← Book details Dr Khaleed Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 91

Sashe 9

Dr Khaleed Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

[10/10, 6:36 AM] ‪+234 701 117 6189‬: ~Dr Khaleel~ By Khaleesat Haiydar
17.....
Abba ya tsura mata ido snn yace "to wa ya turo sa" Ashnaah ta shiga share hawayen fuskarta tana girgixa masa kai tace "wllh Abba ban san wanda ya turo sa ba, ni ban san shi ba, ban san daga ina yake ba," tsawa Abba ya daka mata a fusace yace "ni kike ce ma baki san sa ba" Ashnaah ta fashe da wani sabon kukan tace "Allah Abba ban san shi ba sharri yake min, Abba ya kuma daka mata tsawan yace " tashi ki ban waje" kin tashi tayi ta ci gaba da rusa masa kuka tana cewa ya yrda da ita, mikewa Abba yyi a fusace hkn yasa ta tashi da sauri ta bar wajen ta nufi sama, kasa komawa ya xauna yyi ya shiga kai koma a falon yana naxarin abinda Ashnaah ke cewa ynxu, wayarsa ya dauka ya kira mum dinta yace ta same shi falonsa, ba a dau lkci ba ta sakko kasa, ya nemi kujera ya xauna yana kallonta yace "A ina Ashnaah suka hadu da wnn yaro da ke shirin aurenta?" Momy tace "sae yau kasan da wnn tambayar?' Tun da baka yi ta ba sae da aka daura aure, to ko kadan Ashnaah bata san daga inda mutumin yake ba, to da yake na ga Neman Kai kke da 'yar taka shi yasa ban katse maku hanxarin Ku na aurar da ita ba," Abba ya Mike tsaye ransa a bace yace "kar Ku raina min hankali, ni xa Ku maida yaro ko karamin mutum, Ku hada baki ke da yar ki Ku xo nn Ku caxa min kai, to bari kiji ko da ma da gsken ne bata san mutumin nn ba wllh wllh bbu abinda xae hanata xaman aure da shi, in an kai ta gidan nasa ma ya yanka ta karewar komae knn, yarinyar da bata dauki maganar uban da ya haifeta a bakin komae ba meye amfaninta, ba abun kunya bane ba ma ace kmr ni ana ganin 'ya ta gidan cin abinci da holewa da saurayi, da na hanata wnn sae ta koma wancan sbda ta raina ni ke kuma kina kare ta, to ki koma Ki gaya mata plan din naku Bae yi aiki ba," ya ja tsaki ya ce "mutanan bnxa kawae" dakinsa ya nufa ransa a bace, kan ya shiga ya juya yana kallon Momy da hawaye ya gama wanke mata fuska yace "kar kuma yar nn ta kuskura ta kwana gidana yau, maxa ana magariba a tafi da ita dakin mijinta" yana kai wa nn ya shige dakinsa. Momy ta nufi sama jikinta a sanyaye tana ci gaba da hawayen da take. Dai dai lkcn wa enda suka je yi ma Ashnaah Jere suka dawo kowa na yaba gidan da xa a kaita, kanwar momy ta ja ta xuwa daki tace "haba yaya kukan meye wnn baxa ki daina ba tun daxu, wllh Ki kwantar da hankalin ki, ni na tabbatar maki wnn mutumin ba don ya cutar da ita yyi hka ba, kawae tsabar sonta ne, sae kin ga gidan wllh, Ashnaah ta samu gidan Hutu ni na tabbatar maki yaya," Momy tace "to da kike wnn maganan kin san aikin da mutumin yake ne" Anty farida tace "wllh likita ne, kuma ma babban likita snn mahaifinsa ma babban dan kasuwa ne, sae ma kinga ynda yan uwansa suka tarbe mu daxu wllh don duk suna gidan, ki kwantar da hankalin ki kawae yaya, ba mutanan bnxa bne" Momy ta share fuskarta tace "to Allah yasa, shi kuma Adam Allah ya shiryesa ya dawo da shi hanya". Karfe bakwae da kusan rabi aka tafi da Ashnaah gidan mijinta da bata sani, bbu abinda take masu sae aikin kuka a motar, ita takaicin ta bbu wanda ke son yrda da ita idan tace bata san mijin ba, tafiyar kusan minti talatin suka yi kafin suka iso gidan mai gadi ya bude masu gate driven ya ja motar ya shiga ciki ya samu gu yyi parkin, ana bude ma Ashnaah kofa ta fito ta cire mayafin kanta da sauri tana kare ma kantamemen gidan kallo tana huci ae kam mai gidan nn ya aurar ma kansa fitina da tashin hnkli, aka ce ta fito da kafarta na dama bata ko sauraresu ba ta fito da ta hagu abunta kuma da gangan, suka kama yi mata masifa wae bata jin mgna, bata ko kallesu ba ta shiga bin kanwar mum dinta suna biye da su a baya har suka iso babban falon gidan, bbu abinda bbu cikin falon ba jin ddin rayuwa, Antynta ta juya da sauri ganin yan uwan khaleel a falon tace " ke baki da kunya ko Ashnaah, baxa ki rufe fuskar ba, " Ashnaah ta wara idonta da mamaki tace "ji Anty fa, akwae me bina bashi a nan ne ya fadi in ji da har xan rufe masa fuska" ganin ynda antynta ke kallonta jikinta yyi sanyi don ba Karamin nasiha aka mata ba kan su bar gida daxu yasa Ashnaah ta daura mayafin hannunta a kanta fuskarta a daure ta rike kugu tana kare ma mutanan dake xaune falon kallo.
Chapter 9 · 0% Book details