Sashe 29
Dr Sultan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*(T .O.T)* *Breathe in courage, breathe outfear, together we stand* *Alkalaminmu abin alfaharn mu* https://chat.whatsapp.com/CuNxneQ0ONc6x9yn9a16Jj *The beginning* *Page 21-22* _______tagaza gane wanene zai iya tura mata wannan sak'on?, tad'an shinshina fulawar, kamshi mai dad'i yadaki hancinta, harsaida ta shak'a ta lumshe idanunta, kamar tataɓa jin k'amshinan, to amma a ina?, wannan itace tambayar. Dai dai lokacin kuma Motar Haydar ta shigo gidan da wowarsu kenan daga school tare da Meena, Cikin mamaki duk suke kallon Sultana, "Anty Sultana waye ya aiko miki?. "Wlhy Haydar....ban saniba nima?. Haydar.... Yamaida kallonsa ga Baba Mai Gadi, "waye yakawo?. "Wata 'wani ɗan Saurayi ne. "Saurayi" Sultana ta faɗa a hankali. "Anty Sultana Kodai kinyi sabon Kamu ne?" cewar Meenah, "Bana son Iskanci fa kowaye ya yi a banza,tana ƙoƙarin jefarda jakar Haydar ya yi saurin da katar da ita,"A'a Anty Sultana bai kamata ki jefar da ita ba.taɓe baki tayi, Haydar da Meena sukayi Murmushi cikin gida suka nufa, "Maraba da mutanen Asbiti, cewar Mami. fuska a yamutse Sultana ta nufi wajen su, "Mami Wlh na gaji"Sultana kuwa jingina bayanta da jikin Kaka tayi tana sauke Ajiyar zuciya, "ina kika samo flowers kuma?" "Say zaa nayi kaka ta bata Amsa a takaice, bari Naje nayi sallah a hankali ta mike Kai tsaye ta wuce ɗakin ta jefar da jakar saman gado kana ta wuce toilet Wonka tayi da ruwan dumi tayi Alwalla ta fito a tsanake ta yi Sallah, bayan ta gama ta wuce palon suka ci Abinci. hira suka dan taɓa kana kowa ya wuce makwancinsa.... Washegari , Yau sama-sama Sultana ta wayi gari, dan ta tashi da ciwon Baya alamar zuwan period ɗinta. Ita dama takan fara da ciwon Baya, randa yazo kuma zataita amai har saita jigata. Kafin daga bisani ta koma normal sai shegen ƙwaɗayi kamar mai ciki. Tunda Kaka ta shiga tadasu sallar asuba ta lura batajin daɗi, dan maimakon kwance saita isketa zaune ƙasa a bakin gado kan kafet ta kife kanta a kan gadon. Meena nata da Nana barcinsu a kan gadon . Ita ta fara tadawa kafin su Nana, har zata juya ta fita sai kuma ta dakata ta kalli Sultana data maida kanta ta kife tsakanin ƙafafunta....... “Ke kuma lafiya?”. Da ƙyar Sultana ta ɗaga kai ta kalli Kaka, sai dai gudun kar ace ta shirya aje asibiti a mata allura sai ta daure tace, “Kaka lafiya lau, kawai gajiyace. Ɗan ƙura mata idanu Kaka tayi na wasu mintuna, kafin ta janye tai ficewarta batare data sake cewa komaiba. Meena ce ta ƙaraso wajen Sultana ɗin ta durƙusa. “Anty Sultana ƙarya kikaima Kaka wlhy, daga gani baki da lafiya”. Yamutsa fuska Sultana tayi kaɗan tana maida ƙwallar data cika mata ido. “Baya na ke ciwo Meena nasan kuma period ɗinane zaizo zuwa gobe idan Allah ya kaimu ko anjima”. Nana dake fitowa daga bayi tace, “To miyasa kikaƙi faɗar gaskiya?”. Meena dake tsokanar Sultana tai saurin cewa, “Allura”. A tare suka kwashe da dariya ita da Nana Sultana kuma tai tsaki idonta cike da ƙwalla ta miƙe. Da ɗingishi ta shiga bayi batare data kula dariyar dasu Meena ke mataba har yanzun. Bayan sun idar da salla Meena da Nana suka soma shiri zuwa School, Sultana kam saita koma saman gado ta kwanta. Babu jimawa barci ya yi gaba da ita. kaka da duk ta gama fahimtarta bata nemeta ba, dan tasan zata gama zagayenta ne tazo ta nemeta. Bayan sun kammala breakfast, Su Meena suka wuce makaranta ga baki dayan su, "Wai Nikam ina Sultana Mami ta tambaya,"tana ɗaki ba Lafiya, cike da damuwa Mami ta ce," Subuhalillah Meya sameta ta faɗa tare da ƙoƙarin barin wajen, kai tsaye ta wuce ɗakin su Sultana, koda ta shigo Sultana sai faman juyi take tana damƙe da mara, "Sultana tashi maza ki shirya muje Asbiti, murya a disashe tace,"Anty naji sauƙi, dai dai lokacin kuma wayarta ta soma Ringing, "Kinga ana kiranki Jidda ce,Mami ta faɗa tare da ɗaga wayar, daga can ɓangaren Jidda ta ce,"Daughter Lafiya har yanzu Ban ganki ba?" cikin raunin Murya Sultana tace Mommy banda Lafiya!" "Mike damunki? Kinsha magani?" Kai Sultana ta girgiza mata kaman tana gabanta, "turomin Address ɗin gidan ku ganinan zuwa, suna gama wayar Mami ta tura mata Address ɗin, "tashi ki watsa ruwa kafin ta iso Mami ta taimaka mata zuwa toilet, tana fotowa da Wonka dai dai lokacin Mami ta shigo ɗakin riƙe da Cup din tea Mai kwauri, cikin ɗauriya ta kammala shirin, "karɓi Kisha, fuska a yamutse ta ce ,"Na ƙoshi Mami" "Ƙarbi maza Kisha" Ba yadda ta iya dole ta karba ta sha, kana suka fice ɗaga ɗakin, "Ya jiki Abba ta tambaye cikin kulawa, "Naji sauƙi Abba, dai dai lokacin Jidda ta shigo cikin palon cike girmamawa ta gaishesu, "Asbitin zaku je?" Mami ta tambaya,"Allah ya kiyaye,"Amin kana suka fice daga palon har bakin mota Mami da Kaka suka rakaru,tunda suka shiga cikin motar Sultana ta Kwantar da kai tare Lumshe idanunta,har suka iso Asbitin. A hankali suke takowa suna fuskantar juna. Sosai ya zuba mata ido sabida ya lura gaba ɗaya jikinta karkarwa yakeyi alamun tsananin ciwo takeji gashi a hankali take taku. Ita kuwa Sultana, tafiya takeyi da kyer sabida azaban ciwo da bayan ta da mararta keyi. Kanta a sunkuye take tafiya, Jidda na biye da ita a baya. Ganin yayi ta wani irin sunkuyawa tasa hannunta duka biyu ta damƙe mararta dake matsifar ciwo. "Yauwa ga Dr Sultan na ma yanzu ya iso, muje ya duba ki ko?" hannu tasa ta matse mararta tare da cewa."Allah ya tsareni ya Dubani duk Doctors dake Asbitin nan A rasa wanda zai Dubani sai shi.ta ƙarasa maganar cikin yanayin muryar mara lafiya. "Sir ga marar lafiya nan"Jidda ta faɗa, Dai-dai lokacin kuma suka kutsa kansu cikin asibitin. Kai kawai ya gyaɗa musu yaci gaba da tafiya, har ya shiga cikin wani ɗan corridor ya shiga wanda zai sadashi da Office dinshi ba tare daya ratsa ta cikin Reception ɗin su ba.. A Gurguje Jidda ta buɗe mata File ta wuce dashi Office ɗin Sultan. Jim kaɗan ta dawo. ta kama hannu Sultana,Da ƙarfi ta damƙi hannun Jidda Cikin tausayawa Jidda tace. "Sannu, in sha Allah bazamu jimaba za'a kiraki, dan na nemi al'farman sauran sun yadda.Kai kawai ta iya gyaɗa mata, sai taune lips ɗinta da takeyi. Suna isa office ɗin sa dai dai lokacin ya kira sunanta, batare da ta san waye ba ta nufi Office ɗin.Nurse namiji na ga banta.A haka suka shiga, Ajiyan zuciya taja a hankali sabida tsaruwa da kyau da tsabta da ɗan karen ƙamshin da ya ziyarci hancinta, su sukasa ta son bin Office ɗin da kallo amman ina ciwo bazai bartaba... A hankali ta iso gaban table ɗin baƙin Glass dake gabanshi. Ɗaya daga cikin kujerun biyu dake gaban table ɗin ta zauna. Ƙasa tayi da kanta cikin tarin ciwo da fargaba.Shiru tayi zaune bisa kujerar tayi ƙasa da kanta.Sultan ko kanshi bai ɗago ya kalli inda takeba.shiru Office ɗin sai sautin A.C da yake busawa, Kusan tsawon 2 minute suna a haka, cikin dakiya da rauni ta ɗan ɗago kanta ta kalleshi, Ga mamakinta sai taga asalima hankalinshi baya kanta, baki ta ɗan taɓe, a hankali tace,"Wai daman nan Jidda ta kawo Ni?" Sultan duk abinda takeyi yana ganinta ta ƙasan ido.cikin sanyi Murya ta ce, Nifa Lafiya ta lau. Shiru bai kulataba har sawon wasu mintuna 3 har ta fara zaton ko bai jita bane. Da sauri ta ɗago kanta jin yayi mata magana, cikin wata zazzaƙar murya a takaice yace. "Suna?". Cikin fargaba ta tace."Sultana Abdullahi. Shine sunan da jidda ta buɗe mata file dashi. A hankali ya ɗan ɗago ƙwayan idanunshi ya kalleta. Kanta a sunkuye hannunta biyu duka na kan mararta cikin wani, irin yanayi take wanda yake nuni da tana cikin wahala... Sultana ya maimaita sunan a Zuciyarsa. A fili kuma kauda idonshi yayi daga kanta ya maida idanunshi kan files dake gabanshi, wanda sunanta ke rubuce akan na samanshi yaja da yatsu biyu.Tsiraran idanunshi ya lumshe sabida wani irin bugu da yakeji zuciyarshi nayi tun lokacin ya kasance kusa da ita har zuwa yanzun nan da take gabanshi a zaune. Rubuce-rubuce yayi a ciki file. Kanshi ya kuma ɗagowa ya kalleta a fizge da gefen idonshi, sunkuyar da kanshi yayi tare da cewa. "Meke damunki?". Murya a disashe da son danne kukan da ke son kabce mata tace."Baya da Marata. Kai ya ɗan jujjuya tare da kallon shekarunta dake rubuce a cikin File din, Yar shekara ashirin kuma da ƙorafin ciwon baya, cikin sanyi Murya yace. "Yaushe ya fara miki ciwo?". Hannu tasa ta share hwayenta a hankali tace. "Shekara Huɗu da suka wuce". "Meyasa bakije asibitiba tun lokacin?". Ya tambayeta. "Ina zuwa asibiti duk sanda ya tashi". "Kamar yaushe da yaushe yake tashi?". Ya jefo mata tambayar kamar yadda zuciyarshi ke harbawa da ƙarfin tsiya da kuma sauri-sauri, cikin ɗauriya tace," duk ƙarshen wata. Kawar da kanshi ya yi gefe kaman bai jita ba yaci gaba da Rubuce rubucensa. Saida ya gama ya tura mata file ɗin a gabanta, Jikinta na rawa tasa hannu ta ɗauki file ɗin, ta yunƙura zata tashine, ya basu damar samun kusanci da juna, da sauri ya rumtse idanunshi sabida wani irin matsiffen bugawa da zuciyarshi keyi. cikin zuciyarshi yake maimaita. "Innalillahi wa innailaihi rajiun." A hankali ya buɗe kyawar kyawan idanunshi jin bugun zuciyarshin ya fara yin ƙasa-ƙasa, ido ya zubawa mata ganin ta juya tana tafiya, wani abin al'ajabin a gareshi shine duk taku ɗaya da zatayi tana nesanta dashi sai yaji zuciyarshi na tsinkewa yana bada wani mugun bugun , yayinda bugun tsinkewanta kuwa yaketa dai-dai-ta, Cikin mamaki ya sunkiyar da kanshi yana kallon yadda takeyin taku, tana riƙe da mararta, taje gab bakin fofar fitane, Taji wani irin murɗa da kartan da mararta ya farane yasa ta sakin wani sauti mai cike da wuya. "Wayyo! Allah na, Wayyo Mami cikina Wayyoo Ka...." Da sauri Jidda ɗin nan yayi kanta tare da cewa."Sannu Sultana"a hankali jidda ta zaunar da ita kujerun ƙarfe dake gab da bakin ƙofar. Bata da zaɓin daya wuce ta zauna ɗin, domin gaba ɗaya ƙafafuwan ta rawa sukeyi alamun bazasu iya ɗaukar nauyinta ba ga duhun daya rufe mata ido. Sunkuyowa Jidda ɗin yayi