← Book details Dr Sultan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 54

Sashe 44

Dr Sultan Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

sallar magriba ne ya saka Mami shigone ɗakin Sultana ta tadata. Da ƙyar ta samu ta tashi dan barcin nata yayi nisa sosai. Taimaka mata tayi tai alwala, Koda ta idar bata fitaba tai zamanta a ɗaki, sai da tai sallar isha'i da shafa'i da wutiri sannan ta ɗauƙi wayarta, miss call ɗin Nas ne da massages ɗin sa ba adadi, Sultana ta sauƙe Sassanyan Nunfashi, a hankali ta riƙa bin massages ɗin tana karantawa. "Anty Sultana ya ƙarfin jiki?" "Alhamdulillahi Meena" "Nas ya yi takira lokacin da kike Asbiti, Anty jidda ma ta kira ba adadi. "Allah sarki My Mommy nayi kewarta Sosai, bayan sun gama waya da Nas ta kira Jidda sun jima suna waya.. ____________★★★★ A ɓangaren Sultana kuwa tunda daga ranan da Abba yayi mata maganar aure ta watsar da maganar kasancewar Kaka da Mami ma basu sake yi mata maganar ba ita ma bata sake tada maganar ba hakan yasa bata ɗauki maganar da muhimmanci ba ita kuwa Kaka ko kullum cikin ya mata Addu'a take Sultan al'khairi ne agareta Allah ya tabbatar mata da al'khairi idan kuma ba al'khairi bane Allah ya zaɓa mata mafi al'khairi shima kuma Allah ya musanya masa da mafi al'khairi.... A ɓangaren Sultana kam Soyayyarsu suke Sha hankali kwance ita da Nas... Tsawon sati biyu kenan da zuwan Sultan wajen Sultana, tun lokacin ko bai sake sakata a ido ba, ka a Asbitin ba sake haɗuwa ba.. Sultana duk wata hanya da zata haɗa ta Sultan ta daƙileta... A hankali kwanaki suka ci gaba da shuɗewa, yau sati ɗaya kenan da akayi sallah layya, haka suka gudanar da bukin sallar su cikin kwanciyar hankali. Ƙarfe Shidda suka tashi daga aiki, lokacin da suka fito jidda ta nufi Motarta ta wuce gida, Sultana ta nufi motar,ta tada motar taƙi tashi kusan minti 20 tana abu guda gabaki ɗaya a gajiye ta, wayar Abba ta kira ta sanar dashi, daga can ɓangaren Abba yace mata baya gida, Su Haydar ma basu dawo ba ga hadari kuma gari har yasoma duhu mamana nasan Abin hawa zai Miki wahala, bari naki Sultan idon bai wuce ba ya dawo dake gida, gaban Sultana ne yayi Masifar tsinkewa tana ƙoƙarin magana Abba ya kashe wayar, a hankali ta ɗaga kanta ta kalli sama hadari ta ko'ina yana batun haɗewa, A ɓangaren Sultan ko yana ƙoƙarin barin Office kiran Abba ya shigo, Cikin girmamawa ya gaida Abba," Yauwa Sultan ƙanwarkace motar ta taƙi tashi shine nake son ka maida da gida...Shiru Sultan yayi tun lokacin da Abba ta ambaci sunan Sultana ya nemi nutsuwarsa ya rasa sam baya. Son wata alaƙar da zai haɗa sa da ita..Jin yayi shiru Abba yace ,"Kana jina Sultan?" da sauri ya ce ,"Ehh Abba" "Yauwa na gode". "Ba komi Abba" A hankali ya sauke Nannauyan Numfashi kana ya nufi farfajiyar Asibiti, A natse ya nufi matarsa ya shiga Cak Sultana ta tsaya ganin motar Sultana tafe nanda nan ta nemi natsuwar ta ta rasa A hankali ya yi parking kusa da ita, buɗe bayan mota tayi ta shiga. lumshe idanu Sultan yayi ba tare da yaja motar ba. Sun kai kusan minti huɗuahaka ita batace komai ba, haka zalika shima baice komai, har a fara iska da ƙarfi, ɗago Idanunsa yayi dai-dai lokacin da itama Sultana ta ɗago Idanunta ta kalli madubin cikin motar, idanunsu ne suka sarƙafe cikin na juna. Cikin sanyi Muryar da bai san yana da ita ba,"Halam Ni direban ki ne ?" Jikinta har yarawa yake ta fito , gaban motar ta buɗe ta shiga dai-dai lokaci Ka ɓarke da ruwa kamar da bakin ƙorya, Suka.fice a guje .Tunda suka shiga motar babu wanda yace da ɗan Uwansa komai kowa da irin tunanin da yake Aransa kana ga abin hawa da suke giftawa da ɗan gudu kasancewar maghariba ta gabato gashi har yanzu ana tsula ruwa... jinginar da bayanta da jikin kujeran zuciyarta na bugawa. Suna cikin tafiyar aka wani walƙiya mai masifar haske , Atsorace tace.“Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n”.Ta gefen ido ya kalleta Sultan ya Kalleta. Gudu Sultan yake sosai, Sultana ko duk ta tsorace,cikin Suɓutar halshe tace "Don ka rage gudu bana so!!" Ƙala Sultan baice mata ba. Ƙawar da kai gefe Sultana tayi tare da watsa masa Harara kana ta murguɗa baki, A hankali tace ,"Mugu kawai" Cikin Wata irin murya yace. "Idan kika sake tura min bakin nan, zan tsikeshi🤣" haka dai sukaci gaba da tafiya Suka cikin tafiya aka saki wata irin tsawa mai firgitarwa Cikin wani irin tsananin tsoro Sultana ta saki ƙara mai razanarwa tare da faɗawa jikin Sultan ta mishi wata irin Runguma Wani irin bugawa zuciyarsa keyi da masifar ƙarfe yayin da gaba ɗaya ilahirin jikinsa ya ɗauki rawa ƙoƙarin taka burki yake amma ya gagara saboda yanda ta takure jikinta ajikinsa ta ƙamƙamesa, ta kife kanta afaffaɗan ƙirjinsa, . Wani irin masifaffen tsuma jikin Sultana keyi yayin da numfashinta ke fusga saboda tsananin tsoro Allah ya sani tana masifar tsoton tsawa hakan yasa ta sake ƙanƙamesa tamkar zata tsaga jikinsa ta shige ciki.cikin wani irin yanayi ya ya buɗe hannayensa ya rungumeta da azaban karfi tare da taka burkin motar da ƙarfi, Rungumeta yayi da masifar ƙarfe kana ya cusa kansa atsakanin kafaɗarta da wuyanta. Lokacin da aka kuma sakin wani irin tsawa, Atake zuciyarsu ya buga da mugun ƙarfi , Sultan wani irin rungumeta yayi da masifar ƙarfi yana mai sakin Nannauyan Numfashi. Sultana numfashi ta shiga saukewa akai-akai tare da sake manna kanta ajikin damtsen hannunsa. Ahankali ya juya ya kalli yanda rabin jikinta ke kansa cikin wata Sanyayyar murya, "Sultana!! Wannan shine karo na biyu arayuwarsa da ya taɓa kiran sunanta,"Sultana!! ƙara lafewa tayi a jikinsa, tana shaƙar dadɗan ƙamshinsa turarensa mai sanyi, Buɗe idanunsa yayi da kyar murya a sanyaye ya ce, "sauka a jikina!". Cike da tsoro da kuma sanyin jiki ta janye jikinta daga garesa kana ta sauƙe ajiyar zuciya... "Nidai tsoro nake ji, kayi sauri ka maidani gidan mu" Harara ya watsa mata kana ya cigaba da Driving ɗin sa batare daya tanka taba yana isa ƙofar gidansu yayi Parking cikin sauri ta buɗe motar ta fita da gudun Gaske, kai tsaye ya wuce gida saboda har yanzu ruwan basu ɗauke ba ....jiki a mace.. Sultan ya wuce gida.... ________★★★★ Bayan sati ɗaya, suna zaune a palon Abba ya killi Kaka cikin sanyin Murya yace ," Mama ya batun maganar Auren Sultana naji shuru, gashi Nuraddeen kullum sai ya yi min maganar, Kaka ta sauke Ajiyar zuciya kana tace ,"Nima maganar ta tsaya min rai, Saida kuma matsalar da Sultana ɗin ke mafa dashi, ya kama abita cikin lalama," Haka ne Mama!" Saboda matsalar yasa nake goyen baya ta Aure Sultan shine zai zame mata jigo a rayuwarta kasan cewar Likita! "Wannan gaskiya ne. Suna tsaka da Magana Sultana ya shigo Palon, "Mamana zonan" a hankali Sultana ta nufi wajen su ta zauna, Abba ya fesar da Numfashi mai ɗumi . Palon yayi shiru, kowa ya maida hankalinsa ga Abba yafara nasiha, sannan yaɗora da faɗ'in wannan zama yashafi ki Sultana, Batun Auren kine da Sultan ina maganar ta kwana ?" Cikin raunan'nanyar murya tace ,"Abba wlh banza Aurenshi ba! Abba wlh ɗan isk.....Abba ya yi sauri ɗakarta da ita ta, fashewa da kuka mai tsuma zuciya Sultana ta yi. "Abba wlh bana sonsa Abba ina da wanda nake so!!! ABBA ya dubeta rai Ɓace, waye ne zaɓin baki? Kuma yasa baki taɓa gabatar da shi ba ?"Kintaɓa yi masa magana? Wanene zaɓin naki? Kin taɓa sanar dani kinada wadda ki keso ne? Kai ya Sultana a ƙ'asa tana sauke numfashi da k'yar, saboda damuwar datake ciki, gawani Abu dayazo ya tokare mata mak'oshi saboda tashin hankalin, ta girkiza kai Shiru yayi bata komaiba.cewa ƙanana. Wannan ya k'ara hasala Abba, ya ce Sultana kabud'e baki kayi magana ta ɗ'ago idanunta jajur tazubasu kan Abba, Babu wanda ya lura da halinda yake ciki . Sai ganinta kawai sukai kwance ƙasa wanwar. A take falon ya sake rikicewa gaba ɗaya. Duk suka rufu a kanta ana zubama ta ruwa dan son aga ta farfaɗo. Sai dai kuma ko motsi batai ba balle suyi tunanin dacewa. Kaka ta aza Hannu saman kai tana faɗin ,"Shike nan ta mutu!!!"✍️ (Nima na aje biyo ina hawaye 💔😥) Yanzu Aka soma wasan kudai ku zance da Sadeeya Ka'oje don jin ya zata kaya!!!. _More comments and share pls_ *Sadeeya Ka'oje ce 💋✍️* *DR SULTAN* (A heart touching love story)
Chapter 44 · 0% Book details