Sashe 16
Dr Sultan Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
tunda Ya Maleek baya nan! Nan take maryam ta fashe da kuka,"shike nan ya isa ki Dena kuka nan zamu ci gaba da zama insha Allahu Kaka ta faɗa cikin sanyi Murya" tare da sharewa Maryam hawaye, " Nagode sosai mama Allah ya ƙara Miki lafiya da nisan kwana!" cewar Abdullahi, "Amman ya kamata mu naje ƙaraye ko don nayiwa maƙotana sallama" "shike nan mama ko yanzu zamu iya tafiya! " kaka Ni kam ba zanje ba cewar Maryam" Nan take Kaka ta shirya suka wuce tare da Abdullahi" *ƘARAYE* Suna isowa kai tsaye suka wuce gidan cike da kewar Abdulmalik da ke mata gizo a tsakiyar gida, isowar keda wuya Mutane Unguwar suka fara shigowa tare da yiwa Kaka Gaisuwar Abdulmalik da Kubra, nan take Mutuwar ta dawo mata sabuwa, cikin dauri ta shiga amsa musu tare da faɗa musu zasu koma birni da zama, kowa sai tambatayar Maryam yake, haka Kaka ta shiga rarraba kayan Abincinta ga duk wanda ya shigo gidan, kana ya shiga haɗa musu kayan su da duk wani Abin mafani aka saka a motar Hilux dasuka zo da ita, "Abdullahi sai batun gida ya za'ayi dashi kasan idon aka bashi ba kowa zai nakkashe miye shawarar ka," Mama ina ga kwai ki kyautar dashi ga duk wanda kikega dama, "Bana da sauran dengi a duniya kaman yadda kaima baka saura kowa a duniya. sai Ni, da iyayen Hauwa'u suna rare sune suka fi cancanta dana mallakawa gidan!" Abdullahi ya sauke Ajiyar zuciya kana yace Hakane Mama! Barinsa haka zai sa ya lalace ko bata garin su samu wajen aikata barna" "zan mallakawa Malam liman idon har ka amince, " Haba Mama miye saina wani Abince damu da gidan duk a ƙarƙashin ikon ki muke duk wanda kika ba banda matsala!" "Allah ya yi maka Albarka!" "Amin Mama" Bayan sun gama kwashe duk wani abinci mai mahimmanci suka wuce gidan Malam Liman, bayan ya fito suka gaisa kana ya yi mata gaisuwa, a hankali Kaka ta miƙa mai makullin gida, batare da yasan na miye ba karɓa, "Malam Liman zanmu koma Kano da zama Insha Allahu, wannan makullin gidan muna na mallaka mashi halak malak, cikin tsananin Mamaki Malam liman ya waro ido yana kallon Kaka, Murya na rawa tace ," Mama kin mallakamin gida, saiga waye shar a fuskar malam liman har ƙasa ya duƙa tare da yiwa Kaka godiya, Kaka tayi sauri dakar dashi," Haba Malam liman miye abin godiya anan, da sauri ya nufi cikin gida jim kaɗan suka dawo tare damatar shi, fusaka a sake ta ciga yiwa Kaka godiya.... Haka Kaka riƙa shiga gidan maƙota tana musu sallama, kana suka wuce cike da kewar ƴan uwa da abokan arziki...Sai bayan Isha'i suka iso gida cike da gajiya nan masu aiki suka fara shigar da kayan cikin gida, Kaka na shigowa Suka rungumeta gabaki ɗayan su suna mata Oyoyo kana suka wuce daƙi.... ★★★ yana shigo wa dakin yana farka da sauri ya nufi wajen sa, a hankali ya fara idanunsa suka kaɗa sukayi jazir cikin Wani irin mummunan yanayi ya soma magana murya a disashe yana faɗin ,"ruwa Maryama ta! Zan sha ruwa Kaka ƙishi nake ji!Alhaji Nuraddeen dake tsaye a wajen cikin tausawa yace ",Ruwa kake so? A hankali ya gyara kai, ruwa masu sanyi ya ɗauko cikin fridge a hankali ya fara murɗa wani ƙarfe dake jikin gado,, gadon ya fara ɗagowa kana ya zauna kusa dashi ya buɗe marfin gorar ruwa ya ɗora mishi a baki hannayenshi ya ɗoro saman gorar yana zukar ruwan da ƙarfi har kana iya jin sautin maƙoshinsa dake kwat kwat cike da tausayawa Alhaji Nuraddeen ke kallo sai, da sauri ya janye bakinsa tare faɗin," Ruwa Kaka ban kwoshi ba! a karo na biyu yasa ake dora mashi gorar ruwa ya shanye ta tsas kana ya sauke Nannauyan Ajiyar nan take Zufa ta riƙa tsastafo mishi, dai dai lokacin Dr ya shigo fusakar ɗauke da murmushi, " Masha Allah ya farka kenan?" " Ranka ya dade yaushe kashigo?" Alhaji Nuraddeen ya sauke Ajiyar zuciya mai ɗumu kana yace Ban jiba ina shigo yana farkawa ka" Nan Dr ya shiga dubashi ," Masha Allah komai ya yi dai dai Insha Allahu, zuwa gobe za'a iya sallamar shi!" A hankali ya ware mayan idanunsa da suka kaɗa sukayi jazir ya sauke su akan Alhaji Nuraddeen dake zaune," murya a disashe yace ," Ina Kaka Ina Maryama ta!" Alhaji Nuraddeen ya yi Murmushi kana ya kwantar da hankalinka kaji Wanne gari kake,"Karaye!" Nan Alhaji Nuraddeen ya bashi labarin inda ya gansa a hankali abinda ya faru ya fara dawo mishi a kwakwalwa nan take ya fashe da Kuka mai tsuma zuciya, da kyar Alhaji Nuraddeen ya shawo kanshi ya Dena kuka ," Kana da Numbar iyayenka na sanar dasu nasan yanzu yana suna cikin tsashin hankali," Murya na rawa yace ," Iyayena sun rasu! bana da kowa sai Kaka da Maryam!" Cikin tsananin tausai Alhaji Nuraddeen ya kalleshi kana da Numbar Kaka kota Maryam!?"kabani na kirasu na sanar dasu Halinda kake ciki? A hankali ya gyara kai nan ya shiga faɗa mishin number kaka Kiran farko aka sanar dashi number aka take a karo na Barka tai yariƙa kiran Number a kashe daga karshe ya haƙura... "Number a kashe take, ko Kanada wata number," A'a!" "Zan yi Sallah! A karon farko Alhaji Nuraddeen ya saki Murmushi, " Kasan kwananka nawa a Asbitin nan kai ya gyaɗa a lamar a'a, yau kwanan ka Hudu" a Asibitin nan,, "Murya a disashe yace yau nawa ga wata?" Alhaji Nuraddeen ya faɗa mishin," Nan ya fahimci iya a daɗin kwanakin da ya rasa sallah Alhaji Nuraddeen ya taimaka masa zuwa toilet wanka yayi da duwa ɗumi kana ya yi Alwala ya fito sosai yaji daɗin jikin sa....kasan cewar baida karfi jiki da zaune ya yi Sallah tsawon lokaci ya dauka yana rama sallalolin da ake biyar shi, duk wani motsin sa akan idon Alhaji Nuraddeen sosai yaron ya burkeshi, Bayan ya gama sallah ya zuba mai Abici palpesu kayan ciki kana ya haɗa mishi tea mai ƙauri kana ya miƙa miƙa mishi," Kaci kasha magani ko Yarona!" da sauri ya ɗago ya kalleshi ya sakar mai murmushi, a tsanake ya soma cikin Abinci, sosai palpesu ya yi mishi daɗi, bayan ya gama cikin Abinci yasha magani nan take bacci ya yi awaon gaba dashi..... Saida Baccinsa ya yi nisa sosai kana ya fice daga ɗakin kai tsaye ya wuce gida a gajiye, Washe gari tunda sassafe ya wuce Asbiti koda ya shigo dakin yana zaune a Dr na dubashi ," Ranka ya dade sannu da zuwa" yauwa ya mai jiki?" Alhamdulillah zaku iya tafiya gida yanzu," rubuce rubuce ya yi a takar da kana ya miƙa mishi, Murya a disashe yace "Ina kwana Baba!" A hankali ya sauke sassanyan Ajiyar zuciya, "Lafiya lau Yarona ya jiki?" A karon farko ya saki Murmushi kana yace ," Lafiya lau Baba!" Yauwa sha tea sai mu tafi gida ko, cikin tsananin farin ciki ya daga mishi kai, tea ya haɗa mishi mai kaura kana ya bashi a hankali ya riƙa sha yana Lumshe ido, bayan ya gama suka fice daga ɗakin tare da yiwa Dr godiya kai tsaye suka wuce Nasarawa, lokacin da suka iso gidan haka ya saki baki yana kallon gidan a rayuwarshi ta duniya bai taɓa ganin gida mai kyau irin wannan duk abinda yake a kan idon Alhaji Nuraddeen, koda suka shigo palon zaune take tana kallon,"Habi..... sai kuma yayi shiru ganin yaron dake tsaye, fuska a sake ya gaisheta, "gabaki ɗaya ta kasa ɗauke idonta akan shi, "Ummul khairi lafiya?" Tadanyi Murmushi kana tace ba komai shine marar lafiyan?" "Ehh shine an sallame shi" " Masha Allah ,Allah ya ƙara sauki" "Amin" Kaisa ɗakin ɓaki ya huta koda yake bari yayi breakfast" tare suka wuce darning shiko sai ɗari ɗari yake sam ya kasa sakin jikin sa abinci ma kaɗan ya ci, kana ta kaishi ɗadakin baƙi, mashi Allah dakin ne na Alfarma komi na ɗakin farii ne, " Kayi Wonka sannan ka kwanta ko zakaji daɗin jikin ka" cikin sanyi Murya yace ," Toh Mama! Nagode" tana fitan ya kalli dakin da kyau kana ya sauke sassanyan Nunfashi, ƙofor dake like a dakin ya kallon hakan ya tabbatar mai da toilet ne a hankali ya buɗe kofar ya yi Addu'a kana ya shiga Wonka ya yi da ruwan dumi ya fito nan ya tarar da kaya saman gado ciki da mamaki ya riƙa bin kayan da kallon,ƙananun kaya ne masu matsifar kyau da tsada bayan ya saka kayan ya kalli kanshi a madubi ganin yadda ya yi matsifar kyau," Ina kike Maryama ki ga wannan kyau! Yana jima yana kallon kanshi a madubi, can muka ya ɗan ya mutsa fuska ganin yadda ya rame, sanyi ɗakin ya sakar mai da matsananciyar kasala hana yasa ya kwanta saman katafaren kadon ya lunlube da laulausar blanket nan take bacci ya yi awon gaba da shi.....✍️✍️ _More comments and share_ *Sadeeya Ka'oje ce*💋💋 *DR SULTAN*