← Book details Dr Sultan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 54

Sashe 39

Dr Sultan Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

*💋TITAN'S OF TALENT💋*
*Marubuta masu aiki da fasahar zamani , zalar ilimantarwa,fadakarwa dakuma nishadantarwa*
*(T .O.T)*
*Breathe in courage, breathe outfear, together we stand*
*Alkalaminmu abin alfaharn mu*
https://chat.whatsapp.com/CuNxneQ0ONc6x9yn9a16Jj
*The beginning*
*Page 29-30*
______Sultan dake zaune sanye da ƙanan kaya sun yi masa Kyau sosai, kallon nata yake cike da mamaki,, ya ɗauke kansa cike da shan ƙamshi kamarma irin bai ganta ba ɗin nan shi.......
        " Oyoyo Anty Sultana ”. Salma ta katse mata tunaninta. Juyawa tai inda Salam take, har yanzu mamakin ganin Sultan ɗin bai barta ba,
Sosai mamaki ya kume Sultana, kamar zatai magana sai kuma ta fasa ta sake maida dubanta ga Sultan daya maida dukan hankalinsa kan wayarsa..
"Shigo mana Sultana"
A hankali ta ƙara so cikin palon, "Daddy sannu da zuwa"
"Yauwa yar Albarka"
Kana ta zauna tare da su Salma.
"Toh shi Sultan bazaki gaida hiba?" cewar Abba.
Yanzun kam baki ta kumbura sosai, ta kalli Sultan ɗin da yayi tamkar baisan da zaman kowaba a palon ba tace, "ina wuni".
    Sarai yajita, amma sai ya share tamkar bejita ba,
"Ya Sultan Anty Sultana ya gaisheka" Salma ta faɗa a hankali.
Ya ɗago manyan idanunsa farare tas ya sauke a cikin nata. Karan farko da sukaima juna kallon ido cikin ido. Kusan lokaci guda kowanne gabansa ya faɗi. Sultana tai saurin fara janye nata da ƙoƙarin juyawa.
Shima ɗan lumshe nasa yayi ya buɗe cikin muryarsa mai amo ɗin nan yace, "Lafiya lau"
"Jeki kawo musu ruwa".
A hankali ta miƙe ta nufi cikin tare da Salma, kayan drinks ta haɗo musu masu sanyi,
wani irin Murmushi yayi , tare da miƙewa saboda wayarsa da aka kira,
harar ƙofar da Sultan yabi ya fice ta gefen ido.
Jim kaɗan mai gadi ya shigo, a bakin ƙofa ya tsaya, yana kiran ,"Sultana"
Miƙewa ta yi ta nufin wajensa, tsaye ta tarar dashi rike da 🎁, "gashi"
A hankali ta kai kallo da Sultan dake waya yana faɗin ,"Haba Aziz kasan irin da muwar da najiga reshin samunka a waya da nayi, taɓe baki Sultana tayi, tayi, yauma dai Flower ce mai masifar kyau da kamshi da yar takarda,
*Zan Kasance cikin Son ki har Abada*
 *kalaman bakina sun gaza furta adadin yadda Zuciyata* take* kyaunarki kin zamo tamkar Numfashin da nake shaƙa kece rayuwarta ina Son ki Sosai wallahi ban san na linda zan shiga ba In don na rasa ki ba kece Abar be gena safe da yamma daga Nas*
Wani irin sassanyan Nunfashi ta sauƙe lokacin da tagama karatun,
tafiya take kai a sunkuye
   Karo sukayi, goshin Sultana ya bugu goshin Sultan, Da sauri tai baya saboda azaba. Shima bayan yaja kaɗan yana wani yamutsa fuska idonsa a kanta. Kasancewar Sultana bata taka ɗan step ɗin ƙofar falon Abba dai-dai ba lokacin da tai baya sai ta sake yo gaba zata faɗi.
   Sultan ya tabbatar idan ya barta ta faɗi zataji mugun ciwo ne, dan haka da saurinsa kuwa ya tarota ta faɗo jikinsa. Sai kuma ta firgice saboda tsoratar da tai najinta kwance a ƙirjinsa, ta wage baki zata tsala ihu yayi sauri ɗora lallausan tafin hannunsa saman bakin nata ya rufe,
Cikin tashin hankali Sultana ta fara mutsu-mutsun kwatar kanta, jikinta sai rawa ya ke yi. Shikuma yaƙi sakinta dan ya tabbatar yana sakin nata faɗuwar daya gudar mata a farko sai tayi wadda ta fita a yanzu, cike dajin haushi ya daka mata tsawa, dan jiyayma kamar ya saketa ta faɗin ma yaga ƙarshen tsiwa.
cigaba dayin mutsu-mutsunta nason ƙwacewa takeyi, tuni hawaye kuwa sun fara bimata kumatu,
   baya baya Sultana ta riƙa yi shiko yana biye da ita, Jin ya manneta da bango sai tashin hankalinta ya ƙaru, dan ta zata wani abun kuma zai aikata mata, ta kasa nutsuwa ta fahimci taimakonta yayi. hannayenta duka biyu ta saka tare da dukan ƙarfinta tana ƙoƙarin ture masa hannunsa daya rufe mata baki da shi. Ko gezau baiyiba, saima wani shegen kallo da yake binta da shi tamkar ya manta a inda suke, ga fuskarsa a matuƙar ɗaur, sai dai shima zuciyarsa wani irin harbawa take da sauri-sauri.
Chapter 39 · 0% Book details