Sashe 8
Dr Sultan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
﷽ Bismillah........ ✍ Tallah ! Tallah !! Tallah!!! Shahararriyar Marubuciyar nan Hafsat Muhammad Bature (Boss Bature) wacce ta nishadantar daku a littafin ta mai suna *ABBAN SOJOJI* yau ta sake dawowa muku da sabon labari mai ɗauke da sabon salo na musamman *KURKUKUN ƘADDARA* labari ne mai kunshe da Butulci , tausayi , ban dariya , cin amana , soyayya mai shiga rai karna cika Ku da surutu, *KURKUKUN ƘADDARA* littafine mai ɗauke da Rudani da ban Al'ajabi kudai ku kasance da Alƙalamin *Boss Bature*💋💖 domin ƙarin bayani ku tuntuɓi wannan Number 08103884440 *💋TITAN'S OF TALENT💋* *Marubuta masu aiki da fasahar zamani , zalar ilimantarwa,fadakarwa dakuma nishadantarwa* *(T .O.T)* *Breathe in courage, breathe outfear, together we stand* *Alkalaminmu abin alfaharn mu* https://chat.whatsapp.com/CuNxneQ0ONc6x9yn9a16Jj *Page 7-8* _______Yana barin gidan ta fashe da kuka tana kiran," Ya Maleek!" da kyar Kaka ta lallashe tayi shiru, Abdulmalik bayan fitar dashi daga gidan Kai tsaye ya nufi Kasuwa ba wani jimawa motarsu ta ɗaga cike da kewar Maryam.... Yinin Ranar gabaki ɗaya Haka maryam cikin fushi, da Daddare haka taƙi cin Abinci, Saida kaka tayi mata zan ido kana ta ɗan ciki ƙaɗan, kwanan su Abdulmalik Ukku a birni suka dawo, Wuraren ƙarfe Shidda ya shigo gida, " Maraba da mutanen Kano, Kaka ta faɗa cikin tsananin farin ciki, dai dai lokacin Maryam ta shigo gida dawowar kenan daga Islamiya a guje ta nufi inda yake ta rungumeshi, "Ya Maleek sannu da zuwa!!" A hankali ya juyo da ita suna fuskantar juna, "Kina Lafiya?" da sauri ta ɗago ta kalleshi tare da sakin Murmushi Nan take ɗin dinta suka bayyana, A hankali ya motsa Lips ɗinsa hakan ya sa ko Kaka dake kusa dasu bati me ya faɗaba, " Maryama ta!" ta kira sunanta cikin kasalelliyar murya da ta sa Maryam sauri ɗagowa ta zuba mishi ido domin bata taɓa saninsa da irin wannan Muryaba, a hankali ta sake yin ƙasa ta kanta cikin tsananin kunya, yatsun hannunta ya sha jan lalle ya zubawa ido, ƙasa tayi da kanta tana ci gaba da wasa da yatsunta, a hankali Maryam ta Manyan idadunta ta kallesa, ya ɗaga mata gira tare da jan Numfashi ya fesar, Kaka dake gefe ta saki baki cike da Mamakin irin Kallon da suke wa juna, Abdulmalik har ga Allah ya manta da Kaka na Wajen, Ido a lumshe yaci gaba da kalli yatsun hannunta, Maryam tuni jikinta Yayi sanyi, Kaka sam ta gaza ɗauke ido a kansu, Murya can ƙasa ƙasa kaman mai raɗa yace "waya Miki lalle nan mai kyau!" Sassanyan Nunfashi ta fesar cikin sanyi Murya tace "Kaka!" kaka kam sai Raba ido take ta kalli Abdulmalik ta kalli Maryam, a hankali Maryam ta fara janye hannunta daga nashi, ciki wani irin yanayi da Baitaɓa rikar kanshi ya yi saurin janyo Hannuta yana ci gaba da kallon su, a hankali ya lumshe idanunsa nan take hawaye Masu matsifar sanyi suka zubo kan kyakkyawar fuskarsa, Maryam da Kaka cike da Mamaki suka zubawa fusakar ido ganin Hawaye kwance a saman fusakar shi, haka Maryam ta tsinci kanta da share mishi Hawayen, a hankali ya sauke sassanyan Ajiyar zuciya, " Ya Allah ka jiƙan Ummina!" Ya faɗa can ƙasan maƙoshi, Murya a dishace Maryam tace ," Ya Maleek Kukan me Kake?" A karon farko ya saki Murmushi ƙarfin hali, cikin wani irin yanayi da bai iya jurewa, sun ɗau tsawon lokaci a haka ba tare da sun sake Magana ba. Mutsu mutsu ta fara tare da ƙoƙarin janye hannunta dake sarƙe da nashi, kansa ya ɗago ya kalleta da rikitattun idanunsa, Nan taga yadda idanunsa suka kaɗa sukayi jazir sun sake cika da tace da hawaye, Ƙoƙarin janye hannunta taci gaba da yi jiki a ya ɗago da kansa ya kalleta sai kuma ya Lumshe idon Hawayen da suka cika a idonsa suka zubo, a hankali yaja dogon Numfashi mai bala'in ɗumi da kyar ya tattaro da ƙarfisa, murya a dishace yace," ga wannan, ba tare da yadda sun haɗa ido ba, murya a dishace Maryam tace ," Ya Maleek baka son lalle na Dena!" ba tare da ya kalleta cikin sanyi Murya yace Ina s.... Karab Idanunsa suka sauka kan Kaka dake tsaye ta zuba musu ido, da sauri ya janye Idanunsa daga kallon Kaka, a hankali ya sunkuyar kai tare da shafa kanshi cikin sanɗa sanɗa ya yi ƙoƙarin ficewa daga gidan," Abdulmalik cak ya tsaya jin Muryar Kaka ," Ina zaka je? Cikin sanyi Muryar ya soma Magana," Gida zanje Kaka!" "Dawo Kaci abinci" a hankali ya sauke Ajiyar zuciya, kai a sunkuye ya dawo ya zauna a tsakiyar gida Kana kaka ta aje mishi abincin sa yaci, Kaka na janshi hira har ya kammala, dai dai lokacin Maryam ta iso riƙe da perpar," Ya Maleek duba ga ki waye wannan?" A hankali ya Lumshe idanunsa kana ya buɗe akan takardar, da sauri ya runtse idanunsa, wani irin Amitattacen Nunfashi mai cike da yanayi na Musamman ya fesar da idanunsa suka kan Hoton da jikin takardar, "Ya Rabbi!!" Shine a binda ya iya furta, a hankali yaci gaba da kallon kyakkyawan Saurayin da ke cikin takardar, Kaka ma zajen take kallo, "Maryam waye kuma kika zana?" Wani irin sassanyan Nunfashi ta fesar," cikin sanyi Muryar tace,"Kaka Ya Maleek!! Ne" Wani irin lumshe idanunsa ya yi, wani irin kallo mai tafiya da dukan natsuwa yake binta dashi tun daga farko hoton har zuwa sama ina Aka rubuta YAYA ABDULMALIK da manƴan haruffa, hoton shine sak Maryam ta zana, zane na ɗaya daga cikin bawarda Allah ya yi Maryam, "Maryama ta!" Nina kika zata haka, ai zanen ya fini kyau, Harara ta zabga mishi, murmushi yayi tare da ƙarɓan zane yana Kallo, "Maryam ta! Allah zanen nan ya fini kyau!" da sauri Abdulmalik ya juya yana kallon Kaka," Kaka da zanen nan dani wa yafi kyau!"?yadda yayi maganar da kuma yadda ya marairaice abin yaba Kaka Dariya," fusakar Kaka ɗauke da murmushi tace ," Abdulmalik ai kafi zanen nan kyau kaifa kyakkyawa ne! Ma sha Allah!" Rau rau Maryam tayi da ido sai kun ta ta tsuke fuska kana tace ,"Ya Maleek kaifa kyakkyawa ne!" Abdulmalik a hankali ya tauna lips kana yace," Ki bani hoton nan na tafi dashi ɗakina" Harara ta dalla mishi ,"Allah Bazan Bazan ba daba, Saida na zana ma wani ta karasa maganar cike da tsiwa da murguɗa baki, Abdulmalik ya yi Murmushi, haka suka kasance cikin farin ciki zuwa bayan Isha'i bayan sunyi gama karatu suka ɗanyi hira kana ya wuce gida cike da gajiya... Yana isowa ya ɗan yi yi gyare-gyare a ɗakin.Abdulmalik Gwani ne a fanni tsabta kana ya yi Wonka ya kwanta nan take bacci gajiya ya yi awon gaba shi.... Washe gari ranar baije kasuwa ba wonki yayi musu kayanshi dana Kaka da Maryam, Maryam na tayashi gwanin burgewa, "Kinga ki Dena wankin Nan kar lallenki ya goge, "Ya Maleek idon ya goge Kaka zata min wani, haka suka ci gaba da wonki har suka kammala, ranar gabaki ɗaya a gidan kaka ya yini sai dare ya wuce gida tare da kayan shi da wonke Kaka sai saka mishi Albarka take..... A hankali Rayuwa taci gaba da tafi cikin kwanciyar hankali tuni su Maryam sun koma Makaranta, sosai ta maida hankali wajen karatun, duk abin ya shige mata duhu takan tuntuɓi Abdulmalik, hakan yasa komi ke zuwa mata da sauƙi, a ɓangaren islamiya ma ba'a barta a baya ba, Rayuwar suke cikin kwanciyar hankali da ƙaunar juna, zuwa yanzu Maryam Na gaba da cika shekara goma sha ukku a duniya, A Ɓangaren Abdullahi ma duk bayan wata ɗaya yakan aiko musu da kayan Abinci kaman yadda ya saba da duk wani abun buƙata, kusan kullum sai ya kira su, Abdulmalik da Abdullahi basu taɓa haduwa kasan cewar yana jimawa bai zo ƙauye ba saboda yanayin aikin sa, duk lokaci zaizo ko tunda safe yake zuwa haka zai zauna suyi hira da Kaka harzu zuwa lakacin da Maryam zata dawo daga Kamaranta, kana ya wuce Kano... “Kaka Abba ya Kira, kiran na gab da tsinkewa ta ɗaga, cikin sanyi Murya ta soma magana "Abba ina wuni ya gida Abba ina su Haydar"? daga can ɓangaren Abba ya sauke Ajiyar zuciya Kana," Mamana Lafiya lau suke, Ina Mama"? "Gata Abba" tayi Maganar ta re ɗorawa Kaka wayar a kunnen, "Abdullahi Ya gida"? ta faɗa cike da kewar ɗanta, " Lafiya lau Mama" cikin raɗa Maryam tace "Kaka ga ki gaya mishi na kusan sauka, ranar walima yazo dasu Haydar" Kaka ta talla mata Harara,nan take Maryam ta tsuke fuska tana turo baki, haka suka ci gaba da hira gwanin burgewa, Kana kaka ta mikawa Maryam waya nan ta sanar da shi abinda ta gayawa Kaka," Insha Allahu zamu zo tare, Kafin nan ma zamu shigo Ranar Assabar tare dasu, wani Irin daɗi Maryam taji, sun jima suna hira tana bashi labari Abdulmalik da yajima da sanin sunan sa a baki, Kafin nan sukayi Sallama, cikin wani irin ya nayi mai ɗauke da tsantsan farin ciki.tace , " Kaka Abba ya ce zasu zo ranar Assabar tare da su Haydar! Allah ya nuna Muna," Amin Kaka..." Washegari tunda da sassafe Abdulmalik na shigo ta bashi Labarin su Haydar zasu zo, "Ya Maleek karka je Kasu kaji," "saboda me?" "ka zauna gida muyi hira tare dasu Haydar" "Maryama ta! Idon na zauna a gida wazai min aiki na?" "Ya Maleek don Allah fa nace" " Shike nan zan zauna Amman idon suka jima basu zoba zan wuce kasuwa kin yadda" "Ehh Na yadda na san Abba da wuri zai yake zuwa duk lokacin da zai zo" "Nadai faɗa Miki" "Naji" ta faɗa cike da tsiwa tare da murguɗa baki" "Wannan bakin wata rana saina canye shi idon baki dena murguɗa shi ba" Kallonta Abdulmalik ya yi kana ya yi Murmushi a hankali ya ce ,"Maryama Sarkin tsiwa" A gurguje suka karaya ganin lokaci na tafiya, lokaci ɗaya suka kammala kana sukayi Kaka sallama kai tsaye suka wuce makaranta daga can ya wuce Kasuwa.... sai dare ya dawo, Yau take Assabar tunda sassafe Kaka ke aikin Abinci nan take gidan ya gauraye da ƙamshi mai daɗin gaske koda 8:30 tayi Kaka ta kammala komi tare da taimakon Maryam suka gyara gida tare da kunna turare