← Book details Dr Sultan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 54

Sashe 5

Dr Sultan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*(T .O.T)* *Breathe in courage, breathe outfear, together we stand* *Alkalaminmu abin alfaharn mu* *Page 5-6* _________ A karon farko ya saki Murmushi wanda ya fito daga ai nihin zuciyarshi, Nunfashi Kaka ta fesar tare da sauke Ajiyar zuciya, Kana tace "Maryam tashi mu tafi gida dare nayi, a hankali ta ɗago idanunta suka sarƙe da na Abdul Maleek daya wani irin zuba mata matattun idanunsa da suka sake can launi izuwa ja ko ƙittawa baiyi, cikin wani irin yanayi na tsananin kunyarsa da take a kwana nan, tayi sauri janye Idonta daga nasa, cikin sanyi Muryar mai dauke da kunya tace ," Ya Maleek Saida safe" jin Muryar Kaka ta faɗin," Abdul Maleek zamu tafi Allah ya ƙara sauƙi!, " Mu tafi Kaka" Jin Muryar Maryam ta ratsa dodon kunnesa ya yi sauri Lumshe idanunsa, tare da sauke sassanyan Numfashi, " Kaka bari nazo na raka ku, "A'a Abdul Maleek yi zaman ka kaida baka da Lafiya,"Kaka bana jin komi yanzu, "a'a Abdul Maleek" tana kai ƙarshe Maganar ta ja hannu Maryam suka fice daga dakin kai suka wuce gida.... A hankali ya sauke Nannauyan Ajiyar zuciya, tare da fesar da Numfashi mai Zafi, nan abinda ya faru da shi ya riƙa dawo mishi a kwakwalwa, "Ya rabb" ka kareni daga wannan mummunan Al'amari, narar yabaki ɗaya bai runtsaba, haka ya kwana yana nafilfili tare da kai kukan sa ga Allah sai gab da Assuba mai mai daɗi yayi awon gaba da shi...... A ɓangaren Kaka ma ranar bata runtsa, Washegari tunda sassafe ta wuce gidan Liman, dai dai lokacin zai shiga gida dawowar shi kenan daga masallaci, "Mama ina kwana, ya faɗa cike da girmamawa, "Lafiya lau malam liman ya iyali," Alhamdulillahi Mama" "Mushiga daga ciki" yayi maganar tare da nuna mata ɗan ƙaramin ɗakin dake suka dasu, Bayan sun shiga sun zauna, Mama ta Kalli Malam liman, ta sauke sassanyan Nunfashi cikin sanyi Murya ta soma magana," Malam Liman batun Abdul Maleek ne, lamarin nashi sai ƙara tsauri yake, nan ta shiga bashi labarin abinda ya faru jiya, Ajiyar zuciya Malam Liman ya sauke tare da kallon Kaka da jikinta duk Ya yi sanyi, "Mama tabbas akwai wani babban Al'amari dake tattare da wannan yaro! Daga ɗayan Ɓangare kuma kwai masu son cutar dashi, jin haka yasa a tsorace ta zaro ido jin Abinda Malam liman ya faɗa" Malam liman wannan wane irin Al'amari ne?" " malam Liman Meye ma fita yanzu?" Kaka ta faɗa a rauna ce, "Mama mafita ɗaya ce ya dage da Addu'a saboda rayuwar shi tana cikin hatsari mudɗin miyagun mutanen nan sukayi nasara a kanshi, "Innalillahi! Allah ka tsare shi daga Sherri su..." "Amin ya Rabbi Mama ina Abdul Maleek ɗin yake? Nunfashi Kaka taja kana ta fesar, cikin tsananin damuwa da tashin hankali da take ciki Murya a dishace ta ce,"yana ɗakin sa, komi Malam Liman bai sake cewa ba, rubuta ya somayi a allo cike da natsuwa bayan ya kammala ya wonko da ruwan zam zam kana ya zuba su cikin gorar ruwa, " Yauwa Mama ga wannan ya riƙa sha yana shafe jikinsa, hannu biyu Kaka ta karɓi gorar ruwa cikin tsananin farin ciki ta shiga yi mai godiya, da sauri ya da katar da ita cikin girmamawa ya soma magana"Haba Mama miye abin godiya ai yiwa kaine, mahaifin ya Ron nan kafin Allah yayi mashi rasuwa munyi zaman mutunci dashi Allah dai ya tsare shi daga sharrin miya gun nan, "Amin ya rabbi Malam Liman" "Ke ma Allah ya biya ki Mama yadda ki kayi tsayin daka akan Abdul Maleek Allah ya ƙara Miki lafiya da nisan kwana!" "Amin Allah ya yi Albarka!" har ƙofar gida ya rakata kana ta wuce gida cike da ƙwarin Quiwa, tana gab da shiga gida Abdul Maleek ya iso fuskar shi ɗauke da murmushi kallo ɗaya zaka mishi ka fahimci akwai reshin isasshen bacci a tattare dashi, cikin sun kuyar da Kai da Muryar shi dake dishace har yanzu yace " Kaka ina kwana,"Abdul Maleek an tashi lafiya?" "Lafiya kau Kaka, " ya jiki?" haka ta riƙa jerin mai tambayoyi yana bata Amsa, kana suka wuce cikin gida, da guda Maryam ta ƙaraso wajen shi ta rugumeshi ya ɗanyi baya kaman zai faɗi, "Ke kiyi a hankali fa karki kada shi, cewar Kaka, Kai ta cuta cikin ƙirjinsa tana shaƙar dadɗan khamshi mai daɗi, cikin wani irin ya nayi mai cike da kasala ya fara janyeta daga jikinsa, " Ya Maleek! " Hakan yasa ya buɗe idanunsa cikin sauri ya janyeta daga jikinsa tare da matsawa gefe kallo ɗaya yayi mata ya kawar da kai gefe, maryam ta Lumshe ido ta buɗe akan fusakar sa, " Ya Maleek jiya bakayi bacci ba?" Juyawa ya yi ta re da kallon Kaka, cike da tsuke fuska yace, "Nayi!" Kallon Mamaki kaka ke masa, Wani irin kallo ya watsa mata cikin ɗaya girarsa ta sama," Kiyi sauri mu wuce makaranta, a Gurguje suka karya, kana Kaka ta bashi ruwan maganin ya sha ba tare da yasan na miye ba, saboda ya san kaka bazata cutar da shiba bayan ya sha ya shafe jikin sa, kana suka fice daga gidan, yana kaita makaranta, kana ya wuce kasuwa...... A hankali kwanaki sukaci gaba da shuɗewa, ya yin da Kaka taci gaba da ba Abdul Maleek rubutu da Malam Liman ke aiko mata duk safe, a ɓangaren Abdul Maleek da Maryam shaƙuwar su sai ƙara ƙarfi take..... tunu Su Maryam sun kammala jarabawar su, Ranar da ta karɓo sakamakon ta, Ranar kowa ya shaida saboda tsananin farin ciki da take ciki, Ƙasan cewar ta ƴarinƴa mai kwazo tun shigarta makarantar ita ke dauƙar na ɗaya a class ɗin su, duk da sunyi Hutu kullum dare sai sunyi karatu kaman yadda suka saba, a ɓangaren islamiya tana daya daga cikin yara masu kwazo da hazaƙa, tana daga da cikin wa ƴanda zasu sauke a shekarar nan.... *WAIWAYE ADON TAFIYA* Malam Aliyu Gwani shine cikakken sunan mijin Kaka, Babban Malami ne mai tarin ilimin Addini, daya taka muhimmiyar rawa a duniyar Musulunci, Kasan cewar ya yi gwagwarmaya Rayuwarsa ta neman ilimin lokacin ƙuruciyar shi a garin ƘARAYE ta jahar Kano , hakan yasa ake kiran sa Malam Gwani Ƙaraye, matar sa ɗaya A duniya Maryam (Kaka) wanda ta Kasance ƴar Gwoggon sa, Ƴaƴansu biyu Abdullahi shine Babba sai Ibrahim Mahaifin Maryam dun daga Ibrahim Kaka bata sake haihuba, haka suka ci gaba da renon yayan su cikin kwanciyar hankali Abdullah da Ibrahim sun taso cikin haɗin kai da tausayin juna da kyaunar junan su hakan yasa iyayayen ke tsakanin son su komai a tare suke, Haka kwanaki suka ci gaba da shuɗewa zuwa yanzu Abdullahi da Ibrahim sun zama samari, tuni sun kammala secondary school, har Abdullah ya tafi jami'a, Ibrahim kuma ya ci gaba da neman ilimin addini a wajen Mahaifinsu, ya Rayuwa ta yi ta tafiya cikin kwanciyar hankali, Abdullahi bayan ya kammala jami'a Malam Aliyu Gwani ya basu jari suyi kasuwanci cikin hukunci Allah kasuwancin su ya fara ha ɓaka ciki suka biyawa iyayen na su aikin hajji, Koda suka dawo sun gida musu guda dai dai da na masu kuɗin ƙauye, suna da kamfani da ke sarrafa shimkafa kan farashi mai sauƙi kamfanin su sanannen kamfanin ne saboda sauƙin kayans su, wanda suka saka wa *GWANI RICE LMD* Zuwan da Abdullahi yake a birni nan Allah ya haɗashi da Kubra Galadima mafinta babban Attajiri ne kuma sananne, itace ƴa ɗaya tilo a wajen sa, Kubra yarinƴa ce da tashi cikin gata, tun tana kara Mahaifiyarta Allah ya yi mata rasuwa wajen haihuwa, cikin ƙanƙanen lokaci Soyayya mai ƙarfi ta shiga tsakaninsu, ba wani bata lokaci kayi buki taro ya tashi lafiya, Ranar su Kaka suka kai masu ziya a birnin sam basu samu tarɓar kwarai ba daga wajen Kubra daga karshe dai suka tattara kayan su suka dawo ƙauye, bayan Auren su da wata biyu Allah ya yiwa mahaifin Kabra Rasuwa, sun shiga tsakanin tashin hankali hakan ya haifar da zubewar ɗan ƙaramin cikin da take ɗauke da shi, saida ta yi jinya a Asbiti tsawon sati biyu, haka suka ci gaba da rayuwa, cikin kwanciyar hankali Azziki tana haɓaka, tsawon shekaru biyu kenan da Auren, zuwa yanzu Ibrahim ya zama cikekken Malamin Addini kaman Mahaifinsu, a dayan ɓangaren kuma babban Attajiri a ƙauye su, lokacin Hauwa'u ta kawo masu jiya ɗayar ƙanwar Kaka, Yarinya ce kyakkyawa ga natsuwa da kunya, soyayya mai ƙarfi ta shiga tsakaninta da Ibrahim hakan ya yi wa Kaka daɗi Kasan cewar ƴar uwarci ce ta ko'ina, bada ɓata lokaci ba akayi bukin su, suka tattara kuka wuce Birni Kasan cewar gidan su a haɗe yake, a lokacin Kubra ta shiga da muwa da jin gida ɗaya zasu zauna da Ibrahim, tunda Hauwa'u ta tare a birni bata jituwa da Kubra kullum cikin hantarar Hauwa'u da zaginta taken da ita har Ibrahim ɗin ita a tunaninta dukiyar Abdullahi suke so, don bai taɓa gaya mata dukiyar su a haɗe take ba, saboda Ibrahim ba dukiyar ce a gabanshi ba, Hauwa'u da Ibrahim Rayuwar suke cikin tsananin farin ciki da kyaunar juna... Kubra tun barin da tayi bata koma samun ciki ba, lokacin da ta fahinci Hauwa'u ciki gare sosai hankalin ya tashi ƙiri ƙiri take nuna tsanar cikin, Abdullahi sam baya jin daɗin halaryar Kubra haka Ibrahim sukaci gaba da renon cikin su cikin kwanciyar hankali, har Allah ya sauketa Lafiya ta haifo Kyakkyawar ƴarta, murna wajen Abdullahi ba'a ko magana, narar suna yarinƴa ta ci sunan kaka Maryam, Kaka ta hana a saka mata laƙani, wani lokaci su kira Maryam ko Mamana, Maryam nada sheka ɗaya Allah ya yiwa Malam Gwani Rasuwa, ba ƙaramin tashin hankali suka shiga ba, wannan lokaci Kaka tai kaman ta zare don ƙiɗima, Abdullahi shine ya zame musu Mahaifinsu bayan rasuwar malam Gwani ya kama mahaifiyar su ɗa danwan shi, suka haɗa kansu ba mai jin su sai Allah suna kyaunar junan su matuƙa da mutunta juna, komai zasuyi sai sun shawarci juna, bayan Kaka ta gama ta kaba ba yadda basuyi ta dawo birnin ba taƙi haka suka haƙura suka barta, lokacin lokacin sukan kai mata ziyara, itama takan kawo musu ziya, idon yazo har ta koma ba wani a bin ƙirƙi dake shiga
Chapter 5 · 0% Book details