← Book details Dr Khaleed Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 91

Sashe 24

Dr Khaleed Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

~Dr Khaleel~ By Khaleesat Haiydar
39.....
Dubu biyar Khaleel ya ciro ya mika mata yana kallonta, ta karbe
kudin ta bi bayan frnds dinta da sauri don har sun bar falon suna
dariya, bin ta yyi da kallo ganin ynda take tafiya har ta isa gun
frnds din nata snn ya kauda kai, da kyar Ashnaah ta tilasta su
suka karba kudin don kin karba suka yi da wae sun gode, Khaleel
dae na tsaye daga bakin kofa yana danna wayarsa lkci lkci ya kan
daga kai ya kallesu, ummi tace "to ki taya mu yi masa gdya
Ashnaah, sae wani lkcn kuma" da sauri Khaleel ya daga kai yana
kallon Ashnaah jin sunan da ummi ta kirata da shi wae Ashnaah,
meye kuma Ashnaah, Ashnaah kam har bakin gate ta rakasu snn
ta dawo abunta, har lkcn yana tsaye daga bakin kofa, ta gefensa
ta bi xata shiga falon ya fixgota yana mata wani irin kallo yace "wa
ya baki izinin shigo min da baki gidana?" Duk da ta dan tsorata
amma hkn bae Hana ta dakewa ba tace "to ni nasan ma wa ya
kawo su ba kawae ganinsu nayi ba nima" kallon cikin idonta yake,
ita ma hka, sunkuyar da kanta tayi da sauri don hka kawae taji
kunya ya kamata tuna abinda ya faru jiya da daddare da tayi, ko
hkn ya tuna shima oho, don kawae gani tayi ya dauke kai shima
ya saketa ya nufi gun dayan motarsa da ke Parke a parkn space
din gidan, don Wanda ya saba fita da ya baro shi a clinic,
Ashnaah ta shige falon da sauri abunta, sae da ta ji fitar motarsa
snn ta bude abincin da ya kawo mata, tuwo ta gani da miyar
vegetable yaji nama da kaza, nn da nn ta mike da sauri ta hau
sama ta wanke hannunta ta sauko ta shiga tura kayanta, bude
kofar falon aka yi ta juya da sauri har xata boye abincin ta ga
Meenah ce, ta Mike da sauri tana washe fararen hakoranta tace
"lah ashe dae xa ki xo, shigo mana kika tsaya daga bakin kofa"
Meenah tace "amma dae Khaleel baya nn koh" Ashnaah tace
"waye kuma Khaleel" tsakaninta da Allah tayi tambayar don manta
sunansa take, Meenah ta harareta, da sauri tace "ohh ya fita ynxun
nn, kinsan ni manta sunansa ma nake wllh wllh" Meenah ta karaso
falon har lkcn tana hararan Ashnaah tace "sunan mijin naki kike
mancewa" Ashnaah tace "wllh mance sunansa nake, khaleed ko
wa yake, to wae ma ba sae ka damu da mutun xaka rike sunansa
ba" Meenah ta fashe da dariya tace "ban gane ba, ke da sweetyn
naki kuma" Ashnaah ta tabe baki tace "sweetyn su dae, Sweetyna
na inda yake, Allah sarki usman" Meenah da mmki tace "ban gane
ba" Ashnaah tace "ae idan da Akwae Wanda na tsana a duniya a
ynxu bae wuce dan uwanki ba, Allah yasa baxa ki ji haushi na ba"
Meenah ta xaune nn gabanta tace "ke bani in sha, ae nima duk
duniya bn jin Akwae wnda na tsana irinsa, amma ina kuka hadu
da shi to har kika yrda kika auresa, ae da na ganki kafin lkcn bikin
da na baki shawaran kar ki auresa don...." Ashnaah ta fashe da
kukan takaici ta shiga ba ma Meenah lbrin ynda Khaleel ya aureta,
har ta gama lbrin bakin Meenah a bude yake, don kanta daga
Karshe ta rufe bakin tace "ikon Allah, sae kace a film, amma shine
kike xaune har Yau a gidan sa baki san ynda kika yi kika fidda
kanki ba" Meenah ta girgixa Kai da mugun mamaki tace "kan bu,
amma naga kkrin ki ae in nice wllh wllh bna kwararren sati biyu a
gidan ka, ka hada ni da abbana ka raba ni da momyna, kayi
sanadin daina karatuna uban me xan yi gidan ka, kai har kin bn
haushi wllh, wayyo ina ma ni ce" Ashnaah ta dan marairaice tace
"to bn san ya xan yi ba Meenah, bbu irin fitsarar da bana masa
amma sae dae ma ya nakada min shegen duka" Meenah ta xaro
ido tace "duka? Kika tsaya yake dukan ki, amma ke bnxa ce wllh"
Ashnaah tace "to ae ba iya ramawa xan yi ba baki ganin ynda
yake ne, Kinga wani lkcn ma da yunwa yake bari na fa wllh, ynxu
ki tafi kitchen ki ga a kulle yake tun safe yar shinkafa na bada
kudin a siyo min" ta karashe mgnr kmr xata yi kuka, a hnkli
Meenah tace "amma dae tsaya, baki basa kan ki ba dae koh"
Ashnaah tace "sae kace ina hauka tabdi" Meenah tace "to
alhmdllh, amma dae meye to na kishi da kika ji ya ce xae aure
Zeenat har da wani daukan nmbr babanta" Ashnaah tace "kishi
kuma, ae so nake in gaya ma Baban Zeenat din shine ya dauke
masu yar su don su hukunta shi" Meenah ta fashe da dariya tace
"kuma fa hka ne, to ynxu kin kirasa din ne, Ashnaah tace " ina
naga wayar kiran, ae bani da waya, ki ara min naki ynxu in kira"
Meenah ta xaro ido tace "baki san xa a iya ganowa ba, kuma
gashi Zeenat din tasan nmbr na" Ashnaah tace "to ina da dubu
takwas in baki ki siyo min waya karama sae a sa Min sim, ae
kudin xae isa ko" Meenah tace "to mu tafi tare mana" Ashnaah ta
xaro ido tace "ae ya gaya ma masu gadin kar su bar ni in fita, da
ana bari na in fita da tuni na gudu na kara gaba ae" Meenah ta
fashe da dariya, Ashnaah tace "bari in dauko kudin" meenat tace
"to amma ba ynxu xae dawo ba dae ko, kar ya xo ya sameni in
shiga uku" Ashnaah tayi dariya tace "ae sae dare yake dawowa
gantalallen"
Chapter 24 · 0% Book details