← Book details Dr Sultan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 54

Sashe 3

Dr Sultan Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

tayi,"Kaka service Ake cewa ba Sabin ba, duka ta ɗan kai mata tayi sauri kaucewa tana dariya, "Yauwa Mama gobe zan aiko da Direba ya kawo muku kayan Abinci ina fatan ba wata Matsala, "Ba komai Abdullahi Nagode sosai Allah ya yi maka Albarka," Amin Mama ki ƙara Haƙuri har yanzu Abubuwan sai Addu'a Nasara gane mike da mun Kubra, " Ba komi Abdullah Allah dai yayi maka Albarka tare da zuri'ar ka, " Ya su Nana "Lafiya lau suke, sun ɗan jima suna hira kafin nan sukayi Sallama, Tuni Maryam tayi Bacci, da kyar Kaka ta kaita ɗaki suka kwanta, Washe gari yau ta kasance Weekend ne, Maryam na zaune a tsakiyar gida tana Aiki zane zane nenta, sai faman Murmushi take, "Kaka Kinga na zana Ya Maleek, tayi Maganar tana nuna mara zanen da tayi," Dai dai lokacin Akayi sallama, "Kaka kaman muryar Direban Abba, "Aiko shine ji kice ya shigo, da sauri ta nufi wajen gidan," Kaka tace ka shigo, Binta yayi a baya har inda Kaka take zaune, "Mama ina kwana, "Lafiya lau Atiku ya Hanya"? "Lafiya lau Mama" suna gama gaisawa ya wuce waje ya shigo da kayan Abinci da yazo dasu, Maryam sai faman tsalle tsalle take tana jin daɗi, "Sannu da aiki Atiku ga ruwa ka sha ,"ba musu ya ƙarɓa ya sha tare da yi mata Godiya, "Ga wannan nan yace a baki 50k cike da farin ciki ta karɓi kuɗin tana mishi godiya, sallama ma yayi masu har ƙofar gida suka rakashi, sai lokacin Kaka ta samu daman kallon kayan, kayan Abinci ne kala kala da duk wani Abin buƙata yau da kullum, sai kayan saka kusan kala goma ita biyar zainab Biyar sai su sabulaiya da turarukka masu daɗin gaske, "Ya Allah kayi wa Abdullahi Albarka Allah ka kare a duk inda yake, ta ƙara sa maganar tana share hawayen da suka zubo mata,"Kaka kukan me kike? Murmushi ƙarfin hali tayi," Ba kuka nake ba Maryama, "Kaka me yasa duk Abba ya Aiko muna da kaya sai kiyin Kuka"? Nan take ya nayinta ya sauya, ta sauke Nannauyan Ajiyar zuciya mai zafi.... ★★★★ "Ya Maleek Sannu da zuwa, Ya Maleek Abba na Birnin ya aiko muna da kaya, "Kiyin kyau Maryama ta Ya faɗa a hankali sun kuyar da kai ta yi, "Uhmm Maryama An girma Kunya kike ji"? Murmushi ya sakan mata da taune Lip ɗin sa na ƙasa ya ɗage mata gira ɗaya da Lumshe idanunsa ya buɗe a kan fuskarta ya danyi murmushi tare da tsurawa furkarta ido, " Ya Maleek kayan nan Abba ya aiko min su, "sun Miki kyau sosai, "Nagode, A karon karfo ya saki Murmushi murya. sanyaye ya ce," Maryama ta an girma? Murmushi ta yi ta ɗan marairaice fuska cike da kula ta ce," Ya Maleek bai kai ne ka ce na rage yin surutu ba"? Suka ha ɗa Ido a karo na biyu, da ƙarfin zuciya taso janye Idonta Amman bai bata daman hakan ba cike da ƙwarewa ya Lumshe idanunsa ya buɗe a tsakiyar kwayar idonta, tsabar lamarin yazo mata a bazata tai saurin Janje idota, wani irin kwarjini ya yi mata.... Cikin tattausar muryar sa mai cike da sanyi ya ce ,"Muje gida, a hankali ta sauke Numfashi tare nema duk kan natsuwar, tana gaba yana biye da ita har suka iso cikin gida, ganin Kaka bata tsakiyar gida suka wuce ɗaki, ya yi Sallama, ta basu izinin shiga, koda suka shigo tana zaune a saman tallausar carpet ɗakin na fitar da wani irin fitinannen khamshi mai daɗin gaske, Cikin sanyi Muryar yace," Ina wuni, "Lafiya lau Kaka, " Zauna mana, a hankali ya zauna tare da lonƙosa ƙafarshi,ta hagu, kwanukan Abinci dake gefenta ta aje Nishi a gaban sa, "Sannu da Aiki Kaka!" Murmushi ta sakan mai, "Ya Maleek Ni ba zaka min sannu da aiki ba, tare mukayi girkin, "kwaɓe fusaka yayi cike da zolaya ya ce,"ke ɗin"?.sai kuma yayi dariya mai sauti, da ce wa, " Maryama an girma!" hakannen yasa Kaka Murmushi, " Kaci abin cikin ka Abdul Maleek" kwaɓe fusaka Maryam ta yi tana turo baki gaba tana ce wa," Ai Bazan ƙara ta yaki aiki ba, A hankali ya buɗe kwanon abinci wani irin khamshi mai daɗi ya daki hanci sa, Wani irin sassanyan Nunfashi ya sauke tare da Lumshe idonsa, "Ya Rabb" tuwon shimkafa ne da miyar taushe taji nama da kifi, sai man shanu, nan take ɗakin ya gauraye da ƙamshi, a tsanake ya riƙa cin abinci har ya kammala, Juyowa ya yi ya watsa mata narkakkun Idanunshi sa da bata iya gano mike cikin su, turo baki tayi tare da sunkuyar da kai ta murguɗa baki, "Taso muyi karatu, ba musu ta dauko littafanta sukayi karatu kaman yadda suka saba, "Kaka Nagoge zan wuce gida, "Ji mana Abdul Maleek!" a hankali ya zauna, "Abdul Maleek ya batun karatunka"? Nunfashi ya ɗan fesar cikin sanyi Murya ya soma faɗin," Kaka kuɗin ne bai gama kammalawa ba! kaka Makarantar tana da tsada sosai, " Abdul Maleek idon ka biye wa sai ranar da ka tara kuɗin da zasu isheka ba zaki karatu yanzu ba! Komai a hankali aka farashi, baka san me Allah zai yi nan gaba ba, yanzu nawa ka tara"? Nannauyan Ajiyar zuciyar ya sauke, " Kaka! dubu Ashirin ne a hannun yanzu, "Abdul Maleek, kana nufin tsawon lokacin nan da ka dauƙa kana aiki iya abinda ka tara kenan?, Rau Rau ya yi ido Kaman zaiyi kuka, "A'a Kaka! "Toh ya akayi suka zama 20k"? "daman kwanaki koda na dawo da shago na tarar da An ɓalle ɗakina! "Subuhalillah" kai ya jingiya cikin ya nayin da muwa yace," Wallahi Kaka duk kudin da na tara sun kwashe!" Nannauyan Ajiyar zuciyar Kaka ta sauke, "shine baka gaya min ba"? "Kiyi haƙuri Kaka!", "Allah ya tsare gaba ɓarayi sunyi yawa a unguwar nan, cikin yana yin Natsuwar sa da ya zame mishi jiki, yace "Haka ne Kaka, Allah ya shirye su! "Amin" " Kayi ƙoƙarin Abdul Maleek kar shekarar nan ta ƙare baka shiga makaranta ba, In sha Allahu Kaka zanyi ƙoƙarin, "Allah ya taimaka idon ka tara ra gowar sai na cika ma, "Nagode Kaka cikin yana yin natsuwar sa da ƙasaitarsa ya kalli inda Maryam take zaune,ya Lumshe ido ya buɗe a kan fuskarta, cikin sanyi Murya ya ce,"Kaka Saida safe, "Allah ya tashe mu lafiya, "Amin" Kai tsaye ya nufi ɗakinsa, ya watsa ruwa, a hankali ya fara jin natsuwa na saukar masa, karatun Alkur'ani ya yi kana ya yi Addu'a ya kwanta nan take bacci ya yi awon gaba dashi, can cikin Bacci ya fara ganin wani gaske mai bala'i ƙarfi ya kewaye wani ka tafaren wajen, wasu muta ne sanye da Fararen kaya za gaye da wannan hasken, daga can gefe wasu kyakkyawan ƴan mata ne tsaye ko wacce furkarta ɗauke da murmushi, ɗaya daga cikin ƴan matan ta soma kiran sunanshi ciki wata irin zazzaƙar Muryar mai cike da natsuwa," Abdul M.....!" dai dai lokacin ya farka daga baccin da yake cikin wani irin ya nayi, wata irin Zufa ce me bala'in ɗumi ke sauƙo daga saman kanshi, cike da Razata da kaɗuwa, dafe kai ya yi dake junjuyawa, ya sauke Nannauyan Ajiyar zuciyar mai ɗumi ya juya gefen hagu ya kwanta ta re da yin Addu'a ya sake juya hannu izuwa dama ya yi Addu'a... Sam bacci ya ƙi zuwa sai faman juyi yake cikin wani irin mummunan ya nayin da ke faruwa dashi duk lokacin da ya yi irin wannan markin da yake duk bayan shekara, karatun Alkur'ani ya riƙa cikin sassanyan murya mai cike da kasala.. cikin ikon Allah ya samu bacci ya yi awon gaba da shi......✍️✍️✍️ _More comments and share_ *Sadeeya Ka'oje ce*💋✍️ *DR SULTAN* (A heart touching love story)
Chapter 3 · 0% Book details