← Book details Dr Sultan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 54

Sashe 13

Dr Sultan Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

karatun sa, Kaka ta sauke Ajiyar zuciya," Abdulmalik ba irin yaran nan ne masu matattar zuciya Abdulmalik yaro ne mai son neman na kasanta ba yadda banyi dashi akan ya bari na taima ka masa yaƙi!?" Abdullahi ya fesar da iska mai ɗumi kana yace " Allah ya gafar ta Nishi!" "Amin ya rabbi" "Saida safe Mama ya kama ki kwanta" Bayan tafiyar shi Kaka ta jima zauna kafin nan Bacci yayi a won gaba da ita...... ★★★★.......... *BAYAN SATI ƊAYA* Rayuwa ta juya musu izuwa kunci da baƙin ciki musamman Abdullahi, Kaka Maryam, cikin satin nan daya sunyi wani irin masiffen ramewa, kallo ɗaya zaka musu kasan kusa cikin tsananin damuwa musamman maryam gabaƙi ɗaya ta fita cikin Haiyacinta duk ta dawo Shuru Shuru.... Tuni mutane sun watse su Haydar tuni sun fahinci Mahaifiyar su bata cikin gida lokacin da suka matsa tambaya Abdullahi ya faɗa musu Mahaifiyarsu ta rasu basu wani shiga damuwa saboda yarinya dake damun su, Haydar ne ma ƴa dan shiga damuwa Kasan cewar ya ɗan fisu wayo, daga baya kuma ya saki jiki sukaci gaba da wasar su...... ★★★★★..... A hankali ya fara buɗe idanunsa cikin wani irin mummunan yanayi da kyar ya tattaro duk ƙarfin ya miƙe zaune ya jingina jikin dutse a hankali ya riƙa bin dajin da kallon ko'ina tsit sai kukan tsuntsaye dake tashi, da sauri ya dafe kanshi dake sarawa da matsifar ƙarfi,ƙoƙarin tashi tsaye yake gabaki ɗaya jikinsa ƙarkarwa yake, ga wani irin masiffen kishin ruwa da yake ji, cikin wani irin yanayi a fara tafiya yana faɗuwa kaman yaro mai koyon tafiya daga ƙarshe ya dawo rarraye haka ya riƙa rarrarehe batare da yasan ina yake tafiya ba a hankali ya fara jin kukan motoci a karon farko ya sauke Nannauyan Ajiyar zuciyar ha ya riƙa rarrafe har ya iso saman titin cikin wani irin yanayi ya kiƙe tsaye yana tal gal tal gal kaman zai faɗi magana yake son yin ya kasa saboda masifar bushewa da maƙoshin yayi yana tsaye a waje wata mota ta wuce da masifar guda fuuuuuu. Ƙasan cewar ba ƙarfi a jikin sa wannan isar motar yayi sanadiyar faɗa warshi a' tsakiyar titi... Hakan yasa motar dake tafe ta taka burƙi da ƙarfi har motar na bada wani sauti tsuuuuuuu" direban ya sauke Nannauyan Ajiyar zuciyar, mutumen dake zauna a bayan ya yi sauri safe kanshi yana faɗi" Innalillahi wa'inna Ilahi rajiu'n!!! kana ya sake Ajiyar zuciya.... Motoci dake bayan su suka tsaya da ƙarfi, wasu kattan maza kusan guda huɗu suka diro daga cikin motar ko wannen su riƙe da bindiga da sauri suka nufi matar dake gaba, suka zagaye ta... "Doga duba ga yaron na yare!" Allah ya ƙarama lafiya mutafi kwai yanzu haka shirin miyagu ne! mutumen dake zaune bayan motar Ya yi Murmushi kana yace" duk Abinda ya faru da bawawa daga Allah ne! Koda mugaye ne Allah bazai bari su cutar damu Saboda da kyakkyawar niya muke, Dogo Direba ya sauke Ajiyar kana yace ," gaskiya ranka ya daɗe hankali bai kwanta ba shiyassa bana son mota ta ta zama itace gaba, "Dogo da gaba da baya da tsakiya duk Allah ne ke kare su!" Dogo Direba ya yi Murmushi kana ya buɗe motar gaban shi na faɗuwa, ɗaya daga cikin security ɗin yabi bayan shin da sauri dogo Direba ya dawo wajen mota ,"Ranka ya dade Yaron nan a sume yake.... Ɗaukoshi muje Asbiti, " Ranka ya Daɗe..... da sauri ya dakatar dashi ta hanyar ɗaga mishi hannu jiki a mace ya koma suka tallabo suka saka shi cikin mota. Kana suka wuce da gudun Gaske...... Tafiya suke da gudun Gaske kicin cikin ƙanƙanen lokaci suka iso Kano kai tsaye suka wuce Asbiti. nan take aka soma basu Agajin gaggawa, kasan cewar tare yake da ƴan sanda yasa sukayi gaggawar amsar shi, nan take likitoci suka fara gudanar da aikin su tsawon awa huda kana aka wuce dashi ɗakin hudu, bayan ya biya su kudin su ya wuce gida tare danƙa Amanar a hannu litaka kana ya tattabar mai cewa zuwa Anjima zai dawo.... Suna barin Asabiti akai tsaye suka wuce Nasarawa tun kafin ya iso aka wangale mishi gate wani katafaren gidane mai matsifar kyau da ɗaukar ido gaba ki ɗaya motoci suka dannan han hancu nansu cikin farfajiyar gidan sukayi Parking, a parking space da sauri ƴan sanda suka nufo motar shi kana suka buɗe Mishi, kai tsaye suka wuce cikin gida, dai dai lokacin kwata Kyakkyawa mata fara sol doguwa mai matsifar kyau sanye take wani tsadadden lass doguwar riga ta zauna mata ɗas a jikin a hankali taci gaba da sauko saman bene ɗin fuskarta dauke da murmushi.....✍️✍️✍️✍️ *More comments and share pls* *Sadeeya Ka'oje ce* *DR SULTAN* (A heart touching love story)
Chapter 13 · 0% Book details