayi!" Tashi muje muje a binci ko? tare suka nufi darning sukaci Abinci cike da natsuwa, Bayan suna gama ya wuce ɗaki ya yi wanka kana ya kwanta cike da damuwar sabuwar rayuwa da ya tsinci kansa a ciki da wannan tunani bacci ya yi a won gaba dashi...... "Habibi gaskiya ya ron nan ya kwanta mi har ga Allah hakan nake jisan kaman ɗan da na haifa!" idanunsa ya lumshe tare da kwantar da ita a jikn nasa da kyau ya zame hular kanta yana shafa kanta dake cike da gashi dogo mai tsantsi, sunja tsawo lokaci a haka a hankali yaja musu lallausar Blanket ya rufe su dashi.... Washe garin wuraren karfe 10 security gidan suka shiko palon a kwataiya kusan set ɗaya kowanne cike maƙil da kaya... Anan tsakiyar Palon suka ajiye su... Cikin tsantsan farin Ummul khairi ta soma buɗe kayan tana kallon kaya ne kala kaya na maza shadda, ƙananan kaya jallabiyoyi kayan bacci, turarukka da muyun kan shafawa masu kyau da tsada ta takalma Kala kala e.t.c Abdulmalik kam haka ya saki baki yana kallon ikon Allah wai yau shike da kayan nan masu matsifar kyau da tsada... dai dai lokacin Alhaji Nuraddeen ya shigo Palon fusakar ɗauke da murmushi kamr ko yaushe, cikin raunin Murya Yace ," Sannu da zuwa Baba ," Yauwa my Son! Zo kaga kayan ka idon akwai a binda baiyi ba sai a canza,"Baba Allah ya saka da Alh..... Alhaji Nuraddeen ya yi saurin da katar dashi," bana son gidoya ƙarɓi nan ya yi maganar tare da miƙa Mishi waya kwalin wuyar Samsung Galaxy S23 Ultra mai matsifar kyau da tsada sai ga hawaye shar a fuskar Abdulmalik," Lokacin ɗaya suka sauke Nannauyan Ajiyar ," Sultan!! suka.kira sunan sa tare! A hankali ya ɗago da idanunsa da sukayi kaɗa sukayi jazir cikin wani irin yanayi ," Yace Na'am Baba miye na muka ya yi maganar tare da share mishi hawayen, Sultan ya sauke sassanyan Nunfashi," ashe bayan kaka zan sake haɗuwa da mutane masu kirki ya faɗa a zuciyar sa," Karna sake ganin hawayen nan kaji," kai ya gyaɗa mashi" je kaka wayar ka charge "Ta Baba har ya juya zai tafi Alhaji Nuraddeen ya dakatar shi," Bana son Baba nan da kake kirana ya faɗa cike da zolaya," A karon farko ya saki Murmushi har haƙora sa suka bayyana" Nima dai bana son Maman nan kaman wata tsohuwa lokaci ɗaya suka saki Murmushi," a nan cikin palon ya saka wayar charge, " Larai ina Abu kuzo ku shigar da kayan nan ɗaki ku jera moki yadda ya dace" "TOH Ranki ya daɗe" Ranar haka suka kwance cikin tsantsan farin ciki..... A ɓangaren su Maryam a hankali ta fara sakin jiki zuwa yanzu harta fara maida jikinta tuni an saka ta makarkatar su Haydar a jss3 saboda ƙoƙarinta haka kaka ta rungumu jikokinta tana kulada dasu tare da masu Aiki... A ɓangaren islamiya sosai ta maida hankali da karatun hadisai da harda, Abdullahi ma ya fara maida jikinsa kullum Kaka a gaba take sashi harsai yaci Abincin... a hankali shaƙuwa mai ƙarfi ta shiga tsakin kaka da jikokinta Rayuwar suke gwanin burgewa, Washe gari tunda sassafe Alhaji Nuraddeen suka wuce Asbiti wajen likita tare da saka Dr ya bincika mai lafiyar Sultan ko yana ɗauke da wata cuta, Alhamdulillah duk wasu kwaje kwaje da ya kamata ayi Mishi an kammala tsab bai dauke da kowacce cuta.... Nan ya ƙara jin son yaron A ranshi.. godiya sosai Alhaji Nuraddeen ya yi kana suka wuce gida.... Bayan sun iso gida ya kira Abdullahi ya sanardashi abinda ya faru tare da ɓoyemai wasu bayanai kan Abdulmalik ɗin kan Ainiyin sunanshi da garin da yake da kaka da Maryam da ya rasa, haka wai yaji yana kyaunar yaron shima,nan ya shiga taya shi murna sun jima suna waya kana sukayi Sallama.... Sannu a hankali shaƙuwa mai ƙarfi ta fara shiga tsakanin su zuwa yanzu Abdulmalik ya fara sauyawa sosai ya yi warin fari mai matsifar kyau da ɗaukar ido fatarshi har wani glowing take sumar kanshi ta kara cikowa da tsowo ga wani sheƙi da take... Wasa wasa Abdulmalik ya fara saba wanda sabon sunanshi Sultan da kowa ke kiransa a gidan hasalima ba wanda ya san Ainiyin sunansa na gaskiya, a Wani ɓangaren kuma duk lokacin da ya tuna da Maryama da Kaka har kuwa yake. Sosai facebook ke ɗebi Mishi kewa. haka suka ci gaba da rayuwar su cikin kwanciyar hankalinki, Yau ta kasan ce Assabar Tun safe Ummul khairi keta aiki abinci tare da masu aiki tuni gidan ya gauraye da kamshi, a hankali yake yaku har izuwa Darning erea a hankali ya ɗan juyo jin an jamai kujera tsaye yake fuskar sa ɗauke da murmushi ," Daddy Ina Kwana? A hankali ya Lumshe idanunsa kana ya buɗe a kan kyakkyawar Fuskarsa,"lafiya lau" "Wai me Mommy ka ke girkawa haka niji gidan sai khamshi yake?" "Aiko haƙura Zakuyi da khamshin nan don ban dafa daku ba ta karasa maganar cike zoyala lokacin ɗaya suka saki Murmushi, " Laifin me muka aikata haka?" Dai dai lokacin kwata Kyakkyawar mata shigo," Fuskar cike da damuwa," sauri Mommy ta nufi wajen ta tana faɗin Kulsum lafiya sai kuma ta fashe da kuka lokaci ɗaya Alhaji Nuraddeen da Sultan suka miƙe tare da barin Darning suka nufi wajen su, cike da damuwa ," Mommy ta soma tambatayar ,"Kulsum lafiya mike faruwa? a hankali ta share hawayen murya a disashe tace ,"Anty wlh na gaji da walaƙanci da Dengin Marigayi suke min yau suksan sati guda kenan da suka sani a gaba wai saina bar musu gida tunda an raba gado na tashi na bar musu gida," Shine na ce banza tashi ba zan Ƴa ƴa na ke," Yauwa da safe koda na kaisu Meena islamiya na dawo sun rufe gida wai na tafi na bar musu gida, ba yadda banyi dasu akan subarni suka ƙi, ta ƙara sa maganar tare da fashewa da kuka mai tsuma zuciya," da kyar suka shawo kanta ta Dena kukan," Yanzu ina su Meena ɗin?" ,"Suna islamiya Anty," shikenan ki Dena kuka," je ɗaki ki watsa ruwa ki fito muyi Breakfast, " Anty Don Allah a karbo min ƴa ƴa na bana son su zauna tare su, zasu.. ya isa za'a karɓo su cewar Alhaji Nuraddeen," jiki a mace ta wuce ɗakin ta watsa ruwa koda ta fito Mommy ya aje mata kaya a saman gado bayan ta shirya ta fito Palo suka karya.... "Wacce islamiya suke" Madarasatu Norul Islam ta faɗa cikin sanyi Murya, shike nan zan tura Dogo ya dauko su, batun gida kuma ki bar musu gidan Yara muka canzi gaba da kula dasu,"mommy ta sauke sassanyan Nunfashi tare da kallon Mijin nata ,"Alhaji Allah ya.... "Ya isa" "Ya Nuraddeen nagode sosai itama ya yi sauri da Katar da ita, sanin halinsa na reshin son godiya idon ya aikata alheri.. dai dai lokacin Dogo Deribe ya shigo Palon, "Yau dogo su Meenah zaka ɗauƙo a islamiya Yaya bari na bishi mu tafi tare okay ba damuwa, tare suka fice daga palon.... "Daddy mun gama shirin Maryam tace bazata jeba karatun Hadda Zatayi, Abdullahi ya Kalli Maryam dake zauna,"Mamana tashi ki shirya mu tafi Kinji! Ke kadai za'a bari gida sai ran sunday zasu dawo, "Abba Malam yace idon ban iya sai ya zaneni!"ta ƙarasa maganar kaman Zatayi kuka," Shike nan" Abdullahi ya kalli Kaka," Kaka yace Mama zamu tafi," toh Abdullahi Allah ya Tsare," Amin Amma!" Har bakin kaka ta sakaru tare da Maryam, bayan tafiyar suka wuce cikin gida....✍️✍️✍️ _More comments and share_ *Sadeeya Ka'oje ce* 💋✍️ *DR SULTAN* (A heart touching love story)