Sashe 53
Dr Sultan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
﷽ Bismillah........ ✍ PAID BOOK Littafin *DR SULTAN* na kudine akan 300 kacal , me bukatar ya karanta har karshe zai turo kudinsa ta wannan asusun 1490318334 Sadiya Attahiru kaoje Access bank ,sai a turo shaidar biya ta wannan number 08149979652. Nagode🤗 *💋TITAN'S OF TALENT💋* *Marubuta masu aiki da fasahar zamani , zalar ilimantarwa,fadakarwa dakuma nishadantarwa* *(T .O.T)* *Breathe in courage, breathe outfear, together we stand *Alkalaminmu abin alfaharn mu* https://chat.whatsapp.com/CuNxneQ0ONc6x9yn9a16Jj *The beginning* *Page 39-40* ____________"Adda Sal...Salma, dai dai lokacin a ka Turo ƙofar ɗakin, "Anty Ina key ɗin part ɗin Sultan? zamu saka kaya a ciki, ganin Mommy bata tanka ba yasa ta nufi wajenta ta sake cewa "Anty Lafiya? Sai kuma ta kai Idonta ga hoton da Mommy take riƙe da shi, Allah sarki Bappa da Nenne Allah ya gafarta muku, hawaye ta share cikin raunan'nanyar murya tace ,"Amin" "Amman Anty Me Hoton su Bappa yake a ɗakin Sultan?" "Ni ma ban sani ba" tsaye sukayi a ɗakin sunyi Zugum, kowa da abinda yake tsaƙawa a Ranshi, A ɓangaren Sultan ko zaune a mota yana jiran Atm ɗin sa shiru shiru har tsahon wani lokaci sai faman kiran Mommy yake aman ba'a ɗaga ba, hakan yasa ya nufi cikin gidan, batare da ya so hakan ba, tun da ya saka ƙafarshi a palon hankalin Mutane suka dawo kansa suna faɗin Maraba da Ango" cike tsakanin kunya ya nufi ɗakinsa, tsaye ya tarar da su sunyi cirko cirko, cike da tarin Mamaki ya riƙa binsu da kallon Musamman Mommy dake riƙe da Hoto, cikin ƙoƙarin danne abinda ke ranta tace ,"Sul.... Sultan na Barka a tsaye ko?" Makom ya bata Amsa, ya jefe mata tambaya ,"Mommy lafiya? mike damun ki?" A karo na farko ta saki Murmushin ƙarfin Hali Kana tace ,"Ba komi Sultan" Mami tace ta yi ƙarfin halin faɗin ,"Sultan ina kasan mutanen nan dake cikin hoton nan?" Nannauyan Ajiyar zuciya Sultan ya sauke kana yace ,"Mami Dengin Mahaifiya tace!!! " Cikin tsananin tashin hankali da ruɗu dake tattare da su," Mami tace Degin Mahaifiyarka Sultan? Wace Mahaifiyarka a ciki?" cikin raunatattiyar Murya yace," Ummul Salma!!!" Nan take hawaye Masu matsifar Zafi suka zubo Mishi, Kallon kallon aka tsaya yi tsakanin Mommy da Mami, dai dai lokacin Kuma Daddy ya shigo ɗakin, "Ina fatan Lafiya? Daddy ya yi maganar yana kallon su, "Sultan yanzu kana nufin kai ɗan Adda Salma ne!!!" Cikin wani irin yanayi ya gyaɗa musu kai, A karo na Biyu Daddy ya sake tambatayar Lafiya? Mami ta sauke Nannauyan Numfashi kana yace ,"Abban Sultan! Sultan ɗan Adda Salma ne Sultan ɗan yar Uwar muce.*A DALILIN SO* Muka zamo Tamkar *JINI ƊAYA* Daddy ya sauke Nannauyan Numfashi kana yace,"Allah mai Iko!!, Zama sukayi Ga baki ɗayan su, cikin tarin Ruɗu dake tattare da Sultan yace ," Mommy ku fahimtar dani mike faruwa" Mommy ta sauke Nannauyan Ajiyar zuciya kana tace..... *WAI WAYE A DON TA FIYA* "Alhaji Abubakar Siddi shine sunan mahaifinmu, haifaffen garin dawakin tofa ne dake jahar Kano, Asalinmu Fulani ne, Mahaifinmu babban Attajiri mai darin dukiya da garken Shanaye da tumaki, Matarsa ɗaya a duniya Zainabu yar Gwoggon sa ce, Mu Ukku ne a wajen iyayen mu, Kuma duka mata Ummul Salma, Ummul Khairi, Ummul Kulsum, mun ta so cikin kyaunar Junan haka muke Rayuwar cikin kwanciyar hankali da kyaunar juna, wata rana Bappa ya fita da safe zaije masallaci, yaci karo da wani kyakkyawan Saurayi Mai Suna kwance a ƙofar gida cikin wani irin Mummunan yanayi Ya shigo dashi cikin gida tare da bashi taimakon gaggawa, kwanansa Ukku yana jinya, bayan yaji sauƙi Bappa ya bashi masauƙi a gidanmu saboda ya fahimci saurayin Bai san kowa a garin ba, sannu a hankali shaƙuwa mai ƙarfim ta shiga tsakanin Bappa da saurayin har kiwo yake ma Bappa, ana cikin haka Soyayya mai ƙarfi ta shiga tsakanin Adda Salma da Abduljalil, Allah ya azurta da wani sirrin ƙyau mai fita da kwarjini. ba wani ɓata lokaci Bappa ya ɗaura musu Aure, tare da basu muhalli zama, Rayuwar suke cikin so da kyaunar Juna, Adda Salma ta jima bata haihu, Auren su nada shekara Huɗu aka haifi Abdulmalik, lokacin Ni kuma nayi Auren Kulsum tana gidana, Abdulmalik nada shekara ukku Kulsum ta yi Auren, itama Saida ta shafe tsawon shekara Ukku sannan ta samu ciki, lokacin da cikin ta ya isa haihuwa, nazo ta zauna a wajen Amman Nenne yaƙi yadda haka yasa Kulsum ta koma gida anyi dai dai Adda Salma ma nada ciki, kusan lokaci ɗaya suka haihu da Adda Salma, Kulsum ta haifi ɗa na miji aman baizo da rai ba, tashiga tashin hankali sosai, saboda gorin da take sha a wajen dengin mijin da suke kiranta juya,ganin Halin da Kulsum ta shiga na tashin hankali yasa Adda Salma ta saudakar da yarta ga Kulsum ita ko karɓi ɗa najimin matacce a matsayin nata... Ranar Suna Yarinya taci Suna Aminatu, da sauri Daddy da Sultan suka maida Kallonsu ga Mommy dake ci gaba da faɗin, ba wanda ya san da maganar daga Ni dai Adda Salma da Kulsum ɗi, Lokaci kafin Kulsum ta koma ɗakin ta, Kowa yaga Aminatu sai yace kamanninsu sak da Adda Salma, duk lokacin da akayi magana Adda Salma takan nuna musu ai ba wani Abu bane don Aminatu tayi kama da ita tunda duk Jini ɗaya suke, hakan yasa muke samu tsanuwa a ranmu, bayan Kulsum tayi Arba'in ta koma gidan mijinta... Ranar Kulsum ta cika wata ɗaya da koma a rar faɗa ya caƙuɗe tsakin fulani da makiyaya in da akayiwa iyayenmu da yanzuwan mu kisan gilla... Washe garin bayan faɗan ya lafa muka wuce rugarmu,mun shiga tashin hankali sosai, ganin gawar Bappa da Nenne kawai muka ganin, ba irin neman da bayiwa Adda Salma da Abduljalil da Abdulmalik, lugu da saƙo na rugugarmu mun neme su mun rasa, daga ƙarshe muka haƙura da neman su, satin mu ɗaya a ruga muka dawo Kano cike da kewar Yar uwarmu da muke rasa....... Mommy ta ƙara sa maganar cikin raunin Murya. Wannan kenan🤗 ★★★★_________ Meena dake tsaye bakin ƙofa tana jin duk abinda Mommy take faɗin, nan take jikinta ya soma rawa, daman tare suka zo da Mamk tashi ta shiru shine ta biyo bayanta ashe da rabon taji me suke faɗi, cikin wani irin yanayi ta buɗe kofar ɗakin ta shiga tare da faɗa wa cikin Sultan ta rugumeshi tana kuka mai tsuma zuciya, Wata iriyar zuface ke tsastsafo mishi bisa goshinsa, Kamar an watsa mishi ruwa. Ya kamo lip ɗin shi na ƙasa yana taunewa. Zuwa yanzu gaba ɗaya jikinshi tsuma yakeyi ta ciki. Kanshi ne yakeji yana jujjuya mishi Da sauri ya ɗago kanshi tare da ware matsakaita kyawawan idanunshi, idanunshi sun cika tab da ƙwalla sai sheƙi sukeyi alamun suna iya zubda ƙollan a ko wanne lokacin. Ita Meena sai ƙara shigewa jikinsa take tana shaƙar dadɗan khamshi turarensa... "Allah mai iko Daddy ya faɗa ya faɗa cikin wata irin murya mai cike ruɗu.yanzu da Sultan da Meena uwa ɗaya uba ɗaya suke, kai Mommy ta gyaɗa mike, Murya a rauna ce Mami tace ," Na jima ina zargin Sultan nada alaƙa damu duk sanda na kallesa nakan kammanin ya Abduljalil A tattare dashi,wani lokaci kuma ya kanyi min kama da Adda Salma" Murya na rawa Mommy ta soma tambatayar,"Sultan ina Adda Salma da ya Abduljalil?" Cikin ƙoƙarin danne kukan dake son kubce Mishi yace ,"Ammie na da Abie duk sun rasu!" da gan ya soma basu labarin rasuwar da sukayi tare da Mahaifinshin kafin ya rasu, Mahaifiyashi kuma bazai iya tuna komi a kanta, ko da abin ya faru yana ɗan shekara Shidda. Lokaci ɗaya suka sauke Nannauyan Ajiyar zuciya,"Allah ya jikan su da rahama Allah yasa sun huta!" "Amin" A hankali Sultan ya janye Meena daga jikinsa ya share mata hawaye kana ya sakar mata Murmushi ƙarfin lahi, sai yanzu ya gane dalin da ɗasa yake Masifar kaunar Meena ace jini ɗaya suke.... Cikin tsananin so ɗan Uwan nata tace "Ya Sultan idon an daura Aure zan dawo gidanka da zama!!" Murmushi ya sakar mata, "Allah abin godiya! Ina son maganar nan ta tsaya iya tsakanin muna, bana son kowa yaji har sai ranar da ya ce, "In sha Allahu Daddy!" Yauwa a je aci gaba da shirye shiryen, Cikin mutuwar jiki Sultan ya fice daga ɗakin tare da Daddy. _____________★★★★ Haka a ci gaba da shirye shiryen Ta ko wanne Ɓangaren, yau jumma'a sun safe ake ta shiryen shiryen walima,. Tsab Sultana tai shiri da kayan da jidda ta kawo mata ɗakin Mami . Lass mai matsifar kyau da tsada sky blue da akaima ɗinkin riga da zani. Ya zauna mata ɗas a jiki tare da haskaka farar fatarta daketa ƙyalli. Ƴar ramar da tayi sai ta sake fiddo ainahin dogon hancinta da manyan idanunta masu matuƙar haske da cikar gashi. Turaren ta fesa tana zuba uban ƙamshi tamkar tayi wanka da turare. Gashi cakuɗasun da tayi sai ya bada wani irin shu'umin ƙamshi mai narkar da zuciyar mai shaƙa.Ta saka sarƙa da sauran kayan adon sannan ta ɗauki blue gyalen da aka haɗo mata da shi ta ɗora a kafaɗarta. ta zira flat shoes ɗinta suma blue. Tayi ƙyau sosai tamkar ka saceta ka gudu. Su jidda ma tuni sun kammala shirin su tsab, Ana idar da sallar la'asar mafi yawan mutanen dake cikin gidan suka fice wajen walimar. Anguwar tayi tsit bakajin komai sai karatun alkur'ani, Alhamdulillahi, anyi taron walima an tashi lafiya, inda malamai suka yi wa'azi masu ratsa jiki ga ma'abocin saurare. Gaba ɗaya an gina sune akan zaman aure da kurakuran da muke tafkawa a cikinsa da hanyoyin magancesu, inda amarya da angonta sukasha addu'oin fatan alkairi da zaman lafiya, Tunda aka tashi da walima jikin Sultana sai ya sake yin sanyi, Palon Abba ta nufa sallama, daga ciki suka amsa mata da bata iznin shiga. “amarya da kanta. Miya farune?”. mami ta faɗa tana murmushi. Kallon Kaka da batace komaiba Sultana tayi, sai kuma ta duƙar da kanta hawaye na cika mata ido. Mami tace, “Kinga zonan”. mamana! tai a hankali zuwa garesu, ta zauna a ƙasa jikin ƙafafun Kaka data cigaba da abinda takeyi tamkar batasan da shigowar Sultana ba. "Anty Sultana gobe War haka kina gidan ya Sultan! hawaye suka gangaro