Sashe 2
Dr Sultan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*Page 1-2* *Book1* _____Hayani ya ce ke tashi ta ko'ina Mutane kowa na Harkan gaban shi, Wani kyakkyawan Saurayi ne tsaye a gaban wani ƙaton shago suna saukar da kaya a moto, Jikin shi duk a jiƙe da Zufa, " Sannu da Aiki, Ya yi Murmushi tare da Faɗin "Yauwa Oga, Haka suka riƙa sauƙe kaya a mota suna shigar da su cikin Shago, Gama warshi ya yi dai dai da Kiran Sallah Maggariba, Alwalla Ya yi suka wuce Masallaci, Saida Akayi Isha'i suka dawo Shago, "Oga zan wuce gida Ya yi Maganar kai a sunkuye, "Har zaka tafi Maleek"? "Eh Oga"Toh ga wannan ko sai Allah ya kaimu gobe, "Oga Nagode Sosai, "Miye Na godiya Maleek Hakƙen kane fa, Murmushi mai ƙawatarwa Ya yi, tare da barin shagon, Kai tsaye ya nufi cikin garin cikin ƙanƙanen lokaci ya iso Unguwar su , daga can Nesa ya han geta tsaye, Sai faman Kalle kalle take, ganin shi tafe yasa ta ruga da gudun Gaske ta nufi inda yake, durƙu sawa yayi ƙasa tare da buɗe mata Hannu ta faɗa a ƙirjinshi ya rungumeta, "Ya Maleek! Tun ɗazu nake neman ka Ya Maleek ina Ƙwai da kwai na? Ya Maleek Ina Arake na? Ya Maleek ina.... Yayi saurin da katar da ita a hankali ya janyeta daga jikinsa, ya tsura wa kyakkyawar fuskantar ido, "Irin wannan tabbaya Haka Maryama ta!"? "Ya Maleek kaifa kace zaka siyo min, tayi maganar tana Turo ɗan ƙaramin bakinta mai launin pink color, Numfashi ya fesar cike da gaji, a hankali ya Buɗe lumsheshin idanuwansa da suka ƙara sakayi jajir saboda gajiya, "Kinje Islamiya"? Kai ta ɗaga Mishi, "Bazaki bani Amsa ba? A karo na biyu na sake ɗaga Mishi kai, "Shike nan tunda Baza kiyi magana ba ruwa da ke kwai da kwai Ma Bazan baki ba daman Kaka kawai na saya....tayi sauri rufe Mishi Baki da iya ƙarfinta da laulausar fatarta kaman ta jariri sabon haihuwa, dariya ta bashi sosai ya yi saurin gimtse ta, ƙoƙarin janye hannunta yake sam taƙi bashi dama, ƴar ƙaramar ƴarinƴa da Ida sai shegen ƙarfi, "Uhmm Uhmm ya fara ya jujjuya kai ita ko sai kallonshi take, "Bazato ba Tsammani yaga hawaye na zubo mata a kan kyakkyawar furkarta, janye hannunta tayi daga bakinsa tana ƙoƙarin barin wajen, da sauri ya riƙo hannuta tare da juyo da ita suna fuskantar juna, a karon farko ya saki Murmushi, "cikin sanyi Muryar ya soma faɗin, "Meye a bin kuka a nan"? Kina son Nima nayi Kuka"? a hankali ta girkiza kai almar A'a, "Toh ki Dena kuka bana so Kinji,hannunsa yasa yana share mata Hawayen, " Ya Maleek da gaske Kaka kawai kasaya wa kwai da kwai"? "A'a wasa nake ga wannan ke kadai na sayawa, wani irin daɗi taji, "Ya Maleek komai da komai ka saya min,"Ehh" Ya Maleek Nagode," hannuta ya riƙe suka wuce gida, Koda suka shigo zaune take a tsakiyar gida saman tabarma, da sauri ta saki hannun sa, ta zauna saman tabarma, "Kaka Kinga Abinda Ya Maleek ya kawo min Ni kadai bada keba,"Kaka Barka da dare, "Abdul Maleek Barka kadai an dawo lafiya,"Lafiya kau Kaka, "Madalla ya Kasuwa," Alhamdulillahi Kaka, "Allah ya taimaka, "Amin ya faɗa cike da gajiya, "Maryam tashi ki ɗauko masa Abinci sa, "Kaka bari na gama cikin kwai da kwai na, "Bana son shashanci maza tashi, "A'a Yayi saurin ka tsayeta Kaka ki barta kwai zan ɗauko da kaina, bai jira mi zata ce ba ya wuce cikin ɗin, "wai yaushe zaki girma Maryam, shekara Goma sha biyu har yanzu ba ki sa ciwon kan kiba"? dai dai lokacin ya dawo a hankali ya zauna gefen tabarmar ya fara cikin Abinci cikin natsuwa, lokaci lokaci yakan ɗago ya kalle ta har ya kammala cikin Abincin ya maida kwananan cikin, " Kaka Kinga sallamar da Oga ya bani yau dubu Biyar ne, "Kai Masha Allah, Allah ya ƙara buɗi Mai Albarka Abdul Maleek, "Amin Kaka A kwai Abinda kike Buƙata, "A'a Abdul Maleek Allah dai yayima Albarka, furkarshi dauƙe da Murmushi ya ce "Godiya nake Kaka" Idon Kin gama cikin kayan kwadayin ki ɗauƙo littafin ki muyi karatu kafin na wuce, "Abdul Maleek idon ka biye mata sai ka kwana a gidan nan bata kammala ba, " Ni Wallahi kin saka min Ido da yawa Kaka, tayi maganar cike da Shogoɓa, Aure ma zanyi na huta da wannan ɗumin Naki, lokacin ɗaya suka kwashe da dariya, "Ya Maleek ba kai kace zaka min Au.... "Kinga kina ɓata min lokacin, zumbur ta miƙe tare da barin wajen, " Allah ka shirya min ƴarin ƴar nan cewar Kaka, "Amin ya faɗa a hankali, "Yau Ni zan fara yin karatun idon magana sai ka ƙaramin, " wannan saurin Allah yasa kin iya a bin kwarai Kaka ta faɗa cike da zolaya, "Babu Ru wanki da Ni, tayi maganar tana ƙoƙarin zama, " Abdul Maleek ga wannan idon tayi kuskure ka zane ta, ƙarɓan balar ya yi ya na Murmushi, "Ni na san Ya Maleek bazai da ke ni ba, littafan boko ta fito dasu Nan tashiga yimai bayanin Abinda aka koya musu sosai yaji daɗin yadda take mai bayani komi dalla dalla ko wanne subject, harda Assignment ya nuna mata yadda Zatayi, tana gamawa ta fara karatun Alkur'ani cikin zazzaƙar Muryar ta mai sanyi, tunda ta fara karatun ya lumshe ido yana saurarenta harta kammala, ya ƙara magata, tunda suka fara karatun Kaka ta tsura musu ido tana kallon su, cike da Sona da kyauna, bayan sun kammala hira sukayi ƙaɗan, Maryam sai hamma take, "Kaka ni zan tafi Saida safe, "Toh Abdul Maleek Allah ya tashe mu lafiya, "Amin Kaka, cikin murya Bacci Maryam tace, "Ya Maleek Saida safe, Murmushi kawai ya sakan mata, sannan ya fice daga gidan, Kaka ta rufe gida, tadan yin kakkace kakkacen sanan suka wuce ɗakin, Suka kwanta, Nan take Bacci mai daɗi ya dauƙe su, ★★★ Yana barin gidan kai tsaye ya nufi ɗan ƙaramin ɗakinsa irin na samari, ya watsa ruwa yaji wani irin iska mai daɗi na shiga jikinsa, a hankali ya zauna saman katifarshi, karatu ya soma yi da ɗan rubuce rubuce bayan, yana gamawa ya fara karatun Alkur'ani na ɗan wani lokaci, Addu'a yayi sannan ya kwanta nan take bacci mai ɗaɗin gaske ya yi a won gaba shi cike da mafarkai masu ɗumbi da ɗi da rudarwa, ★★★ Washe gari Tunda Assuba ya farka Alwalla ya yi ya wuce Masallaci, bayan ya dawo ya yi karatun Alkur'ani sannan ya yi Wonka ya shirya, ya gyara ɗakinsa tsab kana fice daga gidan kai tsaye ya nufi gidan kaka.... "Maryam tashi kiyi Sallah karki bani na same a wajen, ko motsi batayi ba, "Wai ba magana nake ba, a hankali ta Buɗe Idanuwanta ta sauke su kan Kaka dake zaune a tsakiyar ɗakin, "Ga ruwan Zafi can cikin bokiti saura kuka ki tsaya shirita ta, A hankali ta fice daga ɗakin, tana gama Wonka ta fito a tsiyar gida ta duƙa tana Alwalla a hankali ta janye hular kanta nan take gashin ta dake kwance har gadon baya ya bayyana baƙi wul da shi sai sheƙi yake, tana kammala Alwalla ta wuce cikin ɗaki Kaka na Zaune tana juya mata Shayi ɗon yayi sanyi, bayan ta shirya ta saka Unifrom farar riga da Blue wondo sai hijabi fari ɗan ma dai daici sosai Unifrom ɗin sukayi mata kyau sun zauna Das a jikinta," Ta yi Sallah, a tsanake ta soma shan shayin , dai dai lokacin ya shigo gidan," Kaka Ina kwana"? "Abdul Maleek lafiya lau shigo Mana,a hankali ya shigo ɗakin ya zauna, "Ya Maleek ina kwana"? "Lafiya lau" "Ga Naka Abdul Maleek, "Nagode Kaka a tsanake ya soma cin abinci, lokaci ɗaya suka Kammala," Tashi mu tafi karmu makara, a hankali ta miƙe tare da ɗaukar jakar Makarantar ta, "Kaka zamu tafi, "Allah ya kiyaye Abdul Maleek Allah ya bada Sa'a, "Amin Sannan suka fice daga gidan, Tafiya suke a natse yana riƙe da hannunta Suna hira gwanin burgewa har suka iso makaranta," Toh ni zan tafiya kiyi karatu Kinji, "Toh Yaya me zaka seya min? ta ƙarasa maganar tana Murmushi, "duk abinda kike so, "Kasiyi irin na jiya, "Shikenan kiyi sauri karki makara, yana tsaye a wajen yana kallon harta shige Ajinsu, A hankali ya sauƙe Ajiyar zuciya, dai dai lokacin mai mashi ya aje wani Malami, "Malam tafiya ne "? Wacer ɗan Ajaɓa, "Ehh kasuwa zaka Kaini, "muje" yana hawa suka wuce, Suna isowa ya sallami mai mai Mashin ya wuce shago, "Oga ina kwana, "Lafiya lau Maleek" Nan ya shiga gaida mutan dake kewaye da shagon Abokan Ogan shi, yana shiga shagon ya fara kakkance Kakkance tare da fitar da Abu marar Amfani bayan ya gama ya share Shagon har zuwa gaban shago ko'ina tsab, Haka ya suka yini a kasuwa suna hadada da Mutane har zuwa Bayan Isha'i, sannan ya wuce gidan yauma kamar jiya da gudun Gaske ta iso wajen sa, ya rugumota, "Ya Maleek sannu da zuwa, "Yauwa kina Lafiya"? "Ya tsaraba na"? "Gashi nan" ya faɗa a ɗan fusace, "Rau rau da ido ganin ya ɓata rai, "Ya Maleek kayi haƙuri, "ALLAH Idon na sake kiyi Miki magana kika share Ni Bazan ƙara saya Miki wani Abuba, "Kayi Haƙuri Ya Maleek!!" Kama Hannuta yayi suka wuce cikin gida, Yauma kamar kullum zaune take a tsakiyar gida suka shiga Yayi Sallama ta Amsa Mishi, "Abdul Maleek Sannu da zuwa, "Yauwa Kaka ya gida, "Lafiya lau' " Tashi ki ɗauko Mishi Abinci, bayan ya kammala cikin Abinci sukayi karatu Sannan ya wuce gida, "Kaka kaman Wayar ki Na Ringing, tashi ki ɗauko tun bata tsinke ba, da sauri ta nufi ɗaƙi lokacin har kiran ya yenke tana dauƙar wayar wani kira ya sake shigowa, "Abba Abdullahi ne ɗaga wayar tayi, "Abba Barka da Dare, daga can ɓangaren aka Amsa da "Mamana Kina lafiya? Ina Mama? "Lafiya lau muke Abba, Abba yaushe zaka kaimu birni nida Kaka, "Abba ka maida mu Birnin tare da Ya Maleek Abba K..... "Ya isa haka Mamana Ina Mama"? "gata Abba, cikin Sanyi Murya Kaka ta kira sunansa,"Abdullahi Ya gida"? Ya Iya linka"? "Lafiya lau suke Mama ɗazu da Safe na kira baya zuwa, " Ehh ɗazu sabin din ya ɗauƙe, Dariya Maryam