← Book details Dr Sultan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 54

Sashe 4

Dr Sultan Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

_💖Story And Written💖_
⬇️
*Sadeeya Ka'oje*

💖الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر💖


.Bismillah........ ✍
https://chat.whatsapp.com/CuNxneQ0ONc6x9yn9a16Jj

*💋TITAN'S OF TALENT💋*

*Marubuta masu aiki da fasahar zamani , zalar ilimantarwa,fadakarwa dakuma nishadantarwa*

*(T .O.T)*
*Breathe in courage, breathe outfear, together we stand*

*Alkalaminmu abin alfaharn mu*

*Page 3-4*

_______ Washe gari , gaba ki ɗaya yinin wannan Rana haka ya yini a kasalance, komai a hankali yake yinsa, zaune suke a tsakiyar gida, suna hira, Kaka ta kalleshi cikin sanyi Murya ta soma magana,
"Abdul Maleek mike da munka"? cewar Kaka, " sassanyan Nunfashi ya sauke, " Ba komi Kaka, gaji ya kawai ke da muna, " Ka tattabar ba komi"? A karon farko ya saki Murmushi,"ALLAH Ba komai Kaka!, "Shikenan, "taso muyi karatu, ya faɗa yana kallon Maryam dake kwance, a hankali ta mike ta nufi daƙi ta dawo dauke da jakar Makarantar, nan suka soma yin karatu cikin natsuwa da kwanciyar hankali, kana ya yi musu sallama, bayan ta fiyar shi Kaka ta rufe gida kana suka wuce ɗaki suka kwanta,
Washe gari ma haka ya tashi ba wani kuzahari, jikin sa ya musu sosai da mafarki, duk da ba wannan ne karo na farko da ya fa irin wannan mafarkin, tawon sati guda kenan yana fama da kasala, Kaka tayi tambatayar duniya ya ki ya faɗa mata,
Bayan Isha'i kamar ko yau she tana tsaye a ƙafar gida, tana jiran da wowar shi, ta ɗau tsawon lokaci tsaye a ƙofar gida tana jiran da wowar shi, " Maryam wai miki ke a waje"? " Kaka Ya Maleek nake jira!"
Ajiyar zuciya Kaka ta sauke, tare da faɗin Allah ya sa yaron nan lafiya yake? bai taɓa kai irin wannan lokaci ba, "Allah ka tsare shi a duk inda yake"
Cikin tsananin da muwa Maryam ta shigo gida, " Kaka ya Maleek bai dawo ba har yanzu ta faɗa kaman Za tayi kuka, Murya na rawa tace" Kaka muje mu nemo shi Kaka!" Bata jira me Kaka zata ce ba ta wuce ɗakin ta ɗauko jiha bi da fitala, kana suka fice daga gidan hankali a tashe, saboda bai taɓa kar War haka ba, "Kaka ko zamuje Kasuwa ƙila yana can, Maryam ta faɗa a hankali, "Bana tunanin yana kasuwa wani lokacin idon Oga ya riƙe shi a kasuwa, yakan kirani da wayar Oganshiya ya sanar dani, " Kaka ƙila ya ƙira ba Network, "da wuya idon yana Kasuwa, ganin Maryam ta matsa sai sunje kasuwa,hakan ya sa suka wuce kasuwa, Nan mai shagon ya sanarda su tun bayan Isha'i ya wuce gida, cikin tsananin tashin hankali da dake tattare dasu, suka baro kasuwar,Nan suka ruƙa neman shi cikin Unguwa,duk sun san baya zuwa gidan koma ha salima ko aboki Baida idon ka ganshi tare da wani to Maryam ce, " Kaka ko zamuje ɗakin sa"? cewar Maryam, "Anya wuya yana ɗakinsa, "Kaka muje mu duba, Haka suka ɗunguwa zuwa ɗakinsa, iso warsu ya yi dai dai sakin wata irin ƙara mai razanarwa, nan take jikin Maryam ya soma ƙarƙarwa,"“Innalillahi wa innailaihi raji'un!! Abdul Maleek ta kira sunansa a rauna ce, da sauri ta nufi cikin ɗaƙin, tana kiran Sunanshi" Abdul Maleek! Abdul Maleek!! tsawa tayi cak, tuni Abdul Maleek ya suma babu a lamar Nunfashi atare dashi, Rungumeshi Kaka tayi tana kiran Sunanshi, cikin tsananin tashin hankali Kaka ta fashe da Kuka tana kiran Sunanshi....
A Ɓangaren Maryam tuni ta fita haiyacinta,
jikin Kaka sai karkarwa da kyar ta tattaro ƙarfi ta, kana ta janye shi daga jikinta, ta zuba Nishi ruwa, ya sauke Nannauyan Ajiyar zuciya, a hankali ya shiga karanto Addu'oi cikin ikon Allah hankalinsa ya fara dawowa jikinsa, a hankali ya ɗago da idanunsa da suka kaɗan sukayi jazir ya kalli Kaka ya yi ƙasa da kanshi, Murya a dishace ya ce "Kaka! zasu tafi dani sai kuma ya fashe da Kuka, A razaje Kaka ta ɗago ta kallesa Zuciyarta na bugawa da ƙarfi idanunta a kansa, "Suwa ye zasu tafi da kai Abdul Maleek!" su tafi da kai su kaika Ina?"
Kai ya gyaɗa mata cikin tsananin tashin hankali da ruɗu dake tattare dashi ya fashe da kuka mai tsuma zuciya, Murya a dishace yace,"Kaka wlh tafiya zasuyi dani Kaka bana son rabuwa daku! "Kaka Ina Maryama ta!"
Wani sabon Kuka Kaka ta fashe dashi tana girkiza kai" Abdul Maleek ba inda zasu kai ka, Abdul Maleek sam baya cikin Haiyacinsa sai sabbatu yake,
Maryam dake baƙin ƙofa tana sauraren sabbatu da Abdul Maleek yake, ta durƙu she a wajen ta saki wanin irin marayan kuka,
Kwallnshi kaka keyi cike da tausayawa ganin yadda ya takure a waje ɗaya yana sabbatu, cikin raunan'nanyar Murya Abdul Maleek yaci gaba da fadin "Kaka gasu nan zasu tafi dani, Wayyo Allah na!! nan Kaka ta shiga tafa Nishi Addu'oi, a hankali ya fara sauke Ajiyar zuciya, Nan take jikinsa ya sake, sai lokacin Maryam ta samu damar shigowa ɗakin, cikin tsananin tashin hankali ta kalli Kaka Murya a dishace ta ce,"Kaka don Allah karsu rabani da Ya Maleek! zujjuya kai ta farayi kaman zautacciya hawaye na bin fusakar ta cikin muryar Kuka ta soma kiran Sunansa, "Ya Maleek karka tafi ka barni don Allah Ya Maleek idon ka tafi ka barni mutu.... ta kasa ƙarasa maganar tayi sai kwai ta fashe da Kuka..... Kaka kam tunu jikinta Ya yi sanyi, Ajiyar nan ta sauke tare da fesar da Numfashi, cikin raunin Murya ta ce "Maryam ki dena kuka karki ta dashi daga bacci Kinga da kyar na samu ya koma Bacci, da sauri tasa hannayenta tana share hawayen, "Kaka na dena Kuka" murmushi ƙarfin hali Kaka tayi kana tace Yauwa " Yar Albarka!" haka suka kasance a dakin na ɗan wani lokaci, lokaci lokaci kaka na tofa mishi Addu'oi, shiko sai sauke Ajiyar zuciya yake, fusakar shi tayi fayau duk da bacci yake Amman tashin hankali da fargaba ke kwance a saman fusakar sa,,
Wuraren 11:30 ya fara buɗe idanunsa da suka kaɗa sukayi jazir bishi bishi yake gani cikin wani irin ya nayi ya danƙi hannu kaka cikin nasa bugun zuciyarshi na tsananta,a hankali ya fara buɗe idanunsa da sukayi masifar nauhi ya sauke su a kan Kaka dake riƙe da Hannu sa, Maryam ta ɗora nata a sama, cikin wata irin murya mai ciki da rauni yace "Kaka zansha ruwa!" da sauri Maryam ta janye hannunta ta ɗebo ruwa cikin robar fenta dake cikin ɗakin, "Gashi Kaka a hankali ya ɗari da kanshi Maryam ta saka Nishi ƙofin A baki haka ya riƙa zukar ruwan maƙoshin na bata wani irin sauti kwat kwat tas ya shanye ruwan, wata irin Zufa ce ta riƙa tsastafo mishi daga saman kai, ya sauƙe sassanyan Numfashi, Murya a dishace yace, " Nagane Maryama ta!."Abdul Maleek me kame ji Yanzu? Kaka ta tambataye shi cike da kulawa" Murmushi ƙarfin hali ya yi cike da ɗauriya, " Bana jin komi kak, " Ka tabbatar"? Kai ya gyada mata a lamar ehh, tashi muje gida ka kwana a can kaga dare yayi ba'a san me zai faru ba, "A'a Kaka ki bari kwai zan kwana a nan,
Maryam kowa idanuta ne suka shiko da kwalla, cikin sanyi Abdul Maleek ya dafa kafaɗar Maryam, cikin sanyi Muryar mai cike da natsuwa," Maryama ta kiyi haƙuri ki Dena kuka Kinji kina son Nima nayi kuka!"? da sauri ta girkiza kai, "Yauwa" Kaka kam sai kallon su take, Ajiyar zuciya ta sauke tare da fesar da Numfashi ta kalli Abdul Maleek ɗin, " kasan baka da Lafiya me saya Baka je gida ba? A hankali Abdul Maleek ya tauna lip dinsa, cikin sanyi Muryar yace," Kaka wlh lafiya kau na baro kasuwa, ina shigowa Unguwar nan kaina ya yi mugun sarawa nan take zazzaɓi mai ƙarfi ya rufeni da kyar na iso ɗaki na tare da taimakon Kabiru" Kaka ko ido ta tsurawa Abdul Maleek kaman mai son gano wani Abu, A karon farko ya saki Murmushi...✍️✍️
*DR SULTAN*
*( THE BEGINNING)*

_💖Story And Written💖_
⬇️
*Sadeeya Ka'oje*

💖الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر💖



Bismillah........ ✍

https://chat.whatsapp.com/CuNxneQ0ONc6x9yn9a16Jj

*💋TITAN'S OF TALENT💋*

*Marubuta masu aiki da fasahar zamani , zalar ilimantarwa,fadakarwa dakuma nishadantarwa*
Chapter 4 · 0% Book details