← Book details Dr Sultan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 54

Sashe 35

Dr Sultan Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

_💖Story And Written💖_
⬇️
*Sadeeya Ka'oje*

💖الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر💖


Bismillah........ ✍

PAID BOOK
Littafin *DR SULTAN* na kudine akan 300 kacal , me bukatar ya karanta har karshe zai turo kudinsa ta wannan asusun 1490318334 Sadiya Attahiru kaoje Access bank ,sai a turo shaidar biya ta wannan number 08149979652. Nagode🤗

*💋TITAN'S OF TALENT💋*

*Marubuta masu aiki da fasahar zamani , zalar ilimantarwa,fadakarwa dakuma nishadantarwa*

*(T .O.T)*
*Breathe in courage, breathe outfear, together we stand*
*Alkalaminmu abin alfaharn mu*
https://chat.whatsapp.com/CuNxneQ0ONc6x9yn9a16Jj
*The beginning*
*Page 25-26*
_________cikin wani irin yanayi mai tsanani ya miƙe zaune tare da dafe kanshi, yayi bala'in fita hayyacinsa saboda wahala ya kasa bari ya huta. Sai da yayi wujiga-wujiga da shi, daga ƙarshema ya yanke jiki ya faɗi.
             A take wasu hawaye masu zafi suka shiga gangaro masa a fuska, ya shiga taunar lip ɗinsa ƙirjinsa na sake zafafa, dai dai kuma Daddy ya shigo Dakin da niyar ya faɗa mishi ya kamata ya leƙa Asibiti gobe. da ƙarfi yaja ya tsaya ganin Sultan kwance a ƙasa ga baki ɗaya baya cikin Haiyacinsa ba abinda ya faɗo masa a rai sai wannan mafarkin da Sultan yake duk shekara, kusan sau Ukku abun na faruwa a gabansa lokacin idon ya kai masa ziyara a India.
Duk da Daddy yasan da yanayin na Sultan sai hankalinsa ya sake ƙololuwar tashi fiye da da can. Wannan al'amari na Sultan na bashi tsoro.. Allah shine yasan gaibu game da matsalar Sultan. To a yanzu gashi al'amarin nasa ya sake motsawa, duk da yakan jima baiyiba ma.
Daddy ya nufi wajensa da sauri ya ɗora kansa Sultan samar cinƴarsa tare da shafa kanshi Cikin murya mai cike da lallashi ya kira sunansa ,"Sultan!".Duk da yana jinsa bai motsa ba, da ƙyar ya miƙa Zaune Daddy da kansa ta shiga toilet ta haɗa masa ruwan wanka mai ɗumi sosai. Kafin ta dawo inda Sultan yake ke rungume da shi yanata faman lallashinsa da masa magana mai daɗin gaske, wadda ko ba'a faɗaba da alama tana tasiri ga Sultan ɗin.
★★★
Mommy ko jin shuru Daddy ya jima yasa ta biyo bayansa, a hankali ta tura ƙofar ɗakin ta shiga,aiko da sauri na nufi wajensu ganin Halinda Sultan ɗin yake ciki.Zama tai kusa dasu itama, ta miƙa hannu ta riƙo na Sultan ɗin tana murmushin jin daɗin ganin ya nutsu,  matsawa tai jikinsa sosai zata rungumesa kamar yanda Daddy yayi masa, sai ya ƙwace hannunsa ya miƙe zumbur Cike da Kasala. ya nufi toilet.
Duk binsa da kallo sukai ita da Daddy, "Abban Sultan mike da munsa?"
"Ina tunanin wannan mafarki ya sake yi,
Juyowa tai idanunta cike da ƙwalla, muryarta na rawa tace, “Habiby! Anya kuwa bazamu nema masa magani ba,
  Daddy dake kallonta ya ɗanyi Murmushi yana nazarin maganarta, sai da yaja tsahon lokaci kafin ya amsa mata. “Shawaranki mai ƙyaune Habibaty, Na jima ina tunani akan haka na tabbata akwai wani babban Al'amari dake tattare da ɗan naki.
     Kafin ta samu damar bama Daddy amsa Sultan ya fito daga toilet ɗaure da towel, dan duk zatonsa sun fita. Turus yaja ya tsaya yana kallonsu ya maida ƙifar toilet ya rufe, jingina yayi a jikinta ya lumshe idanu zuciyarsa na ƙara bugawa.      
Daddy ya Kalli Mommy," Kinga tashi mu tafi yaron naki kunyar fitowa haka yake a gaban mu. Badan Mommy taso hakanba ta yarda suka fita.
A hankali ya buɗe kumburarrun idanunsa dake cike da barcin da baisan ranar yinsaba, ya sake lumshesu yana sauraren yanda Daddy ke lallaɓa Mommy akan su fita su bashi waje ya shirya, idan yaso saisu dawo daga baya.
Sultan najin sun fita shima ya fito sai da ya leƙo ya tabbatar babu kowa sannan ya fito. Bai kalli ko inda Mirror ɗinsa yake ba balle ai tunanin shafa mai ya nufi wajen kayansa kawai. Dogon wando black mai taushi da farar t-shirt data kama jikinsa ya saka. Ya taka zuwa gaban gadon yana cije lips ɗinsa, A hankali ya sauke Nannauyan Numfashi, tare da dafe ƙirjinsa da ya yi masa nauhi."Ya Allah ya faɗa da ɗan ƙarfi.
Har rige-rigen shigowa ɗakin Yanda sukagansa a kan gadon ya saka hankalinsu sake tashi, suka zagayesa da tambayoyin yaya akai? Yanda jikinsa ke rawa zufa na fito masa sai duk tausayinsa ya sake kamasu, Mommy tai saurin zama ɗaya gefensa tare da kwanciya a jikinsa tana hawaye. Zama Daddy ya yi a gefe suka saka Sultan ɗin a tsakiya, Daddy ya fara tofa mishi Addu'oi a hankali ya fara sauke Ajiyar zuciya.a hankali a hankali ya fara samun natsuwa, haka suka ci gaba da zama a ɗakin har Sultan ya yi barci.....
Washegari
A hankali ya buɗe idonsa wanda su ka ma sa nauyi saboda gajiya, ya rufesu saboda hasken da ya karaɗe ɗakin yaiwa idonsa ƙarfi. Ɗan wasu daƙiƙai ya ɗauka kafin ya sake buɗe idon a karo na biyu.
Lokaci guda kuma mafarkin da yai ya dawo ma sa. Da sauri ya tashi zaune saboda tunowa da yai da abinda ya gani a mafarkin. Agogo ya duba ya ga ƙarfe goma na safe, kenan ya jima yana barci. Idan ya tuna da kyau to ba maganin bacci ya sha ba jiya. Ya shigo ɗaki, Wonka ya yi ya sanya jallabiya ya gabatar da sallar.Assuba
Fitowar da zai yi bayan ya shirya cikin ƙananun kaya baƙar shirt da guntun wando baƙi na jeans ya haɗu da Ihsan tana haurawa sama.
Ya Sultan ina kwana" Ta faɗa a hankali
" lafiya" ya faɗa ba tareda ya kalleta ba.
Ihsan ta bishi da ido tana haɗiye wani abu mai ɗaci da ya taso ma ta tun daga wuya.
Wajen Daddy ya nufa
my Boy" Dad ya faɗi lokacin da Sultan ke ƙoƙarin zama a ɗaya kujeran.
Zuwa yai ya tsugunna a gaban Daddy Daddy ya shafa goshinsa ya ce "Allah ya ma ka albarka"
Sultan ya amsa da Amin
"Ya jikin na ka?"
"I'm fine Daddy"
"Allah ya ƙara sauƙi"
"Amin Daddy".
"Mommy Ina kwana"
"Lafiya lau ya ƙarfin jik?"
"Alhamdulillahi Mommy!".
Tare sukayi Breakfast cikin kwanciyar hankali, ranar dai a gida ya yini har dare...
Washegari cikin ikon Allah ya wayi gari da walwala kaman ba shine a ka sha fama da shi da Daddare ba. Wuraren ƙarfe huɗu ya leƙe Asbiti tarba ta musamman ya samu daga wajen yaran sa, A ɓangaren Aiki kuma Alhamdulillah komi na tafiya yadda ya dace sai bayan maggariba ya dawo gida..
Bayan Isha'i Sultana na zaune a ɗaki suna chatting da Jidda, kira ya shigo a wayarta. Kiran na gab da tsinkewa ta ɗaga ba tare da tayi magana ba, daga can ɓangaren ," Assalamu Alaikum ya yi maganar cikin wata irin zazzaƙar Muryar mai Amo,da sauri Sultana ta mike zaune tare da faɗin ,"Waye?"
    My Sweetheart kenan, abinda ka ke so ai duk wuya duk rintsi sai ka samu"
"Chan ta matse ma ka" ta faɗi tareda kashe wayar.
Ya sake kira ba ta ɗauka, "nace waye wai?"
"NAS NE!!"
"Sultana haƙiƙa Ƙaunar acikin Zuciyarta tamkar ta bo ne da yuƙa mai ƙarfi ta yishi gogewar warsa Abu ne mai matukar wahala ina ƙaunar ki! Bani da burin daƙushe Miki farin cikin ki koda na second ɗaya ni ki ɗauke cewa yanzu ne kika samu mahaɗin Rayuwarki bani da wani a buri a Rayuwa da wuce na hanki cikin farin ciki!!!"
Jikin Sultana ya yi sanyi, sosai kalamansa suka ratsa Zuciyarta,
A hankali a hankali NAS ya cigaba da kiran Sultana, tun tana ƙin ɗauka har ta koma idan ta ɗauka za ta surfa ma sa masifa, shi kam da gaske ya ke dan haka bai damuba duk abinda za ta ce ma sa shanyewa ya ke. Cinkin ƙanƙanen lokaci sai da ya san yadda ya ja hankalin Sultana har tana ɗan kulashi ta dena ma sa faɗa idan ya kira. A dayan ɓangaren kullum sai ya Turo mata massage na kalaman soyayya masu ratsa zuciya katin waya ma sai ta ture duk bayan kwana ukku sai ya Turo mata katin 5k...
( Haba Sultana😡😡)
     ★★★★
Isowar sa kenan cikin gidan a gajiye. Kai tsaye ɗakin sa. Jim ƙaɗan Ihsan ta shigo ɗakinsa Tana jin ƙaran ruwa a banɗaki lokacin da ta ajiye ma sa tea ɗin a ɗakin, kamar za ta fita sai kuma ta samu kujera ta zauna tana jiran sa. Kusan minti biyar sai ga shi ya fito ɗaure da towel. Ya na faman goge gashin sa da ɗan ƙaramin towel ya ganta ta ƙura ma sa ido.
"What the fuck! Mi ki ke yi a ɗaki na" Ya daka ma ta tsawa Daburcewa ta yi ta fara kame-kame.
"Get out" ya daka ma ta tsawa ba shiri ta fita da gudu dan ta san halin sa sarai.
Sai da ya shirya cikin farar riga da wando baƙi three quater sannan ya buɗe laptop ɗin sa ya na duba wani aiki da Dr Nasir ya turo ma sa. Yana dubawa yana kuɓartea ɗin sa a hankali. Ba laifi Nasir yai ƙoƙari, da alama ya san aikin sa dan tunda ya fara ma sa aiki bai samu kuskure ɗaya cikin ayyukan da ya ke sa shi ba, sai dai da saura tunda dududu sayi Ukku kenan da Nasir ɗin ya fara ma sa aiki kenan.
★★★★
A hankali soyayyar NAS da Sultana ta fara nisa, domin har Meena da Jidda sunsan komi...
Washe gari bayan ta dawo da wajen Aiki, tana ƙoƙarin shiga cikin gida mai gadi ya da katarda ita, "Madam gashi yamimama bag🛍 mai k'yau, ta amsa tana tafad'in namiye Baba?. "Wannan yaron ne ya sake da wowa, aiko da sauri Sultana ta nufi wajen tuni ya Ron ya ɓace, kai tsaye ta wuce ɗaki 🎁bud'ewa sukayi, flower🌹ce tanata k'amshi, sai zobe Azurfa mai masifar kyau da tsada
Sultana tasauke ajiyar zuciya tareda tunanin sak'o makamancin wannan da aka taɓa bata wata ukku dasuka wuce , da ƴar ƙaramar takarda,
*_kenafi ƙauna cikin matan duniya bani da buri sai muyo Auren dake!*
Wannan shine kawai arubuce, Sultana ta maimaita baitikan yafi sau goma, to wanenen wannan?,Kodai ya NAS ne? Kai anya kuwa?.
Saikuma turare mai masifar k'amshi, Sultana ta shinshina turaren talumshr idonta.
Jitake tabbas tataɓajin wannan k'amshin, amma a ina?.
Shine abin tambayar.
Da sauri tatashi zuwa gurin ajiye muhimman abubuwanta ta aje su anan..
Koda Meena ta shigo ta bata labarin sosai Meena tayi mamaki,"Anty Sultana nifa ina zargin NAS ne ke turo Miki saƙon nan gaskiya, "Nima Meena nafi zargin Shine!"
"Aiko Anty Sultana kiyi duk yadda Zakiyi ki gano ko waye. Suna cikin managar kiran Nas ya shigo," Yauwa Anty Sultana ki nuna mai sauƙonshi ya iso kin gode, Meena ta faɗa a hankali," mai Sultana ta gyaɗa mata, "Assalamu alaikum ta faɗa cikin sanyi Murya, " daga can ɓangaren Nas ya sauke sassanyan Nunfashi kana ya ce," Ina fatan saƙo Na ya samu ƙaɓuwa a wajenki?" da sauri Sultana ta waro manyan idanunta kaman tana a gabansa tace ," daman kaine?" Nas ya saki Murmushi mai sauti, Meena ga baki daya hankalin ta kan Sultana dake faman sakin Murmushi kaman gonar Auduga.
"Allah ka shammateni Nas!" Ta faɗa cike da shagoɓa, sun jima suna waya cike da zallar Soyayya....
Chapter 35 · 0% Book details