← Book details Dr Khaleed Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 91

Sashe 21

Dr Khaleed Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

~Dr Khaleel~ By Khaleesat Haiydar
34.....
Biyar da kusan rabi Khaleel yyi parking a compound din su
Meenah ya fito yana kallon agogon hannunsa ya nufi cikin gidan,
Ashnaah tayi tsaki ta bude motar ta fito ta kulle snn ta bi bayan
sa, bbu kowa falon ya haura sama, ita kuma ta samu kujera ta
xauna, tana karema falon kallo, ko ina tsaf sae kamshi ke tashi, ba
a dau lkci ba Anty fiddausi smll mum dinsa ta sauko dauke da
murmushi a fuskarta ta karaso cikin falon tana ma Ashnaah sannu
da xuwa, Ashnaah ta dan sunkuyar da kanta ta sauka kasa da
ladabi ta gaisheta, hkn ba karamin mamaki ya ba anty ba, ta
amsa da fara'arta tana tambayarta ya gidan, Meenah ce ta sauko
kasa Momynta tace ta dauko ma Ashnaah drinks ta nufi kitchen
sae ga ta ta dawo da faranti ta dire gaban Ashnaah tayi gaba
abunta, Ashnaah ta bi ta da harara, Khaleel ne ya sauko daga
sama ya xauna gefen smll mum din tasa yace "sannu Momy na"
ta hararesa tace "me kke min a sama" yyi murmushin da ya
bayyana dimples dinsa da fararen hakoransa yace "nothin mum
kallo na tsaya yi a bedroom din ki" Satan kallonsa kawae Ashnaah
take, ya daga kai ya kalleta ta dauke kanta da sauri tayi kmr kallo
take, ya Mike ya nufi fridge ya bude ya dauko ruwa ya dawo falon
ya xauna, hira suke tayi da mum din tasa ita dae Ashnaah mayar
da hnklinta tayi kan program din da ake a TV, momy tace "xa ku
jirani Khaleel xan dan fita in dawo ynxu" yace "its almost magrib
fa mum ina xa ki" tace "eh nasani ba dde wa xan yi ba, gidan
Hafsa xan tafi" yace "OK xa mu jira ki, ki gaida min ita don Allah
in kin je" ta hararesa tace "wato ita ce ka raina baxa ka gidan ta
ba ko kana ganin kan ku daya" Khaleel yyi dariya yace "not so
wllh mum, xan je in Allah ya yrda" sama ta nufa ta dauko makullin
motarta da mayafi tace ma Ashnaah sae ta dawo ba dde wa xata
yi ba snn ta fita don xuwa gidan kanwarta. Khaleel ya Ciro
wayarsa yyi dialing nmbr Zeenat yace "mu hadu garden mu yi
mgna Zeenat" katse kiran yyi ya mike ya fita daga falon Ashnaah
ta bi sa da kallo snn ta ja dogon tsaki ta tabe baki, Zeenat ta
sauko sanye da wani material dinta me kyau ja da milk colour ta
yafa mayafi milk colour, tun xuwan su gidan bata sakko ba sae
lkcn, ta dan yi murmushi tana kallon Ashnaah tace "Sannun ku da
xuwa" Ashnaah ta galla mata harara tace "ke dae xan ma sannu
da xuwa, gun ki na xo xa ki wani ce min sannu da xuwa" Zeenat
bata ce komae ba ta nufi kofa a sanyaye ta fita, bayan kmr minti
goma da fitan ta sae ga Meenah ta sauko ta nufi kitchen da sauri,
Ashnaah ta bi ta da kallo snn tayi tsaki, duk ta tsane su gaba
daya, abinda ta ji Khaleel ya ce a waya ya dawo mata da sauri,
wae sauko muyi mgna, to wacce mgnan xa su yi, da sauri ta
mike a xuciyarta tace "Ae sae na ji wllh wllh" ta nufi kofa da sauri
ta bude ta dan leka tsakar gidan ta ga ba kowa, hkn yasa ta fito a
hankali ta durkushe a balconyn da sauri don kar a ganta ta shiga
tunanin ta inda xata gansu a gidan, a dudduke ta fito daga
balconyn ta nufi inda take tunanin kila xata gansu duk da bata san
kan gidan ba, tafiya take kmr munafuka tana duddukawa, duk inda
taga alamar hanya ne saka kafarta kawae take, tayi mmkin girman
gidan kmr gidan su Khaleel, can ta hangosu xaune tsakiyar flowers
kmr xae shige jikinta, ta sauke ajiyar xuciya, alhmdllh har ta shigo
garden din knn ta fadi a xuciyarta, Ta duka ssae don kar su ganta
ta shiga bin bayan flowers din da ya kewaye garden din har ta iso
bayan wata flower inda ta tabbatar xata dinga jin abinda suke
cewa ssae, ta duka da sauri ta ji sun yi karo da abu kmr mutum
ssae ta tsorata har ta wage baki xata saka ihu ta ga Meenah ce,
Meenah ta rufe bakin ta da sauri ita ma a tsorace alamar
Ashnaahn tayi shiru, shiru Ashnaah tayi tana kallonta, sae kuma ta
juya tana kallonsu Khaleel, yana xaune dab da ita yana facing
dinta kan kujera, ita kam sae wani sunkuyar da kai take, Ashnaah
ta ji Khaleel yace "kin yi shiru Zeenat" sae ga hawaye a fuskarta a
hankali tace "ya Khaleel ni bna son komawa gida ynxu, nasan ina
komawa Abbana ba tausayina xae ji ba dole sae ya hadani da
Umar I knw" Khaleel yyi shiru yana kallonta snn yace "ba xae yi
hka ba Zeenat xae ji tsoron a sake rasa ki, wata daya Ae ba wasa
bace duk sun yi nadama na tabbatar maki, ni ynxu mum din ki
kawae nake ji ma kince tana da hawan jini" Da sauri Zeenat tace
"xan iya kiranta ko ynxu ne in mata bayanin komae I knw she wil b
very happy hearin frm me after a long tym" Khaleel ya dan yi
murmushi yana shafa sajensa yace "kar ki kirata tukun, ynxu dae
ki ban digit din dad dinki I knw wat 2 do" tayi shiru tana kallonsa
a dan tsorace, wani Sabon hawaye ne ya shiga bin kuncinta ya
dago kanta da sauri yace "wae kukan me kike Zeenat" sunkuyar
da kanta tayi da sauri, a hankali tace "bana son rabuwa da kai ya
Khaleel" shiru yyi yana kallonta, ya dago kanta yana murmushi ya
rungumota jikinsa yace "kar ki damu Zeenat we re still togeda bbu
abinda xae raba mu" shiru tayi bata ce komae ba ya shiga share
mata hawayen fuskarta da mayafin jikinta snn yace "to ban digit
din dad" Ashnaah da ke ta wani xufa kmr me jin xafi ta juya tana
kallon Meenah dake ta tabe baki tana kallonsu, a hankali tace"kin
fito da wayar ki don Allah" murya can kasa Meenah tace "me xa
kiyi da shi" Ashnaah tace "plss ki ban" Meenah ta bude pattern
din wayar ta snn ta mika ma Ashnaah, dae dae lkcn da Zeenat ta
shiga kira ma Khaleel nmbr dad dinta yana sa wa a wayarsa,
Ashnaah ma ta shiga kwashewa da sauri da sauri, har Zeenat ta
gama snn tana kallon Khaleel a hankali tace "watch ur wordz dear,
kar kuma ka nuna masa kai ka daukeni don abun baxae mana
kyau ba" Ashnaah ta mike da sauri ta na kallon Meenah tace "tashi
mu je" Meenah ta jawo murya kasa kasa tace "ki jira su tashi
mana sae mu bi ta kitchen" ba musu Ashnaah ta koma ta xaune
kan carpet grass din, Khaleel ya mike yana kallon Zeenat yace
"tashi mu shiga kafin mum ta dawo its almost magrib" Zeenat ta
mike ya kama hannunta suka nufi cikin gida ta front yrd, mikewa
Meenah tayi da sauri tace "kin dae iya gudu ko" Ashnaah ta Mike
tace "eh" snn suka nufi cikin gida ta kofar kitchen da gudu kar su
Riga su shiga, sama suka nufa da gudu Meenah ta bude dakinta
suka shige suna mayar da numfashi.
Chapter 21 · 0% Book details