← Book details Dr Sultan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 54

Sashe 46

Dr Sultan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*💋TITAN'S OF TALENT💋* *Marubuta masu aiki da fasahar zamani , zalar ilimantarwa,fadakarwa dakuma nishadantarwa* *(T .O.T)* *Breathe in courage, breathe outfear, together we stand* *Alkalaminmu abin alfaharn mu* https://chat.whatsapp.com/CuNxneQ0ONc6x9yn9a16Jj *The beginning* *Page 33-34* _______Hankali a tashe suka wuce da ita Asbiti, An musu ƙarɓar gaggawa saboda halin da Sultana take ciki. yanda suka ga likitocin na kai kawo ɗakin da aka saka Sultana hankalinsu ya daɗa tashi sosai. Duk kuma sanda wani ya fito suka tambaya baya basu amsar komai yake wucewa da sauri. Tun suna ɗaukar al'amarin ƙarami har suka fahimci yanada girma sosai, dan Doctors har huɗu sun ƙaru bayan na farko. Sai faman yin ƙus-ƙus kuma sukeyi a tsakaninsu...." Cikin ƙarfin hali Abba ya dubi Dr yana faɗin, "don idan yarinyar nan ta rasa ranta ne ya kamata ku sanar mana, dan kunata sake ɗaga mana hankali da rashin cewarku komai da kai kawon nan naku". Dr Sadiq ne ya tada kansa ƙasa cikin girmamawa yace, “Ai mana afuwa Ranka ya dade, ba muna ɓoye muku komai baneba. Kawai muna akan aikine shiyyasa, amma insha Allahu zakuji komai nanda ƴan mintuna kaɗan" Shiru wajen yayi babu wanda yace komai, sai dai a zukatansu sam basu gamsu da zancen Dr Sadiq ba. Kaka dake zaune a hankali ya jingina jikin kujera ta lumshe.ta faɗa duniya tunani. Tun da suka iso Asbitin har zuwa yanzun zuciyarta a ruɗani take. Motsin da taji a kusa da ita ne ya sakasa ta buɗe idanunta da ƙyar.Abba ne ta gani tsaye. "Mama muje gida ki huta ko" Duk da halin da take a ciki itama sai da tausayinsa ya kamata jin a yanda yayi magana. Tasan ƙarfin hali kawai ya keyi tun jiya akan al'amarin nan, amma shima a ruɗanin yake. Hannunsa ta kamo da ɗayan hannunta, ta Zaunar da shi. "Abdullahi inaji a jikina karon nan mutuwa Sultana Zatayi , a wannan karon zuciyata bazata iya ɗaukar wannan al'amarinba!!" Ta ƙare maganar da fashewa da kuka. Shima sai ya ji hawaye na ziraro masa batare da ya shirya yin hakan ba. Dan zuciyarsa ta karye gaba ɗaya. Ya rungumeta a jikinsa sukayi mai isarsu kafin ya ɗagota yana kallon yanda take faman dafe kanta dake mugun sarawa. Haka sukaita hawaye har sai da baba Abba ya fahimci Kaka na neman rasa numfashin ta. Sake ruɗewa yayi ya shiga girgiza ta jikinsa na rawa. Yama rasa miya kamata yay mata, kiran sunanta kawai yake iya yi da iya ƙarfinsa. Mami ta ƙara so wajen su da saurin tare da rungume Kaka tana kiran Sunanta.... da saurin Abba ya kira Dr suka duba kaka Allurar Bacci akayi mata kana nan take bacci ya yi Awon gaba da ita.... Wuraren 12:40am Doctors ya buƙaci ganin wasu a cikin su Abba. suka shiga office ɗin, aka bar Kaka kawai a ɗakin. Dr Halima ta ɗanyi gyaran murya tana kallon sauran ƴan uwanta uku likitocin. Kawuna suka ɗaga mata alamar bata damar magana. Ta amsa musu da kai itama tana sake gyara zamanta. Cike da girmamawa a garesu tace, “Dama munason muku bayani ne akan abinda ke faruwa idan bazaku damu ba”. Babu wanda ya iya ce mata komai a cikinsu. Dan haka ta cigaba da faɗin, “Maganar gaskiya yarinyar nan tana cikin mawuyacin hali, duk yanda mukaso ceto rayuwarta ma mun gagara, dan aikin yafi ƙarfinmu. Amma a yanzu dai abinda muka iya kawai shine jawo numfashin ta da wasu na'urori kafin a samu mafita. Muna Bukatar Babban likita da zai dubata, matsalarta, sai dai kuma ganinsa shine tashin hankalin musamman da ya kasance yana Aiki a Asbitin kansa dan haka munyi ƙoƙarin nemansa dan muji ko zai iya mana alfarmar ganinsa amma bai ɗaga wayar ba, sai dai mun kira ɗaya daga cikin ya ransa yanzu haka ya tabbatar mana zai bincika mana shi, idan har ya amince zaizo zamu iya ganinsa a koda yaushe. idan bai aminceba yana da wani uzurin kuma shi zaizo ya ga yarinyar ko zai iya bada wata mafita akan matsalar tata dan shima babban likita ne”. Cike da gamsuwa da bayaninta duk suka karɓa mata da “Allah yasa a dace” tare da musu godiya sosai akan wannan taimako da sukai musu. Daga haka suka tashi suka fito kowa yana addu'ar dacewa a cikin ransa... Mami ta kalli Abba Murya a raunace tace ,"Abban Haydar bazu kaita Asbiti n Sultan ba inaga haka zaifi" Murya a disashe Abba ya ce, saidai mu bari mu ga yadda hali Zaiyi!!" wasa Wasa har gari ya waye amma babu labarin likitan da ake tsumayen jira. Su kuma likitocin basuce musu komaiba. Haka suka cigaba da zama jugum-jugum suna addu'oi a zukatansu har tsahon wani lokaci. lokacin sallar Azzuhur ne ya sake tadasu suka nufi massallaci, bayan an idar da salla suka sake fitowa suka sake zaman jiran tsammani. Mami ta kalli Abba cikin Sanyi Murya tace ,"Abba Haydar ya kamata Mama ta koma gida ta huta tana buƙatar hutu sosai, Abba ya sauke Nannauyan Numfashi kana yace," Na kira Haydar yazo ya kaita gida, yana rufe bakinsa Haydar na isowa, fuskarsa cike da damuwa ya gaida iyayen nasa,da kyar Abba da Mami suka shawo kan Kaka ta yadda suka wuce gida.... Bayan ta fiyarsu lokacin ɗaya Abba da Mami suka sauƙe Nannauyan Ajiyar zuciya, haka suka shafe tsawon Awa ɗaya zaune a wajen ba wani labari.... "Abban Haydar da zaman jiran tsammanin nan da muke da mun wuce Asbitin Sultan tunda duk private hospital ne. "Ina ga haka za'ayi tashi mu tafi" Abba na ƙoƙarin miƙewa zuwa office ɗin Doctor Halima, sai kuma ya hangota tana fitowa da ga office ɗin nata fuskarta ɗauke da murmushi. Kafin ya samu damar mata magana yaga ta nufi ƙofar fita da hanzarinta. Kamar zai bita sai kuma ya fasa, ya cigaba da tsaiwa a wajen yana jiran ganin ko zata dawo wajen su... Tsayuwar tasa tayi dai-dai da shigowarsa cike da takunsa na ƙarfi da lafiya, wanda idan baka saniba zaka iya ɗauka tsabar isa ce da izza ke ɗawainiya da shi. Amma sam ba haka baneba, halittar tasa ce kawai haka. Kansa duƙe yake sakamakon file ɗin Sultana da ke a hannunsa yana dubawa. ga wani irin ƙwarjininsa da cikar haiba, Kamar kullum sanye yake cikin suit, na yau ɗin sun kasance Black color, Dr Aryan na gefensa Doctor Halima na daga gefen damarsa, da alama bayani take masa akan matsalar. Sai Nurse Yusra dake ɗauke da jikkarsa a hannu, da Doctor Nasir da wasu likitoci biyu da Nurse guda biyu na biye da bayansa. Har suka zo suka gitta Abba bai ga fuskarsa da ƙyau ba, dan har lokacin kan nasa a sunkuye yake ga file ɗin. A dai-dai ƙofar ɗakin da Sultana ke ciki suka ja birki, su Abba da duk suka zuba nusu ido duk suka miƙe, sai dai kafin wani cikinsu yace wani abu. Ya tura ƙofar ɗakin ya shige har lokacin hankalinsa nakan file ɗin...... Daga shi sai Dr Halima da Dr Aryan suka shiga . A hankali ya ƙarasa gab da gadon da Sultana take kwance sannan ya ajiye file ɗin ya kai dubansa gareta, bai ganeta ba sam, saboda na'urar da aka saka mata mai taimakama numfashinta fita. Ya ɗan ranƙwafo kanta kaɗan ya kai hannu ya zare na'urar mai haɗe da oxygen. Ba ƙaramin bugawa zuciyarsa tayi ba da sauri ya janye Glass ɗin idonsa ya ƙare mata kallo. da sauri ya maida na'urar saboda ganin yanda ƙirjinta ke sama da ƙasa da sauri-sauri ga jikinta na karkarwa har gadon kansa na motsawa. Luuu ya ɗanyi da idanunsa ya lumshesu ya sake buɗewa a kanta. murya a cinkushe ya dubi Doctor Halima a ɗan faɗace ya ke faɗin, “Anyi matuƙar sakaci da lafiyar yarinyar nan da har take neman shima matakin ƙarshe, A Rayuwarta 💔😥 (Allah ya baki lafiya Sultana🤲😥) Cikin ɗauriya yace ," Su waye suka kawo ta?" duk suna waje, Baice komaiba, ya dai sake kai dubansa ga Sultana, sai kuma yayi saurin ɗauke kansa batare da nasan dalilin yin hakan ba. Juyawa yayi zai fita. Doctor Halima tai saurin ɗaukar file ɗin da ya ajiye suka fita.... Kai tsaye ya wuce Babban Office ɗin ta aka tanada saboda manya baƙin lokitoci ake gaiyata aiki... komai tsab yake, dan tunda Dr Halima ta tabbatar da zuwan nasa ta saka aka sake tsaftace office ɗin duk da dama ƙa'ida kullum sai an share an goge. Gudun a girshe su... A hankali ya zauna sannan ya kunna Computer ɗin da ke a gaban sa . Yanda yayi matuƙar zuba idanunsa ga Computer ɗin zai tabbatar maka abunda yake yi a ciki yana da matuƙar muhimmanci. A haka Dr Halima ta turo ƙofar bayan tayi knocking ta shigo, Batare da ya ɗago ya kalleta ba yace, “Matsalar yarinyarnan babba ne, sai dai zan mata wani ƙaramin Aiki yanzun, dan haka ku shiryata zuwa theatre room”. Ya miƙa mata file ɗin gabansa yana cigaba da faɗin, “Wannan mahaifinta zai saka hannu anan, ko mahaifiyarta Kuma dole ɗaya da ga cikinsu ake buƙata kawai”. gyaɗa masa kai da faɗin “Okay sir”. Daga haka ta fice... Cikin girmamawa ta ƙarasa wajen su Abba Fuskarta ɗauke da murmushi tace, “Congratulations, mun samu nasara babban likitan da ganinsa ke da matuƙar wahala ya amshi gayyatarmu”. Cike da jin daɗi suka shiga faɗin "Alhamdulillah Allah mun gode maka!!" Da ga haka ta buƙaci magana da Abba Babu musu ya bita office. Bayani tai musu akan ƙa'idar saka hannu da Dr Sultan ya sanar mata, jikin Abba bar karkarwa yake ya ƙarɓi file ɗin ya saka hannu..... Bayan Abba saka hannun da Dr Sultan da wasu likitocin biyu sai Dr Halima ta uku suka shiga theatre room da Sultana da ko maƙiyinta ya ganta a wannan lokacin sai ya tausaya mata.... (Dr Sulta Allah yasa ayi aikin cikin nasara!!!💔🤲 Tsawon lokaci suka ɗauke a theater room ɗin Sai kusan ƙarfe takwas na dare dai-dai su Sultan suka fito, duk su Abba suka miƙe tsaye don son jin yaya ake ciki? Su Doctor Halima ne kawai suka tsaya musu bayani, dan Sultan yana ɗakin bai fito ba... A tare suka shiga faɗin Alhamdulillah Koba komai sunɗan sami kwanciyar hankali duk da ba cewa akai Sultana samu sauƙi ba, Su Dr Halima da suma fuskokinsu ke
Chapter 46 · 0% Book details