Sashe 34
Dr Sultan Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
sauraren masu tarar tasu ba ta shige sashensu da gudu tana ƙwalama Kaka kira. Da sauri Kaka dake ƙoƙarin fitowa taja baya dan kaɗan ya rage suci karo da Sultana Faɗawa jikinta tai ta ƙanƙameta tana faɗin, “Kaka, nayi kewarki ”.Kaka dake murmushi tasa hannu biyu ta rungumeta itama, sai da ta tabbatar sunji ɗumin juna kowa na sauke ajiyar zuciya kafin ta ɗagota da ga jikin nata. “Sultana! Yaushe ne zakiyi hankali kisan kin girma ne?,"Kaka daga dawota har zamu fara faɗa ko Cike da shagwaɓa ta karasa maganar tare.da saka kanta a kafaɗar Kaka tana faɗin, “Kaka ni indai ina gabanki Ni ƙaramar yarince, nayi kewarki ne my Happyness. Ina Mami take?”. "Maraba da yan Saudiya, Mommy ta faɗa cike da farin ciki da gudu Meena, Nana,Khalil Arif Haydar suka rungumeta," Mami munyi Missing ɗinki," Nima nayi missing ɗinku. Bayan sun janye jijin daga na Mami suka nufi wajen Kaka tare da rungumeta gabaki ɗayan su, "Mami ta kalli Abba cikin Sanyi Murya tace,"An dawo lafiya? Allah ya karɓi ibada" "Amin ya rabbi,mun same ku Lafiya. "Alhamdulillahi" Kana suka wuce cikin palon tsawa cak da Daddy ya yi hin an sauya komi na palon i zuwa sabo ya kalli Mami,"Lafiya? " Mami ta yi Murmushi kana ta ce ," Aikin Abban Sultan ne bayan ta fiyar ku da kwana ɗaya ya Turo masu aiki komi na gidan nan an sauya shi izu sabo hadda ɗayan ɓangaren na Uncle Ibrahim..sai yanzu maganar Daddy ta faɗo mai ɗaya taɓa tambatayar yana da ra'ayin sabo gida nan gaba, ya ce mishi a'a ya fito son gidan nan tunda ba shike dai keda shiba... Waton da wannan damar ya yi amfani ko, ya faɗa a hankali. Nan suka shiga jagayen gida. Ko'ina Ma sha Allah gwanin burgewa. tarba ta Musamman suka samu daga wajen Mami, Abinci sunci Saida suka ture, suna zaune a palon suna hira, Mommy ta kira Mommy tayi mata sannu da zuwa, bayan sun gaida Mommy ta sanar da ita sabon gidan da suka koma, cikin tsananin Murna ta taya ƴar uwar Tata murna.jin jima suna waya, bayan sun gama wayar ta kira Daddy shima ta taya shi murna, Nan Mami ta sanar da Abba da kaka Abinda ke faruwa, suma sosai sukayi Murna, duk da Abba ya sanda komi Amman bai haya ya nuna tsantsan farin cikisa ba...sun jima a palon suna hira yaushe gamo. Bayan sallah la'asar suka wuce gidan Mommy banda Sultana da Kaka.... Sai bayan Isha'i suka dawo a gajiye ko wannensu ya wuce ɗakin sa... *SULTAN* Bayan ta fiyar su Mami, ya dawo ɗakinsa ya yi Wonka ya shirya, a hankali ya zauna gefen gado tare da ɗaukar wayarsa ya kira babban Aminsa, Aziz kusan sati ɗaya kenan yana kiran sa wayar sa a kashe.yanzu ma a kashe take, cike da takaici ya wulgar da wayar gefe gado kana ya kwanta tare da Lumshe idanunsa yana mai jin zuciyarsa na mai nauhi da haka bacci ya yi a won gaba shi...Yauma kamar duk shekara da yake irin wannan Mummunan mafarkin da yake duk bayan shekara hakan ne ya sake faruwa dashi, sai dai na wannan karon ya sha babban da saura.. wannan Dattijo da yaga A Umura shine ya gani a mafarkinsa tare da wata kyakkyawar mata yana zauna a ge fensu da wata matsifar budurwa fusakar da lullɓe da farin mayafi. A hankali yarinƴar ta fara janye matafiya, dai dai kuma wata mata sanye da baƙaƙen kaya ta shigo ɗakin da matsifar guda Hannuta riƙe da ƙaruwar yuƙa Idanuwanta sunyi Masifar ja, gadan gadan ta tunkari Sultan tana zazzare idanunta masu matsifar ban tsoro. da ƙarfi ta ɗaga yuƙar zata soka mishi dai dai lokacin ya farka daga baccin da yake cikin wani irin ya nayi, wata irin Zufa ce me bala'in ɗumi ke sauƙo daga saman kanshi, cike da Razata da kaɗuwa, dafe kai ya yi dake junjuyawa......✍️✍️ (To wata sabuwa inji yan caca, ni dai nayi nan🏃🤣) *Assalamu alaikum! Ina matuƙar godiya da Addu'oi ku, da masu kirana, damu min text nagode sosai Allah ya bar zumunci!! Don Allah kuma a ci gaba da haƙirin reshin samun Update a Kai a kai. Nagode sosai* _More comments and share pls_ *Sadeeya Ka'oje ce* 💋 *DR SULTAN* (A heart touching love story)