← Book details Dr Sultan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 54

Sashe 30

Dr Sultan Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

ya amshi file kana tace. "Zauna bari inje Pharmacy in amso miki magungunan da alluran sai ayi miki". Kai kawai ta iya gyaɗa mata... da sauri Jidda ta bar wajen.bayan mintuna goma ta dawo tuni Sultana ta fara fita haiyacinta," kije ki mata Allurar, Jidda ta ware manyan idanuny," Sir Wallahi Bazan iya ba tsoron Allurar tsiyane da ita , Ta gefen idonshi ya ɗan kalli Sultana da keta durƙushe a wajen ɗaya. cikin bada murni ya ce ."Tazo". Da sauri Jidda ɗin ya juyo ya nufoshi, hannu yasa ya amshi allurar, kana ya ɗan kalleta a fakaice yace. "Zo nan". A hankali ta taso cikin sanyi takeyin taku tana matsoshi. A take kuma bugun zuciyarshin ya fara tsananta Taku biyu tayi ana uku yaji ƙirjinshi ya bar tsinkewar da yaketa yi ɗin, sai kuma bugun da yakeyi da sauri-saurin ne yaketa tsananta.da sauri ya dafe ƙirjinshi lokacin da ta iso gab dashi, cikin ranshi ya kuma cewa. "Ya Rabb" A zahiri kuwa, da kai ya nuna mata ta kuma matsowa, ba musu ta matso, yatsarshi ya jujjuya mata alamun ta juya mishi baya, still babu musu ta juya, a hankali ya murza kujerar da yake kanta, ya juyo ya fuskanci bayanta, dai-dai saman mazaunanta ta sama ta ɗan gefe kaɗan, ya saita, tsinin bakin allurar, cikin iyawa da gwarewa rumtse idanunta tayi da azaban ƙarfi sabida, wani zafi da taji yana ratsata, hannunshi yanada masifar zafine, Da ƙarfi tace. "Wach Allah na zafi-zaffi." Wani irin azaba taji lokacin daya fara sakar mata ruwan allurar a jikinta, babu zato babu sammani yaji tasa hannu damanta ta damƙe hannunshi dake mata alluran hannunta na hagu kuwa yarfashi take tare dasa kuka da sauti tace. "Wayyoo Allah na Zafi nake ji, bugun zuciyarsa ko tsananta yake, ya kusan hallakashi lokacin data riko hannunshi, da sauri ya tura mata ruwan kana ya zare Allurar da ƙarfi. Sannan ya miƙe tsaye, sabida muddin yana kusa da ita babu makawa wata ƙil zuciyarshi zata faso ƙirjinshi ta fito woje. Wani dogon tsaki yaja tare da juyawa ya bi gefen Jidda ɗin ya fice daga Office ɗin... da sauri Jidda ta riƙo hannuta suka fice ɗaga Office ɗin. Ta kaita ɗakin ta kwantar da ita nan take bacci ya yi awon gaba da ita... Sultan da sauri yake tafiya sabid iya yedda yake nesanta da ita iya yadda kirjinshi ke dai-dai ta bugawa, sai kuma tsinƙewa da zuciyarshi keyi... Bacci Sai Sultana ta yi sai ƙarfe Shidda ta farka, ba ɓata lokaci suka wuce gida, har gida Jidda ta kaita, sai lokaci ta tuna da wayar ashe cikin mota tabarta, Miss Call ɗin Mami da Kaka. Da Abba ba iyaka... lokacin da suka iso ƙofar gida Sultana ta kalli Jidda ta ce," me yasa zaki kai wajen Ɗan is..... "ya isa Sultana Jidda ta yi sauri dakatar da ita," to in ba iskanci ba zai sani a gaba yana mun tambayoyi, wannan sam bai dace da zama likita ba ɗan jarida yafi dace wa dashi... "Kai Nikam me Dr Sultan ya yi Miki kika tsaneshi haka, karfa ƙiyayyar da kike mai ta kowa so! Wata rana, " Allah Ubangijin ya tsare ni ko shine Autan maza a duniya Bazan zaɓa Auren sa ba!" (Ni dai nace Humm😅🤸🤣). Jidda ta sauke Nannauyan Ajiyar zuciyar,kana tace,"Allah ya kyauta" Ƙala Sultana bata ce mata ba ta fice daga motar ta nufi cikin gida... Kai tsaye bathroom ta wuce, tabbas kuwa baƙon ya iso, Wonka tayi kana tayi al'wala dan ko bata salla bata zama babu al'wala. Tana fitowa ta kimtsa jikinta kana ta zura tattausan doguwar riga. Tana kokarin fitowa falo Meena na ƙoƙarin shigowa da sauri Meena ta zaro ido tare da cewa. "Yaushe kika dawo?". Hararanta ta ɗanyi tare da cewa. "Ban sani ba" Cikin tausayawa Meena tace. "Sorry Anty Sultana Kai ta gyaɗa alamun gamsuwa kana tace. "Ya jikin naki Anty Sultana!" "Naji sauƙin" "Na dawo a guje fa, wannan Sultan ɗin hannunsa zafi. Zaro ido na mamaki Meena tayi tare da cewa. "Anty Sultana Shida kanshi ya miki?". Kai ta gyaɗa tare da cewa. "Eh". Cikin taɓe baki tace. "Lallai yau kin tashi da ƙafar dama, gashi kuwa naga har kin worke". Wucewa sukayi zuwa tsakiyar falon, cikin sauƙe numfashin Sultana tace. "Ba doleba Ko don mugutar da ya yi min dole na warke, Dariya Meena tayi tare da cewa. "Kinji allurar manyan likitocin da duniya keji dasu dai". Uhum kawai tace sannan suka fara cin abinci, sunaci suna hira. "Wai ina Mami da Kaka, "Barci suke, sai gab magriba kaka ta farka daga Barci ruwa ta watsa don taji daɗin jikinta... "Sultana ya jiki" "Lafiya lau Mami, tun ɗazu na dawo ai. su Khalil basu dawo ba har yanzu, "Mami Kinsan yau hadda suke sai 8 zasu dawo..." "Na manta Sam" A hankali Meena ta wuce ɗaki don yin Sallah, Sultan ta nufin ɗakin Kaka , koda ta shigo tana Sallah zama tayi tana karanta Askar a wayarta bayan ta kammala ta kunna Data tana chatting da Jidda dake tsokanarta.. Kaka ko bayan ta sallame sallah taci gaba da Addu'oi...har zuwa bayan Isha'i, ƙarfe 8:15 su Khalil suka dawo a gajiye,bayan sunyi Wonka suka ciki Abinci,kana kowa ya wuce ɗakin sa....., Sultan bai samu dawowa gida ba sai bayan magrib...haka kuwa ya shigo gidan rai a hade saboda tsabar gajia da yayi...driver na shigowa ya samu wuri yayi parking sanan ya bude motan ya fito saidai tun kafin ya zagaya ya bude mishi kofa mai Security yazo ya bude yana mishi sannu da zuwa, Sultan bai iya ce mishi komai ba sai hannu daya daga mishi kafin ya nufi cikin gida a yayi da fusakarsa zai baka daria sosai...ya lumshe idanunsa tareda dora kanshi shoulder din Mommy murya can kasa cikin yace"Mummy na gaji ta shafa kanshi fuskanta daukeda murmushi itama tace,"welcome back son..akwai gajiyan aiki koh"...ya ɗan tauna lips dinshi kana ya ce "Akwai gajia sosai Mommy.. "ina Salma da Salim?" "Sunyi Bacci tun ɗazu" je ka watsa ruwa kazo muci Abinci, jiki a mace ya wuce ɗakinsa ya watsa ruwa ya fito ya shirya cikin lallausar jallabiya yana zuba kamshi, ya fito palon ruwan tea kawai ya sha ya wuce ɗaki...... Haka Sultana ta kwana ranar cikin takaicin Sultan da jidda da duk ta tattara laifin a kan Jidda da ta kaita wajen Sultan ɗin, Bata da riko sam idan akai mata abu. amma sai gashi Jiya da yau Abun ya tsaya mata a rai da tarkacensa sun kasa barin ranta harma washe gari da shima dai haka ta yini babu walwala saboda jininin tana, Jidda tuni ta kama kanta don ko a Asibiti bata sakar mata fuska ba.... Washegari ya gama shirya kanshi cikin suit kaman ko yaushe ya nufi parlon Mummy don yin breakfast, A Gurguje ya yi Breakfast ya wuce Office. Cikin ƙanƙanen lokaci ya iso, bayan mintuna 5 Sultana ta iso kallon motarsa take tanan dalla mata Harara tare da jan tsaki.. kana ta wuce.... A hankali Rayuwa taci gaba da tafiya cikin kwanciyar hankali. cikin ƙanƙanen lokacin Sunan Sultan ya kaɗe duniya saboda kwarewar Aikinsa. Kowa yasan Dr Sultan haka yake, mutum ne mai ƙoƙari akan aikinsa da himma, ga tausayi sosai musamman ga marasa ƙarfi. Bashi da yawan magana idon ma kaga yana doguwar magana Murmushi to a gida ne, Wanda bai fahimcesa ba zaita ɗauka kamar girman kaine bisa ga ɗaukakar da Allah ya basa. Idan kuma ka fahimcesa zaka gane cewa haka halayyarsa take, shi kawai aikinne a gabansa ba shiririta da shashanci ba. Akance likitoci mafiya yawansu sunada son mata, sai dai ga Dr Sultan sam ba haka baneba ko a nan Asbiti ƴan mata da dama sun nuna mai so. Duk yanda matan ke binsa da soyayya shi bama su ishesa kalloba, shi fa a rayuwarsa damuwarsa kawai shine aikinsa, sai ko family ɗinsa da taimakon marasa ƙarfi. yanda yake gudanar da Rayuwarsa Allah ya ɗaukakashi a duniya a dalilin ƙwaƙwalwar aikin likitanci daya azurtashi da ita, likitane shi da kota wane fanni zai iya gunar da aikinsa akan mara lafiya, sai dai abinda ba'a rasaba kam, dan Allah shine mai komai da kowa. A ɓangaren Sultana ma sosai ta maida hankali ga Aikin ta... A dayan ɓangaren kuma Al'ummar musulmai tana faman shirye shiryen Azumin watan Ramadan...yau Azumi sauran kwana biyu, Daddy tun Azumi saura sati ɗaya yake rabon kayan Azumi da mabuƙata, A ɓangaren Abba ba'a barshi baya ba.... Washe garin washe gari. Da daddare watan Ramadan ya bayyana. Haka yasa dukkan ɗauka cin Musliman duniya suka cika da farin ciki tare da yin niyan ɗaukar azumin watan Ramadan ɗin, kana kowa yana shirya bukatunsa dan miƙa su ga Ubangiji Mabuwayi...✍️ Ina ma kowa Barka da jumma'a 🥰💖 _More comments and share pls_ *Sadeeya Ka'oje ce* 💋✍️ *DR SULTAN* (A heart touching love story)
Chapter 30 · 0% Book details