Sashe 15
Dr Sultan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*Page 11-12* _______fuskar ta ɗauke da murmushi ta ƙara so wajen sa tare da Rungume sa. A hankali ya sauke sassanyan Ajiyar zuciya. tare dai lafe a jikinsa tana shaƙar dadɗan khamshi mai daɗi, Lumshe ido tayi kana ta buɗe a kan kyakkyawar fuskansa, cikin Murya mai kama da raɗa tace ,"Sannu da zuwa Habibi!" A hankali ya Lumshe idon kana ya sauke sassanyan Ajiyar zuciya, cikin sanyi Murya yace," Yauwa Habibity!"A karon karfo ta saki murshi Mai ƙawatarwa, kana tace "Ya hanya? Numfashi ya ja kana ya fesar, cike da gajiya yace ," Alhamdulillahi!" "muje ciki kawatsa ruwa" Kana suka wuce ɗaki rike da hannun juna, kallon ɗaya zaka musu ka fahimci tsantsan so da kyauna da shaƙuwa mai ƙarfi, Masha Allah wani haɗaɗɗen daki suka shigo mai matsifar kyau, cikin tsananin kewa ya rungumeta nan take suka faɗa duniya masoya, kana sukayi Wonka tare, bayan ya gama shiri ta kallesa," Habibi ina zuwa kuma?" A hankali ya sake Ajiyar zuciya kana yace ," Gidan Abdullahi zanje nayi Masa gaisuwa!" "Gaskiya kam ya kamata kaje karya yi fushi da kai, ya ɗanyi Murmushi," Abdullahi bazai yi fushi dani ba saboda yasan Uzurin da ya riƙe Ni! " Wannan Gaskiya ne Habibi ba mai shiga tsakanin ku" tare suka fito daga ɗakin kai tsaye suka wuce darning,da kanta da riƙa ciyar dashi Saida ya ƙoshi kana ya shiga bata ita ma gwanin burgewa, "Yauwa ki haɗa min Abici mai ɗan ruwa ruwa zai kai Asbiti, "Subuhalillah Habibi waye ba lafiya?" Nan ya bata labarin abinda ya faru ,"Ya Allah ya jikin nashi"? Numfashi ya fesar kana ya ce ," Alhamdulillahi zanje gidan Abdullahi daga can zan wuce Asbiti" "Allah ya tsaye!" ", Amin ya rabbi Habibity ya faɗa tare da manna mata Kiss a hankali ya Lumshe idon, har bakin mota ta rakashi cikin girmamawa security suka Gaisheta fuska a sake ta amsa musu. "Barka da fitowa ranka ya dade!" "Yauwa Dogo, security suka buɗe mishi mota kana yashi a tsake suka fike daga gidan, kai tsaye suka wuce GRA, Suna isowa mai gadi ya buɗe musu gate a tsanake Dogo ya danna hanci matar cikin gida, dai dai lokacin Abdullahi ya iso fuskar ɗauke da murmushi ƙarfin Hali, "Sannu da zuwa Abdullahi ya faɗa cikin sanyi Muryar, saukar yaushe?" Batare da ya bashi amsar tambayar shi yace, " Ya ƙarin haƙiri!?" "Alhamdulillahi mun gode Allah!" "Allah ya gafar ta mata! cikin raunin Murya Abdullahi yace," Amin!" Kana suka wuce cikin gida kai tsaye suka wuce ɗakin Kaka, "Mama!!" Abdullahi ya kira sunanta cikin girmamawa" Kaka dake kwance saman lallausar Katifa ta mike.murya a disashe tace ," Abdullahi ƙara so mana" Kai a sunkuye ya shigo ɗakin ,"Barka da war haka Mama!" "Yauwa Abdullahi" "Mama ga Nuraddeen can Palon yazo gai sheki" Kaka ta sauke Ajiyar zuciya kana tace ,"wannan Abokin ka da kake bani Labarin?" "Ehh Mama shi koda aka yi rasuwa yana india dawowar shi kenan daka India" "Masha Allah" Tare suka fito daga ɗakin fuskar Kaka ɗauke da murmushi har suka ƙarasa cikin palon Abdullahi mai matsifar kyau, Suna isowa Alhaji Nuraddeen ya durƙusa har ƙasa ya gaida Mama cike da girmamawa da sauri Kaka ta dakatar da ta hanyar daga ƙafaɗun sa Kana ta zaunar dashi saman Sopa masu matsifar laushi, Fuska a sake Nuraddeen ya soma gaida Kaka tare da jajanta mata rasuwar Kubra, " Allah ya jikanta da rahama Allah yasa ta huta !" Suka Amsa da "Amin" Kana Kaka tace ya Iyali? " Lafiya lau mama" Mama ai Matar ce wannan dake kawo Abin tunda akayi rasuwar" cewar Abdullahi, "Allah sarki Allah ya yi Albarka, Allah yasa a gama Lafiya!"cikin tsananin farin ciki da Addu'ar suka amsa da "Amin" "Naji gidan shiru ina yara halam?" "Ina suna ɗaki Abdullahi ya bashi amsa" Dai dai lokacin Nana ta shigo Palon fuska a tsuke hannunta riƙe da tap ta yara," Kaka Kinga Khalil ya goge min Gama ɗina" sai kuma ta fashe da Kuka," zo Nan Nuraddeen ya faɗa tare da riƙe hannunta kana ya zaunar da ita saman ƙafafunshi, " Ki Dena kuka Kinji ya faɗa tare da kai Hannusa yana share mata Hawaye, sai gasu sun fito ga baki ɗayan su, da sauri Haydar da khalil suka ƙara so wajen tare da rungumeshi cikin tsantsan farin suka soma faɗin," Oyoyo "Daddy sannu da zuwa!" a hankali Maryam ta zauna kuka da Kaka, "Daddy yaushe kazo?" Cewar Haydar, "Banjima da zuwa ba" Daddy Ina kaje kwana biyu mun Dena ganin ka? " Tafiya nayi yau ɗin nan ma na dawo!" "Daddy Ina Mommy?" "Tana gida tace na gaishe ku gaba ki ɗayan ku, kuma tace yaushe zaku kuzo mata weekend? "Daddy yau Monday ran Friday zamu zo Weekend" "Yauwa Allah ya kaimu" "Amin Daddy" A hankali Kaka ta cewa Maryam je kicewa Azumi ta haɗo mata ruwa, a hankali Maryam ta kike kana ta wuce Kicin, "Abdullahi wannan kuma wace?" a hankali ya fesar da Numfashi kana yace ƴar Ibrahim ce Ƙane na!" "Allah sarki kasan ban santa ba Allah ya jiƙansu da Rahama!" "Amin ya Allah" Dai dai lokacin Azumi ta iso hannunta dauke da tire mai matsifar kyau kayan drinks ne ƴa ƴan itatuwa masu sanyi, "Sannu da zuwa ranka ya daɗe cewar Azumi" "Yauwa ya aiki" "Alhamdulillahi yanka ya fade" kana ta wuce, sosai yasha kayan marmarin kana suka ci Baga da hira zuwa na dan wani lokaci, Lokacin cinda zai tafi ya ba Su Haydar kyautar 100k Azumi kuma 10k kana ya yi musu sallama, har bakin mota Abdullahi ya raka shi nan yake sanar dashi daga nan Asbiti ya nufa ,"waye ba Lafiya. Nuraddeen?" Nan ya sanar dashi abinda ya faru, cikin tsananin damuwa ," Abdullahi yace Allah ya bashi lafiya ," Amin" kana ya shiga Mota suka fice daga gidan kai tsaye suke wuce Asbiti, tare da likita suka wuce ɗakin da aka kwantar dashi har zuwa yanzu bai farka ba, kallon yaron yaro cike da tausayi a Ranshi yake faɗin wa wanne hali yan uwanshi suke cike oho.... "Ranka ya daɗe ga kuje ka zauna" cewar Dr, "Bazai farka yanzu ba kenan? "Ranka ya dade da wahala gaskiya Allurar Bacci ka mai saboda ya nayin jikin sa yana bukatar Hutu sosai!" "Okay ba dawuwa Allah ya tasheshi lafiya!" "Amin" "Yauwa ga katina koda za'a buƙaci wani abun bana kusa" a hankali Dr ya karɓi katin tana kallon da sauri ya aware manyan idanunsa yana kallon sunan dake jikin katin NURADDEEN MAI NERAH! Cikin tsananin Mamaki yaci gaba da kallonsa mutumen da sunanshi ya kewaye da duniya,tabbas shine" a hankali Alhaji Nuraddeen ya ɗago ya kallonsa," Shi kowa sam Baisan Maganar ta fito ba, ya miike tare da barin ɗakin kai tsaye suka wuce gida..... Nuraddeen da Abdullahi tare sukayi jam'iya Nuraddeen Mahaifinshi Babban Attajiri ne kuma dan Kasuwa ne a Kano Nuraddeen shi kadaine ɗanda suka haifa Nuraddeen yana Ss3 Allah ya yiwa Mahaifiyar shi rayuwa, farkon shigarshi jami'a Allah ya haɗashi da Abdullahi kasan cewar Course ɗinsu ɗaya wasa wasa shaƙuwa mai ƙarfi ta shiga tsakanin su Nuraddeen yaro ne mai kirki da kyauta ga tausayi ga son taimako, yadda yake rayuwar shi da mutane sam ba Zaka dauka ɗan masu kuɗi bane rayuwar shi yake kaman kowa, shaƙuwar su tayi karfi sosai a makaranta ba wanda bai sannu ba baru wansu da ƴan mata karatun su suka saka a gaba, bayan sun kammala jami'a sukaci ga da zumunci su, Abdullahi baida wani Aboki a duniya kaman Nuraddeen haka shima Nuraddeen baida wani Aboki kaman Abdullahi duk abinda zasuyi sai sun shawarci junan su, Mahaifin Nuraddeen haka ya dauki Abdullahi kaman ɗan cikin sa, Mahaifin Nuraddeen mutum ne mai matsifar son yara, Haka Nuraddeen ma kusan halayen sa ɗaya da Mahaifinshi... Nuraddeen can waje yawacen ya wace shi ƙauyuka wajen taimakawa ta takkawa Allah ya haɗashi da Ummul khairi bafulatanar daji kyakkyawan da ita wasa wasa soyayya mai ƙarfi ta shiga tsakaninsu ba bata lokaci Akayi Auren bayan Auren su ya saka ta Kamaranta yaƙi da jahilci cikin ƙanƙanen lokacin ta fara waye a bangaren ilimin Addini ma har gida malami ke zuwa koya mata karatu, bayan Aure su da shekara Biyu Allah ya yiwa Mahaifin Nuraddeen rasuwa, Nuraddeen ya gaji duk a binda ya mallaka, tsawon shekara goma sha biyar kenan da sukayi Aure, Allah bai taɓa basu haihuwa ba, likitoci sun tabbatar musu da duk lafiyar su lau lokaci ne kwai bai yi ba, tun abin na damusu har suka barwa Allah, hakan yasa shida Matar shi suke tsananin son yara, zuwa yanzu Nuraddeen baida kowa sai matarshi da Abdullahi da ya kasance tamkar dan uwanshi haka ya dauƙi ƴa ƴan Abdullahi tamkar ƴa ƴan cikin sa wani lokaci a gidan shi suke hudu ko weekend. Kubra har ta raru basa shiri da Ummul khairi, saboda ƙashi da hassada da tasawa kanta ganin yadda Ummul khairi ta ke sharhiliya da dukiyar mijinta tare da ƙanwarta Ummul Kulsum,duk da ta kasance ƴar Attajiri matar Attajiri, Abdullahi duk da ya kasance mai kudi Nuraddeen ya kereshi shi da komai..... Wannan kenan....👌🙌🤗 Gab da maggariba ya shigo gida Kai tsaye ya wuce masallaci dake cikin gidan Saida kayi Isha'i kana ya wuce cikin gida cikin tsastsan farin ciki ta rungumeshi tare da manna shi hot kiss a kumatu, "Sannu da zuwa Habibi ya mai jiki ina fatan yaji sauki?" Ya sauke Ajiyar zuciya kana yace jiki da sauki!" "Masha Allah, Allah ya tashi kafaɗunshi Allah kuma ya baka ladan taimako, "Amin Habibity!!" Tare suka ci Abinci kana suka wuce daki, sukayi Wonka a tare bayan suna gama shirin suka kwanta rungume da juna nan take bacci ya yi awon ya gaba su...... *BAYAN KWANA HUƊU* Zaune suka a Palo suna hira Kaka ta kalli Abdullahi cikin sanyi Murya tace "Abdullah ya kama mu koma gida! Kodan makarantar Maryam kusan kwanan mu goma sha ukku kenan" Abdullahi ya sake Nannauyan Ajiyar kana yace," Mama don Allah karon nan ki dawo nan da zama Ko dan yaran nan! Kafin na samu mai kula dasu.don Allah Mama," nan take Idanunsa suka shiko da kwalla, Su Haydar suka haɗa baki wajen faɗin "Kaka don Allah karki koma ƙauye! Murya a disashe Maryam tace " Kaka Nima Bazan iya zama ƙauye ba