← Book details Dr Sultan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 54

Sashe 38

Dr Sultan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

, harta samu kwarin guywar kallon cikin idonsa, amma kwarjinin dake taredashi yasakata saurin janye idon nata,
Kuttt! Yafad'a yana binta da kallo, yana rasa mizaice, saikawai yaja ajiyar zuciya, dolenema yayi bincike akan yarinyarnan, danyasan wacece ita?, shifa mamaki take basa, saikace aljana, tunda yake babu macen data taɓa kallon tsakkiyar idonsa sai yarinyarnan, duk girman mace kwarjini yake mata takasa masa kallon minti2 ma, bare cikin idonsa, duk jidakan yarinya da isarta, inhar zatazo wajensa tace tana sonsa, kotazo suyi wata magana, wlhy inhar yadasa mata idonsannan na yan sakannnu kawai saikaga jikinta narawa, tashiga hankalinta daganin bakin Rijiya bawajen wasan makaho baneba.
Amma yau ga yarinya k'arama, ta kalli tsakkiyar idonsa.
Ya furzar da huci daga bakinsa, Wanda yasaka su Daddy kallonsa.
"Sultana kuje sama kukai kayan a ɗakina.
"Mommy yau a ɗakinki zamu kwana wajen Anty Sultana, Salma da Salim suka faɗa, "Salma a zaku takure a ɗakin ku barsu Kinji, ,"nan ta ke ta marairaice fuska kakam Zatayi Kuku, Mommy ki barsu zamu kwana a tare, "A'a sai dai Salma ta kwana tare da kuku, Nana taje ɗakin Ihsan su kwana tare,
"Mommy Nifa".
"Kaje ɗakin Ya Sultan ka kwana, dai dai lokacin kuma su Haydar suka iso da Khalil da Arif, "Yauwa ga Ya Arif nan ma yazo zamu kwana a tare..
Nan take palon ya ƙara hargitse wa da hayaniyar su, kafinan suka ci Abinci na musamman da Mommy ta girka musu. Sai bayan Isha'i Ihsan ta fito daga ɗakin fuska a tsuke, sama sama suka gaisa dasu Sultana, Ƙarfe 8:50 su Haydar suka wuce gida haka a bar Arif.. bayan ta fiyarsu Sultana ta wuce ɗakin Mommy tare da Meena, "Anty Sultana karku rufe ɗaki ina nan tafe, ,"sai kinzo...
Suna shiga ɗakin Meena ta wuce toilet Wonka tayi ta fito ta saka kayan bacci ta kwanta nan take bacci ya Awon gaba da ita.
Bayan tafiyarsu, Salma bata jima ba ya yi Awon gaba da ita, koda Sultan ya shiga palon tana kwance, kashe Tv ya yi kana ya ɗauke a hankali, kansan cewar bacci nata baryi nisa Sosai ba, ta buɗe idanunta a hankali, cikin muryar Barci tace ,"Ya Sultan kaini wajen Anty Sultana...
Sultana Meena na fitowa daga toilet ɗin itama ta shiga Wonka tayi ta fito
bayan tafito tashirya cikin wando dogo da Riga Na cartoon kalar Pink sunmata kyau.sosai, tana gaban mudubi tana tufk'e gashinta Dan bataso tayi barci dashi ahaka, yaturo k'ofar yashigo, da sauri Sultana tajuya tana kallonsa.
'Dauke yake da Salma a kafad'a, saɓanin d'azun yanzu yasaka doguwar jallabiya, Salim nabiye dashi abaya, da'ala shi baiyi barcinba.
Ko kallonta baiyiba yad'orata a gadon Mommy, saida yagyara mata kwanciya sannan,
sannan yamata addu'ar barci ya shafa mata, Salim yace Ya Sultan ni awajenka Jan kana.
"Arif na can na jiran aka palon ɗakin ka Zaiyi barci.
Taɓe baki Sultana tayi,
Duk abinda takeyi ya Sultan Na kallonta ta k'asan idonsa, bakinsa yataɓe ya kauda kansa daga kallon nata. yafice abinsa, batareda ya nuna yamasan dawata hallita a d'akinba.
Da uwar harara Sultana taraka bayansa harya fita.
Yana fita ta kace wutan ɗakin ta kwana, nan take Barci ya ɗauke ta...
_Washe gari_
Har 8:30am Sultana bata tashiba, tuni su Salma da Meena sun tabar ɗakin ita kad'ai taketa juye-juyenta ƙaton gadon Mommy
Kowa ya hallara a dining har Daddy kasancewar weekend ne,
Mommy takalli dukkan yaran babu Sultana da Sultan ,
Meena tashi kakira Yayan ku, kekuma Salma kira Anty Sultana.
Da to suka amsa.
Babu dad'ewa saiga ya Sultan sunfito shida Meena rike da Hannun juna har k'asa ya durk'usa ya gaida iyayen nasa, k'annensa suka gaisheshi.
Yaja kujerar ya zauna, Sultana suka fito, da alama saida Salma tasha dagama wajen tashin Sultana, dan kayan barcinema ajikinta sai hijjab data d'ora iya ƙirji a saman kayan barcin, daka kalli idonta kasan yanzu tatashi a barci, saboda akwai ja acikinsu, gasukama sun k'ara zama manya, durk'usawa tayi tagaida Daddy, ya amsa cikin fara'a,
"Mommy Ina kwana"
"Lafiya lau Anty Yara"
Daddy yace tashi kizauna d'iyata yanuna mata kujera d'aya data rage wadda take kusada ya Sultan .
Jitayi tamkar tafasa ihu, amma babu damar hakan, dan Daddy kallon mahaifi take masa.
Mommy ta haɗawa Daddy Abincisa dasu Salma da Salim. "Sultana tatashi ha had'a masa shima, bak'aramar kid'ima zancen Mommy yasakataba,
Babu yanda zatayi tahad'a masa komai, yanata danna waya abinsa tamkar baisan mi'akeyi a dining d'inba,
Kowa yagama zuba abincin Daddy yayi bismillah, kowa yayi aka fara break, Sultana dukata takura, sai juya cokalin takeyi, shiko a kwalar rigarsa, abincinsa yakeci hankali kwance,
bayan sun kammala break fast Sultana tazare jikinta zuwa kicin taya masu aikin gidan Aiki Abinci....
Bayan La'asar, Sultana ta nufi gadin, tafiya take a hankali kai a sunkuye
batare data san mike a gabanta ba. Kaɗowar iska da sassanyan ƙamshin turare mai daɗin gaske ya sakata tsayawa cak ƙirjinta na harbawa da ƙarfi. Fararen idanunta ta janye daga kan wayar tare da ɗago kanta gaba ɗaya, a kan mutumin dake kishingiɗe bisa wata lallausan kujera, yana Danna lap-top ƙirar kamfanin apple dake akan wani ƙaramin table Gefensa kaɗan wani ƙyaƙyƙyawan bowl ne fari na tangaran cike da ƴaƴan itatuwa masu in ganci. Duk da tana a gab da shi aikinsa yake hankali kwance baiko nuna alamar yasan da zuwanta ba.
A hankali ta kawar da kanta gefe tana kallon gwaiba. Matsawa tayi a hankali, tsalle tayi da niyyar tsinkowa dan bishiyar na da tsayi sosai.
tsalle ta kuma yi amman ta kasa ga dai hannunta na taɓawa sede baza ta iya tsinka ba.
"Ki bar nan".
Sassaanyar muryarsa mai sanyi ta daki kunenta. Ƙirjinta ne ya sake harbawa har tanaji kamar jininta daya tsinke na neman biyo hudojin gashin fatarta ya fito. Bata da niyyar cewa komai, gata tsaye tamkar an dasata ta gagara ɗaga ko ƙafa ɗaya tabar wajen duk da haka zuciyarta tafi buƙatar da tayi. Jin shiru ba'a amsa masa ba, ga tsaiwar mutum yanaji har yanzu a gabansa ya sashi ɗago manyan idanunsa masu haske ya sauke a kanta. Fuskarsa dake a kame da kwarjini ya sake tsumewa yana sassauta girman idanunsa tamkar mai son lumshesu..
A fisge, tamkar an jawo furucin daga bakin Sultana ta yamutsa fuskarta da ƙanƙance manyan fararen idanunta , "Ansa dokar shika nan ne?"
Kamar yanda bai motsa daga yanda yake ba haka bai ce mata komai ba, bai kuma janye idanunsa a kanta ba har yanzu, tana matuƙar jin kaifi da tasirin idanunsa a dukkan ɓargon jikinta da jijiyoyi da gudanar jini.
Harara ta balla masa ta ƙyaɓe fuska da raɓashi ta wuce, danji take ƙafafunta tamkar ba'a kansu take ba.
Kai tsaye ta wuce cikin gida fuska a tsuke ta nufi ɗaki ta kwata cike da takaicin Sultan, da wannan takaici barci ya yi Awon gaba da ita, sai gab da maggariba ta farka, ruwa ta watsa tare da Alwalla kana ta fito, dai dai lokacin Meena na shigo ɗakin," Anty Sultana kinsha barci yau. Harara Sultana ta dalla mata, "yi haƙiri karki sauke barin nan a kaina, Saida suka Isha'i suka fito Palo.... Koda suka shigo palon Salim na kuka
Miya faru kake kuka Salim?.
Cikin kukan ya nuna Salma, ta Sultana ta maida kallonta kan Salma ita ma tana niyyar kukan.
" Meki kamasa?"
" Anty Sultana biscuit d'ina da yana Sultan ya bani shine ta kwace min." "Anty Sultana jiya tare mukaci nawa"
Bata k'arasaba taji Salim ya fusge hannunsa anata yakwasa aguje.
Juyowa tayi da sauri Dan ganin itama Salma tagudu.
Kasa ya duk'e suka shige jikinsa, bataga fuskarsaba saboda sun kare, amma jin yanda kirjinta keta harbawa taji ajikinta shine, dak'yar tacira k'afa danufin Darning..
Tare sukaci Abincin, bayan sun gama Daddy ya kalli Sultan, "idon sun gama ka maida su gida gobe Monday, wani irin farin cikin Sultana taji.... ai da sauri ta wuce ɗaki ta haɗa kayanta ta fito Palon Meena da Nana har ga Allah basa son barin gidan,
Lokaci da zasu tafi Daddy ya basu 200k su sa kati. da farko ƙin ƙarɓa Sukayi Saida Daddy ya yi musu jan ido kana suka ƙarɓa tare da yi masa Godiya. Har bakin mota suka raka su.
Meena ce a gaba Sultana na zaune gefen Meena, har suka iso gida Sultana Ƙala bata ce ba, suko sai hirar su, suke gwanin burgewa.suna isa ƙofar gida Sultana ce farko fita.
"Ya Sultana kazo muje cikin gida ka gaida Mami, Ya Sultan ni banma taɓa ganin kazo gidan nan ba,"Ameenatu! dare ya yi Zanyi na san duk sunyi Bacci next time zan shigo in sha Allahu. Ya Sultan.... Pls tayi maganar cike da Shogoɓa, kai ya gyaɗa mata alamar A'a, jiki a mace ta fife daga motar...
Saida yaga shigar su cikin gida kana ya wuce...
Waje gari, da safe Sultana ta wuce wajen Aiki...
A hankali Rayuwa taci gaba da tafiya cikin kwanciyar hankali. A ɓangaren Sultana da Nas Soyayyarsu suke Sha hankali kwance.
Yau ta kasance Weekend, tunda safe Sultana ta wuce gidan su jidda
Kaka ko yau tunda safe ta tashi da matsanancin ciwon kai. Bayan La'asar Mami ta bata maganin ciwon kai, tana sha bada jimawa barci ya yi a won gaba da ita...
Sai ƙarfe Shidda Sultana ta dawo.
Duk da takalman data gani na maza a ƙofar palon Daddy bata damu ba, sallama tayi kawai, kafimma su gama amsa mata ta shige dan duk zatonta Su Haydar a ciki, tunda tasan duk suna gidan. A shagwaɓe ta buɗe baki zatai magana. sai dai cin karo da fuskar da batai zato ko tsammanin gani ba ta sata waro manyan fararen idanunta waje cike da al'ajabi.....!"✍️ 
*Har yanzu dai muna cikin Book 1*
_More comments and share pls_
*Sadeeya Ka'oje ce* 💋✍️
*DR SULTAN*
(A heart touching love story)

_💖Story And Written💖_
⬇️
*Sadeeya Ka'oje*

💖الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر💖


Bismillah........ ✍

PAID BOOK
Littafin *DR SULTAN* na kudine akan 300 kacal , me bukatar ya karanta har karshe zai turo kudinsa ta wannan asusun 1490318334 Sadiya Attahiru kaoje Access bank ,sai a turo shaidar biya ta wannan number 08149979652. Nagode🤗
Chapter 38 · 0% Book details