← Book details Dr Sultan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 54

Sashe 23

Dr Sultan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

irin wannan kyau ha ka Kodai A ɗaura Auren yanzu ka tafi da matarka, dai dai lokacin Mommy ta karaso da Ummul Kulsum da kanta ke sunkuye ga baki ɗaya a kunyace ta ke, Abdullahi ko ga baki ɗaya ya kasa ɗauke idanunsa kanta wani irin kallo yake binta dashi mai cike da ma'anoni "Sannu da zu wa Ango cewar Mommy bayan sun gama gai sa wa Mommy da Alhaji Nuraddeen su ka wuce, A hankali ya Abdullahi ya sauke sassanyan Nunfashi kana ,"Ya gida Kulsum!" A hankali ta Lumshe idanunta ta buɗe akan fusakarsa cikin sanyi Murya ta ce," Lafiya lau" "Ya su Mama!" "Alhamdulillahi" Bada ɓata lokaci ba ya sanar da ita abinda ke ta fe da shi, cikin Ikon Allah ko buƙatar shi ta karɓi hira suka sha sosai cike da so kaman waƴan da suka shekara a ta re. Wuraren karfe 10:30 ya yi mata sallama ta re da bata Number wayarshi, har bakin mota ta rakashi baiko bi ta kan Aminin nashi ba...🤣🤣 Bayan ta fiyar shi Ummu Kulsum ta sauke sassanyan Ajiyar zuciya tare da yi wa Allah godiya fuskarta ɗauke da murmushi ta wu ce ciki gida wuraren 11:10 ta kira shi tare da tambatayar ya iso lafiya nan fa suka barke da hira sun jima suna waya kana su ka yi sallama.. Ranar da haka su ka kwana cikin farin ciki.... Washe gari Abdullahi ya sha tsiya wajen Alhaji Nuraddeen 🤣 (Haba Abdullahi tun ba'a je ko'ina ba ina ga idon Anyi Aure zai manta da Nuraddeen 🤣🤣🤸) ★★★★★ A bunka da manya cikin ƙanƙanen lokaci suka fahimci juna duk wasu shirye shiryen Aure sun kammala Abinsu, lehe ma tuni ta haɗa abinda tare da Mommy gyara na Musamman Mommy ta yiwa ƙanwar ta ta A ɓangaren Alhaji Nuraddeen ba'a bashi a baya ba sosai ya gyara Aminin nasa... Ranar jumma'a kaka daura Aure gagarumin buki aka shirya na gani faɗa. Bayan Isha'i Amarya ta ta re ɗakinta... tarba ta Musamman Ummul Kulsum ta samu daga wajen Kaka... Washegari Abdullahi ya gabatar da ita a wajen ƴaƴansa, "wannan sun Nan Mama ga reta Maryam,zo nan mai sunan Mama!" Fuska a sake Maryam ta nufi wajenta,"Kina Lafiya?" Lafiya" "Abban Haydar yanzu kowa da Sunan Mama yake kiran ta ba sakayawa? Gaskiya Bazan yadda a riƙa kiran sunan Mama kai tsaye ba" ta yi maganar cikin gaskiya da gaskiya,"Kaka ko sai kallo su ta ke tana Murmushi har ga Allah Ummul Kulsum ta kwanta mata a rai, Abdullahi ya yi Murmushi kana ya ce "Mama ce ba ta son A kiranta da ko wanne suna!" Ummul Kulsum ta marairaice fuska kana ta ce,"Allah Ni kam ba zan "iya ba! Ni daga yau zan riƙa kiranta Sultana!!! Mama don Allah a yimin wannan Alfarma!" Fusakar Kaka ɗauke da murmushi ta ce," Ba komi Maman Haydar warin daɗi ta ji, Ranar dai ha ka suka kasance cikin tsantsan farin, Satin Ummul Kulsum biyu da tarewa Meenah da Arif suka dawo gidan da zama Haka sukaci ga ba da Rayuwa cikin kwanciyar hankali da so da kyaunar juna, ★★★★★★★.......... "Sultan Daddy ya ki ra sunansa cikin sanyi Murya, a hankali ya ɗago da kansa kana ,"Na'am Daddy!" Batun karatu tu ne? Mi ye burin ka? a hankali ya sauke sassanyan Nunfashi kana ya ce "Likita Daddy!" "Wow Ma sha Allah my Boy wacce ƙasa ka ke son ka yi karatu? " Daddy ko'ina ma zan iya ina takardun ka suke," Suna ɗaki Daddy je ka kawo min su, A hankali ya mike ya nufu ɗauki sa, jim kaɗan ya dawo riƙe da ta kardunsa cikin girmamawa ya miƙama Daddy takardun, ya na duba takardu ya na Murmushi, Ma sha Ɗan na wa ashe jarumi ne! Bayan ya maida ta kardun ya kalli Sultan kana ya ce," nan da sati biyu komi zai kammalu ka kasan ce cikin shiri... dai lokacin Mommy ta iso palon Fuskarta ɗauke da murmushi kaman ko yaushe, "Ni fa bana son ɗan uban cin nan da ake nunamin sai ku zauna kuna hira ba ni, ga ba ɗaya su su ka ya yi Murmushi, fuska a shogoɓe Sultan ya ce "Sorry Mommy!" "Na bi Sorry nan da gudu" "Batun karatun sa ne, "Mommy ta sauke Ajiyar zuciya kana ta ce ," Gaskiya ne Nima a bin na a raina" "In sha Allahu nan da sati biyu komi zai kammala yaron naki ya ce Likita ya ke son Zama! "Auww DR SULTAN!! Allah sunan ya yi daɗi!" "Allah ya tabbatar da Alheri" "Amin ya rabbi" ★★★★★★★.......... Bayan sati biyu kaman yadda Alhaji Nuraddeen ya faɗa tuni an Kammala duk wasu shirye shiryen ta fiyarsa washe gari wuraren 12 jirgin su ya ɗaga zuwa India ta re da Alhaji Nuraddeen.... Haka Mommy ta dawo gida cike da kewar Ɗanta da mijinta....satin Alhaji Nuraddeen ɗaya a India ya dawo gida... cike da kewar ɗan sa... Ranar da ya dawo tarba ta Musamman ya samu da ga wajen Habibity ɗin sa..... A hankali kwanaki suka ci gaba da shuɗewa tun bayan tafiyar Sultan kullum sai sunyi video call, A ɓangaren ka ratun sa kuma Alhamdulillah ko mi na tafiya yadda ya dace, duk wani Abin buƙata Alhaji Nuraddeen ya tanar da Mishi gida suku tun ya seya Mishi ɗaki biyu da palon kusa da Makarantar su ga maƙuddan kuɗi da ya zuba mishi a account. hakan ya sa ya maida hankalin sa sosai wajen karatu.... A ɓangaren Abdullahi komi Alhamdulillahi komi na tafiya yadda ya kamata Wata irin shaƙuwace mai ƙarfi ta shiga tsakanin Kaka da Ummul Kulsum Maryam wasa wasa ta saba da sabon sunanta gaba ki ɗaya kidan yanzu an Dena kiranta da Maryam harda Kaka.... Shaƙuwa mai ƙarfi ce ta shiga tsakanin Meenah da Sultana.... duk weekend su kan je gida Alhaji Nuraddeen wani lokacin hadda Sultana... Rayuwa taci gaba da tafiya, komai bisa tsari.., Lokaci na tafiya Rayuwa na ju yawa eh zuwa kwanaki - kwanaki na komawa makonni Makonni na juyuwa eh zuwa wattani Wattani na juyawa eh zuwa shekara Bayan tsowan shekara Takwas!!! "Mommy mun kammala shiri cewar wata kyakkyawar yarinya ƴar shekara bakwai, ta sake ce wa "Daddy mu yi sauri kar jirgin su Ya Sultan ya iso, Dai dai lokacin Alhaji Nuraddeen suka fito ta re da wani kyakkyawan Yaro dan shekara shidda kamanni su sak da yaron, "Ina Ihsan,"Daddy ta na waje" "Je daki ki kira Mommy da gudu yarin ƴar ta wu ce ɗaki ta na faman kiran "Mommy Daddy ya ce ki fito mu ta fi jirgin su Ya Sultan ya iso. "Mu tafi ta yi ta re suka fito daga ɗakin tuni Alhaji Nuraddeen sun fita waje Mommy na iso wa Security suka buɗe mata Mato a tsanake suka fice daga gidan kusan mota Ukku kai tsaye su ka wuce Airport, i sowar su ya yi dai da saukowar jirgin... Bayan mintu na Biyar mutane suka fara fitowa, mutum ukku ne suka sauko Sultan ya biyo bayan su, sanye da tailored suit sunyi matsifar yi masa kyau, tun bayan sakkowar sa ya hango iyayensu, don ha ka ya na saukowa ya nufo gurin su janye da trolly, da sauri Salma, Ihsan, Salim, suka isa gurinsa hannunsa ya buɗe su kowa suka shige ya rungumesu bayan ya janye su daga jikinsa ya isa gurin Daddy tamkar gaisuwar Indiawa su kayi Daddy ya buɗe Hannunsa shi kuma Sultan ya shige ya yi kwance a kirjinsa Kamar wani ƙaramin Yaro. Sun jima a haka sannan ya isa gurin Mommy ƙasa ya zuɓe a gabanta yana murmushi ita ko wa Hannuta ta ɗora a bisa kansa cike da farin ciki dai dai lokacin Abba Abdullahi ya iso fuskar ɗauke murmushi, Hannu ya miƙa Abba Abdullahi su gaisa kana ya ce ," An iso lafiya My Son? Cikin sanyi Muryar yace Lafiya kau Abba" kai tsaye suka nufi gun motocin su, a tsanake suka fice daga Airport ɗin," Wani farin ƙalle Salma ta saka ta rufewa Sultan Ido tana Murmushi haka suka ci gaba ta dafi ba tare da ya san ina suke nufa ba.... Har suka iso anan gama Parking Securitys su ka buɗe mu mota a hankali su ka fito daga motar Salma na riƙe da hannun sa, basu tsaya ko'ina ba a ƙofar gate, Ya Sultan Buɗe idonka " A hankali ya fara janye ƙallen daga saman fuskar sa har wani bishi bishi yake gani, cike da mamaki ya riƙa bin Gate ɗin da kallon ganin an kwawata shi da wani farin zare daga tsaki ana saka red ɗin zare anyi mishi Ado mai matsifar kyau a hankali Daddy ya fito da Almakashi mai matsifar kyau ɗan ma dai dai ci, "karɓi nan cewar Daddy jiki a mace ta ƙarba a hankali mommy ta ƙara so wajen ta ɗora Hannuta saman na Sultan kana Daddy ya ɗora nashi Abba ya ɗora nashi sai Salma Salim, Ihsan, a hankali Securitys suka fara ƙirga 1,2,3,!! Lokaci ɗaya suka yanka zaren cikin tsananin farin ciki, Mutane dake tsaye a wajen suka soma taɓi, A hankali Sultan ya sauke Nannauyan Ajiyar zuciyar, Mai ga ɗi ya buɗe gate ɗin gana ki ɗaya, Daddy ya Kalli Sultan cikin sanyi Murya ya ce ," mu shiga ko, cikin wani ɗin yanayi ya tattaro da duk ƙarfisa suka wuce ciki a hankali ya ɗago da kansa yana kallon wajen karab Idanunsa suka sauka kan Rubutun da Saman ginar SULTAN PRIVATE HOSPITAL.....ciki wani irin yanayi mai cike da tsantsan farin Sultan ya rungume Daddy ta re da faɗin Thank you so much Daddy Allah ya ƙarama lafiya da nisan kwana Daddy!" a hankali ya share kallor da ta zuɓo mishi... a hankali Daddy ya janye shi daga jikin sa, kana suka soma za gaye Asbitin, lungu da sako Saida suka za gaya komai an ta nada sun ɗau tsawon lokaci suna zaga ye Asbitin kana su ka wuce gida.....✍️✍️✍️ _More comments and share_ _domin neman ƙarin bayani 👉08149979652_ *Sadiya Ka'oje ce* *DR SULTAN* (A heart touching love story)
Chapter 23 · 0% Book details