← Book details Dr Sultan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 54

Sashe 32

Dr Sultan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*The beginning* *Page 23-24* _____ Alhamdulillah an shiga watan azumin ramadan cikin rahamar Allah da yardarsa. Kowanne musulmi na ƙwarai yana cike da farin cikin shigar wannan wata mai tarin Albarka dake zuwa mana a cikin watanni goma sha biyu na shekara sau ɗaya kacal ya wuce. Randa aka kai azumi na goma Daddy ya gama shirya maganar Umrah da sukan kanje duk shekarar, tafiyar baifi saursa kwana uku ba Kaka ta kwanta Zazzɓi, hakan yasa Mami ta fasa tafiya, Amsar passport ɗinsu Daddy yayi musu komai su duka,.Haka kawai sai Sultana ta tsinta kanta da rashin jin ɗokin zuwan, duk da kuwa tana matuƙar son rayuwa a ƙasar saudia saboda karon nan da sultan Za'a tafi. Ranar Ta samu Kaka a ɓoye ta roƙeta akan ita bazata je ba karon nan, ita batason zuwa batajin daɗin jikinta. Harara Kaka ta watsa mata tana taɓe baki. Batare da tace mata Uffan ba a zancen ta ɗauke kanta ta maida ga karatun Alkur'ani da take karatu. “Kaka dan Allah Sultana ta faɗa cike da shagwaɓar data saba yima Kaka tana kwanciya mata a gefen kafaɗa. Ture mata kai Kaka tayi tana faɗin, “ da Allah jacan Dukfa take-takenku ina sane dasu. Yanzu bautar Allah ce ma baƙyason zuwa saboda Sultan zaije ko yaya? Baki Sultana ta sake kumburawa tana faɗin, "Kaka don Allah fa" Kuma Umrah babu fashi sai kinjeta. Dan Allah idan kunga juna ke da Sultan ku mutu Ni bansan me yaron nan ya tare Miki ba, haka ranar naji kina zaginsa don ya yi Miki Allura. Sultana bata sake tankawaba, dan ita ɗaya tasan damuwar da take ciki. Washe gari Jirgi su Sultan ya ɗaga tare da su Ihsan, Salma, Salim, Mommy,. Bayan shan ruwa suna zaune a Palo, Sultana na kwance saman cinyar Kaka Lafiyarki kuwa Sultana? Kina tafiya kamar hankalinki baya jikinki?”.Kaka dake zaune a falo tana duba ta faɗa tana kallonta. a hankali ta kiƙe saune ɗora kanta gefen kafaɗar Kaka ɗin. “Kaka kaina ke ciwo fa yau tunda safe,. Shiru Kaka tai kawai tana kallon Sultana, dan gaba ɗaya a kwanakin nan tana kula da ita kamar akwai abinda ke damunta. Ta zaunar da ita yafi a ƙirga tana tambayarta amma sai tace mata babu komai. Jin Kaka batace komaiba itama sai bata sakeyin magana ba, tama lumshe idonu kamar mai barci. Sun jima a haka, kafin Kakada taji Sultana ta mata nauyi a kafaɗa taɗan ɗago ta kalleta, numfashi take saukewa a hankali na barci. ta girgiza kai kawai da ɗagota a hankali ta gyara mata kwanciya a kujerar tare da ɗaura kanta saman cinyarta. Aiko kamar jira take saita sake gyara kwanciya da ƙyau a cinyar Kaka ɗin. "Mama lafiya take kuwa?” Abba ya ya faɗa yana ɗaura hannunsa saman goshin Sultana. Ɗago ido Kaka tai ta kallesa dai-dai ya janye hannun ya sake maidawa a gefen wuyan Sultana. “Lafiya lau take, barcine kawai”. Janye hannun ya yi yana sauke ajiyar zuciya da faɗin, “To Alhamdulillah, "Abban Haydar har ka foto, Mami ta faɗa lokacin da ta fito daga Kicin tare Meena. "Zanje gidan Nuraddeen, Kanta ta jinjina masa cike da girmamawa, tare da masa addu'ar dawowa lafiya. "Amin ya amsa ya yi gaba. Harya kusa ficewa a falon sai kuma ya tsaya tare da juyowa. “Banji motsin su Arif ba, " Sunyi bacci tun ɗazu..... ★★★ Yau Azumi 15, yaune Kuma su Sultana zasu wace Umra. Kaka ta Zaunar da ita Kaka tayi tai mata doguwar nasiha akan wannan tafiya, tare da tunatar da ita manyan ibadu da idan taje zata maida hankali a kansu ba shashanci ba. Tsaf Sultana ta riƙe komai a ranta, tareda ƙarfafa ranta akan in sha Allah zata zama mai himma. Ƙarfe 10:40.jirginsu ya ɗaga zuwa ƙasa mai tsarki. Ta tafi cike da kewar Kaka da Mami da Jidda.. _____________________ *SAUDI'A* Cikin sa'a kuwa yana isa airport ɗin jirginsu na sauka.Lumshe idanu tayi tana karanto addu'oi da fatan cika alƙawarin da taima Kaka akan kama kanta. A hankali suka fito. Sanye take cikin Abaya mai masifar kyau, an ma rigar ado da duwatsu manya da ƙanana, sai veil da ta naɗa a kanta wanda ya sake fidda ƙuruciyarta da ƙyawun da Allah ya bata. Farar ƙafar ya haska tana sanye cikin Black ɗin takalmi da yayi masifar mata ƙyau. Sai ƙaramar jakarta itama dai Black ɗince. Kallon agogon dake ɗaure a hannunta tai lokacin da suke ƙoƙarin sakkowa daga jirgin, ta ɗan yamutse fuska tana sauke hannun a hankali da kai dubanta can ɗan nesa dasu. Wani irin bugawa ƙirjinta yayi saboda hango Sultan dake tsaye jikin mota sanye cikin Jallabiya ta masa ƙyau.sosai, ya ƙara ƙiba da ƙwarjini a idanun mai kallo kamar ba azumi ake ba, Sultan da ya yunƙuro saboda hango Daddy dake a gabansu da yayi yaja ya tsaya cak lokacin da idanunsa suka sauka akan Sultana ƙirjinsa ya yi matsifar bugawa , ya kasa motsi balle ɗauke ido daga kallonta har suka ƙaraso inda yake. Abba ko sai kallo su yake,"sultan ya ibada ya Abba ya faɗa tare da kallon sultan ɗin. sauƙe Nannauyan Ajiyar zuciya,ya kasa ɗauke idanun nasa daga kan Sultana da ta ɗauke kanta gefe tamkarma batasan da zamansa ba a wajen. "Alhamdulillahi Abba da ƙyar ya janye Idanunsa daga kallon Sultana. "Daddy sannu da zuwa, "Yauwa my Boy, Meena ta nufi wajen Sultan ta rungumesa tare da faɗin,"Ya Sultan ya ibada?, "Alhamdulillahi Aminatu!" wani irin tsam take ji a jikinta duk lokacin da ya kira ta da sunan, ɗaya bayan ɗaya ya riƙa rugumersu Haydar, kana suka shiga Mota, Sultan kam rabin hankalin na'a tuƙi ne rabi akan Sultana da a yanzuma ta ɗauke kanta tamkar bata gansa ba. A haka suka iso gidan nasu a mai ƙyau da tsari da Daddy ya saya musu Saboda Aikin Ummra da yake zuwa duk shekara. Sai da ya Parking motar inda ta dace kafin su fita shi da Haydar ya buɗe musu Mota suka fito, Sultana a kuma ta buɗe da kanta ta fito tana kallon gidan ta yi da duk shekara suka sai sun tarar da An sabun tasa, zuciyarta har wani zallo take saboda ganin Sultan, duk yanda tai tunanin zata daure sai ganinsa ya canja dukan ƙudirin nata lokaci guda. Sai dai kamar yanda ya fiske itama haka tai ƙoƙarin fiskewar. dai dai lokacin kuma su Salma da Salim, suka iso wajen A guje tare da Rungume Sultana,"Anty Sultana oyoyo, suka faɗa tare cike da tsantsan farin ciki, "Anty Sultana I miss You! "Miss you too my baby's ta faɗa tare da shafa kumatun su, kana suka nufi wajen Abba,"Abba ina Mami da Kaka? Me yasa basu zo ba?, "Salma kaka ce ba lafiya shiyassa basu zoba" Marairaice fuska Salma ta yi tare da faɗin,"Allah ya bata lafiya Abba" "Amin Ummul Salma!" Ƙirjin Sultan ne ya yi matsifar bugawa.cikin wani irin yanayi ya lumshe idanusa kana ya buɗe akan fusakar Salma yana mai jin tsakanin Sonta a ransa. "Ya Haydar, Ya Khalil Ya Arif ya Hanya?" "Lafiya lau little Sis, Sunan da Sultan ke kiran wani lokacin.. Daddy ko kallon yayan nasa yake cike da so da kyauna... Sultan ne a gaba lokacin da zasu shiga gidan, cewar Daddy ya yi musu jagora shine mai gida suko baƙi ne Sultana ita ce ƙarshe tana karanto duk addu'ar da tazo mata a baki domin samun sassauci daga daga bugun zuciyar da takeji.. Falon tsaf yake ko ina a gyare, ga ƙamshi mai daɗi yana tashi da sanyin ac. cikin tsananin farin ciki Mommy ta musu sannu da zuwa, "Oyoyo Anty Sultana. Karan farko Sultana ta saki wani lallausan murmushi da har ya bayyana fararen haƙoranta waje, ta taho da wani irin ɗoki ta rungume Mommy, a hankali Sultana ta janye jikin, ,"Anty Yara ya jikin Mama!" "Alhamdulillahi Mommy taji sauƙi sosai, Gabaki ɗan su suka Rungume Mommy, "Arif Autan Abba ina Mami," Arif ya yi Murmushi kana yace ,"Lafiya lau take Mommy, Mommy ta maida kallon ta ga Ihsan kana tace,"Ihsan kai musu kayan su ɗaƙi," Mommy Nidai a ɗakin ki zan zauna Nana ta faɗa cike da shagoɓa,"TOH shike nan..," Mommy Nima a ɗakinki zan zauna, taso ki koma ɗakin Ihsan, Kafinma Mommy ta rufe baki cikin sauri tace, “A'a zan zauna anan tare da ke Mommy. da ga Mommy har Daddy kallonta sukai, amma saita ɗauke kanta tana ɓata fuska danma kar Mommy tace dole sai taje. Abba Shima har zai sake magana sai kuma ya fasa. Murmusawa Mommy tayi kawai tana ɗauke kanta batare da ta sake cema Sultana komai. Sultan Kafeta yayida idanu kamar mai nazarinta, sai kuma ya ɗauke kawai yana ƙaɗa kansa.. Har ɗaki Mommy ta wuce da Sultana. Kana ta dawo Palo, Daddy ya kalleta cike da zolaya yace ," Kinga ya yanki kin manta da ni ko?" Kai ta sunkuyar cike da kunya Sultan dake zaune a Palon, tuni su Meena sun wuce ɗaki tare da Ihsan.. "Ya hanya?" Mommy ta faɗa cikin girmamawa. "Alhamdulillahi" "Bari muyi sallah ko, "Toh sannan suka fice atare kai tsaye masallacin suka nufa cike da nutsuwa da kuma kamala suka gabatar da Sallah da karatun Alkur'an.. Bayan sallah la'asar suka wuce Kicin don haka kayan buɗe baki.Cikin ƙanƙanin lokaci dai suka haɗa duk aiyukan da zasu iya ajiyesu ba tare da sun samu matsalaba. Cikin ikon Allah shida da Rebi suka gama kan aikinsu. Sultana , ta jerasu a Foodflaks, Nan duk suka wuce ɗaki. Wanka sukayi, kana sukayi al'wala sannan suka fito falo. A nan suka samu su Daddy,Koda aka kira sallah ruwa da dabino kawai suka ɗanci, sannan suka gabatar da sallah magriba ,tare suka shigo gida, Ihsan ta kalli Sultan da gaba ɗaya hankalinsa akan Sultana yake. Haushine ya sake turniƙeta, murya a cinkushe tace, “Ya Sultan Barka da shan ruwa Kallo ɗaya yay mata ya ɗauke kansa. "Lafiya" Nan suka shiga gaida iyayen nasu. Dai dai lokacin kuma Massage ya shigo a wayar Sultana, a hankali ta ɗaga wayar ta karanta massage ɗin, *Barka da shan ruwa Sweetheart, Allah ya ƙarɓi ibadar mu. daga NAS* taɓe baki tayi a hankali tace ɗan wahala kayi ka kagama, Cikin sanyi Murya Meena ta ce ,"Nas ne halam? Kai ta ɗaga mata.... A haka dai suka kammala buɗa bakin, yayinda kowa yaci
Chapter 32 · 0% Book details