← Book details Dr Sultan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 54

Sashe 18

Dr Sultan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*The beginning* *Page 13-14* ___Bacci sosai ya yi sai gab da maggariba ya farka a gurguje ya yi Wonka ya rama sallalolin da bai samu damar yi ba, yana zauna saman sallah, aka buɗe ƙofar ɗakin a hankali ya ɗaga kansa tare da kallon ƙofar tsaye take fusakar ɗauke da murmushi," Ka farka kenan?" tun dazu nake kai da komowa," kai a sunkuye yace,"Mama! Barka da warhaka," Barka kadai Yarona! Ya ƙarfin jiki?" "Alhamdulillahi!" " taso muje Kaci abinci ko kafin aka kira sallah" "Cikin sanyi Murya yace ," Mama saina yi Sallah.maggariba" "Aa Yarona Ci yana gaba da Sallah don. Haka taso muje Kaci abinci," Kaman wani ƙaramin yaro taja hanunsa suka wuce Darning da kanta tayi sarcevig ɗinsa Kana ta tura mishi Plate ɗin a gaban sa, a tsanake ya soma cikin Abinci yana Lumshe ido," "Yauwa ko kaifa ba gashi kana gamawa ba ana kiran sallah" dai dai lokacin Alhaji Nuraddeen ya shigo Palon fusakar ɗauke da murmushi ya kalli matar tashi ," Ya tashi ke nan?" Murmushi na kara faɗaɗa a fuskarshi tace ya tashi da kyar ya yadda zai ci Abin wai nabari sai anyi sallah," Raron nan naki inga shine limamin unguwar su ya faɗa cike da zolaya, lokacin ɗaya suka saki Murmushi," "Tashi muje masallaci ko? Kaman jira yake da sauri ya mike tare suka fice daga palon a hankali ta sauke sassanyan Ajiyar zuciya," Barka da warka Ranki ya daɗe" "Yauwa Ladidi ya aiki ," Alhamdulillahi" " ina fatan An kammala Abinci?" "Ehh Ranki ya daɗe" "Yauwa a jera komi saman Darning"tana kai ƙarshe Maganar ta wuce ɗakin, Sai bayan Isha'i suka shigo palon dai dai lokacin ta iso palon ," Sannun ku dazuwa" "Yauwa" "Mama ina wuni" "Lafiya lau Yarona" "An kammala abinci," "Nidai a kwoshe nake bana jin yunwa, aiko zanma ɗure a gidan ta faɗa cikin zolaya" ga baki danyan su suka wuce Darning Abinci su sukaci cikin. Kwanciyar hankali da natauwa, Bayan sun gama cikn Abinci Alhaji Nuraddeen ya kalleshi cikin sanyi Murya ya soma Magana,"gashi har yau bamu san sunanka ba!" a karon farko ya saki Murmushi tare da fesar da Numfash Kana yace ," Sunana Abdulmalik!" a hankali ta sauke Nannauyan Ajiyar kana ta fesar da iska," Kallonta Alhaji Nuraddeen ya yi kana yace ,"Lafiya?" "Ba komai fa!" "Are you sure!? Gira ɗaya ta daga mai tare da sakin Murmushi" "Ma sha Allah suna nan Uncle ɗina! In sha Allahu idon ka ƙara jin sauƙi sai ka koma gida ko, kar Kaka da Maryam su shiga damuwa," dai sauri ya gyada mai kai tare da faɗin Ni Ko yanzu ma zanje wajen su! "Mai sunan Uncle yanzu kam dare ya yi " ka bari ka huta nida kaina in sha Allah zan maida ka gida!"cikin tsastsan farin ciki ya yi mai godiya, "Kaje ka kwanta ko" a hankali ya mike Kai tsaye ya wuce ɗaki ya watsa ruwa Kana ya kwanta cike da kewar Maryam da Kaka da haka har Bacci ya yi a won gaba shi...... ★★★★★..........★★ Jikin Abdulmalik ya yi sauki sosai Alhamdulillah kwana huɗu kenan da samun sauƙin sa, tunda sassafe suka wuce Ƙaraye cike da zumuɗin ganin Maryam da Kaka, lokacin da suka iso da taimakon Abdulmalik Alhaji Nuraddeen ya iso gidan su Kaka, . lokacin da suka iso yara cike a ƙofar gida wasu na shiga sawu na fitowa masu shiga kowannen rike da kaya, cikin tsananin damuwa da tashin Abdulmalik ya fito daga Mota lokacin da yaron Unguwa sukayi ido huɗu dashi suka kwasa a guje tare da faɗin fetalwa ta shiga gari, nan take mutane suka fara guduwa, da farkon abin yaba wa Alhaji Nuraddeen dariya, nan take gari ya dauƙa da labarin bayyana Abdulmalik, haka mutane suka tsaya cirko cirko a ƙofar gidan Kaka, cikin tsananin tashin hankali da ruɗu Abdulmalik yariƙa binsu da kallo ɗaya ba dayan ɗaya, Alhaji Nuraddeen ya yi gyaran Murya cikin sanyi Murya ya soma magana ," wai mike faruwa?" Nan hankali kowa ya dawo kan Alhaji Nuraddeen," lokaci ɗaya mutanen dake wajen suka sauke Nannauyan Ajiyar zuciya," Abdulmalik daman kana yare?" Sai lokaci Alhaji Nuraddeen ya fahimci mike faruwa, Ayuba yaci gaba faɗin ai tsawon sati Ukku kenan da labarin mutuwarsu, Alhaji Nuraddeen ya sauke sassanyan Nunfashi kana yace," Abdulmalik bai mutu ba nan ya shiga basu labarin da Abdulmalik ɗin ya bashi har izuwa haɗu warsu, sosai Al'ajabi ya kama su da jin Labarin da Alhaji Nuraddeen ya basu, Sai lokacin Abdulmalik ya samu damar ya yi magana cikin raunin Murya ya soma magana," Ina Kaka da Maryama ta!?" dai lokacin Malam liman ya iso ƙafar gida da farko ya tsorata da ganin Abdulmalik tsaye, cikin ɗauriya ya ƙaraso wajen tare da ba Alhaji Nuraddeen hannu suka gaisa kana ya maida kallon da Abdulmalik. Cikin tsananin tashin hankali da ruɗu dake tattare dashi ya gaida malam Liman, Kana Alhaji Nuraddeen ya shiga yiwa Malam liman Abinda ke tafe da su da labarin abin ya faru, Cikin tsananin mamaki Malam Liman ya Kalli Abdulmalik cikin sanyi Murya ya soma tambayarshi ya jiki," Murya a dishace ya soma magana ," naji sauƙi!" "Allah ya ƙara sauƙin!" "Malam Liman ina Maryama da Kaka!" Nan Malam Liman ya shiga bashin labarin koma warsu Kaka birni, cikin tsananin tashin hankali jikinsa ya soma karkawa," sai kuma ya fashe da kuka mai tsuma zuciya jikin kowa a wajen ya yi sanyi, sanin irin shaƙuwar da ke tsakanin su,"Malam ya ɗora da cewa yanzu haka sun mallakamin gidan su, Alhaji Nuraddeen ya sauke Nannauyan Ajiyar zuciya, cikin tausasa halshe yace ," yanzu kenan sun koma Kano da zama? Ko kana da Address ɗinsu ko number waya haka ,"wlh banda masaniya akan su, Number Mama bata shiga shima ɗan nata kuma banda wata masaniya akan sa halima rabona dashi tunda mahaifinsu ya rasu duk garin nan kuma ba wanda yake da masaniya a kansa, Saida yana kamfanin mai suna Gwa....... Bai kai ga karasa ba Abdulmalik ya yenke jiki ya faɗi a sume, cikin tsananin tashin suka dukufa akansa don ganin sun ceto rayuwar sa cikin aikon Allah ya sauke Nannauyan Ajiyar zuciya, "Nagode sosai Alhaji Nuraddeen ya faɗa cikin girmamawa in sha Allahu kuma daga yau kula da Abdulmalik ya rataya a kaina canzi gaba da kula dashi har ranar da Allah zai baiyanar da Kaka da Maryam ɗin.... Godiya sosai malam Liman ya yi sama ko ba komai Alhaji Nuraddeen ya kwanta masa a rai duk da bai naɗa musu koshi waye ba, a hankali Alhaji Nuraddeen ya kalli Abdulmalik kana yace ," Ko a wai abinda zaka ɗauka?" a hankali ya gyaɗa mishi kai, lokacin da zasu tafi Alhaji Nuraddeen ya ba malam Liman kusan 50k..... tare da Number wayarshi koda wani Abin ya taso.. Kai tsaye suka wuce dakin Abdulmalik cike da kewa ya riƙa bin dakin da kallo komai na yadda ya barshi, yana kuka ya soma kwasar kayanshi da takardun sa na makaranta da duk wani abu mai mahimmanci kana ya fito daga ɗakin jiki a mace ya nufi wajen mota ya shigar da kayan bayan Booth. a tsanake suka bar ƙofar gidan... Kai tsaye suka kama hanyar Kano tafiya suke a hankali.. Abdulmalik ido kawai ya runtse cikin wani irin yanayi mai Tsananin kai kuma ya juyuwa ya runtse ido tunowa da kalaman Maryam lokacin da zai tafi ," Ya Maleek Allah ya sada mu da Alheri!" Wannan kallama ta tsaya mishi a rai haka ya riƙa tubka da warware har suka iso gida.... Tamkar wanda aka zarmewa lakkar jiki Haka suka shigo cikin palon ," Habi......saikuma tayi shiru ganin Abdulmalik a tsaye ," Sannun ku da zuwa!" Jiki a Mace suka zauna Abdulmalik da dan kunshin kayan, " Lafiya dai?" Lokaci ɗaya suka sauke Nannauyan Ajiyar," Alhaji Nuraddeen bai ɓoye mata komi ba ya sanar da ita bayanin da Malam liman ya yi mi shi, "Allah yasa hakan shine Alheri! "Amin" Alhaji Nuraddeen ya yi gyaran Murya cikin tausasa halshe ya soma magana ," Abdulmalik!" Cikin raunin Murya yace ," Na'am Baba!" " Wannan itace Matata sunanta Ummul khairi tsowon Shekara Goma sha biyar kenan da Auren mu Allah bai taɓa bamu Haihuwa!" daga yau ina son kadauƙi Ummul khairi a matsayin Mahaifiyarka, bana son ka a jeta a wani matsayin da bana Mahaifiya ba!" Ummul khairi ta sauke sassanyan Ajiyar zuciya, kana ta kalli Abdulmalik dake zaune jikinsa duk ya yi sanyi cikin sanyi Murya tace," Abdulmalik wannan shine mijina! Alhaji Nuraddeen Mai Nerah! Ina son daga yau ga ɗaukeshi a matsayin Mahaifinka! Gidan nan gidan Mahaifinka ne kayi duk abinda kake so, Ina fatan zaka ɗauke mu tamkar yadda muka ɗauke ka!" Cikin wani irin yanayi Abdulmalik ya gyaɗa kai dan damuwa ƙarara ta fusakar sa da cikin idanunsa cikin ƙarfin hali ya sakar mata murmushi, " Yauwa Uncle ɗina .Allah ya yi maka Albarka! cewar Alhaji Nuraddeen," Murya a disashe yace ," Amin!" "Wai da gaske sunan Uncle ɗin mu gareshi," Alhaji Nuraddeen ya gyaɗa mata kai," Yayan Mama ne Kuma yana bala'in so na!" Lokaci kafin ya rasu kullum a gidansa nake kwana" "Allah ya gafarta mishi tare suka Amsa da "Amin" "Wannan ai babban suna ne gaskiya Bazan iya kiran sunan Uncle kai tsaye ba" Shidai Abdulmalik sai kallon su yake, Cike da zumuɗi Alhaji Nuraddeen yace ," wanne suna zaki riƙa kiran sa?" Kai ta ɗan daga kaman mai tunani ," Uhmm Aryan! cike da zolaya Alhaji Nuraddeen yake ,"A'a bakin ta.dan turo cike da Shogoɓa da sauri Abdulmalik ya sunkuyar da kai, a karo na biyu ta sake cewa,"Affan! "a'a Abba! Ya girkiza mata Kai," Ayman! "A'a Aslam! A karo na Barka tai tariƙa faɗin sunaye," yana faɗin A'a," fuska a tsuke taci gaba da faɗin sunayen ," Allah na gaji!" kana taci gaba,"Muslim! Arif! Sultan!!" da sauri Alhaji Nuraddeen yace ," Yes wannan ya yi! SULTAN!! Allah sunan ya yi daɗi sosai kuma ya dace dashi," Abdulmalik ya Lumshe idanunsa kana ya buɗe akan fusakarsu, "A hankali ta sauke sassanyan Nunfashi kana tace ," da gaske sunan ya yi!?" "Sosai ma" "Sultan! Sultan!! Sultan!!!" Abdulmalik da sauri ya juya yana Kallonta" a karon farko Alhaji Nuraddeen ya saki Murmushi, kana yace Mahaifiyar ka ta maidaka Sultan saboda sunan Uncle ɗin a gareka!" Ɗan
Chapter 18 · 0% Book details