← Book details Dr Khaleed Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 91

Sashe 33

Dr Khaleed Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

~Dr Khaleel~ By Khaleesat Haiydar50....Mikewa Khaleel yyi ya bude baki da mmki yana kallonta, rasa ma me xae ce mata yyi, to wae ita wnn wace irin mutum ce, tambayar da yyi ma kansaknn a xuciyarsa yana ci gaba da kallonta, ta galla masa harara tace "to wae sbda kayi bako sae in ta tsayawa da yunwa baxan nemi abinda xan sa a cikina ba" Najeeb ya fashe da dariya har da kyakyatawa, a fusace Khaleel yyi kanta kan tayi tunanin gudu har ya kamata ya kuma komawa sama da ita ya bude dakinsa ya tura ta ciki da karfi snn ya kulle dakin ya jingina jikin bango ya dafe kansa, yana tunanin shi kam me xae ma yarinyar nnya ji ddi bnda Wanda yyi niyyar mata da, yana ji tanarusa kuka tana bubbuga kofar ya juya ya sauka kasa, Najeeb yace "haba doctor, ka barta tayi harkangabanta mana, me ta tsare maka a nn, ko kuma in ce me ta tsare mana" kallon bnxa kawae Khaleel ke masa, can ya ja tsaki yace "look, idan bbu takamaiman abinda ya kawo ka ka tashi ka bar min gidana in tafi in kwanta pls" Najeeb ya hade rai yace"ka ga fa wlkncin ka ke hadani da kai wllh, is there anything wrong with my coming here? Sae in tashi in bar maka gidan ka malam" Khaleel ya dan yi murmushi yyi kwanciyarsa kan 2sitter din da yake xaune yace "to Allah ya baka hkuri" Najeeb yace "to ynxu dae wnn ita ce yarinyar da ka aura" Khaleel yace "yeah" Najeeb ya dan yi shiru snn yace "kayi ynda nace maka?" mikewa Khaleel yyi da sauri ya xauna yana kallonsa yace "look ni fa bbu abinda xanbari ya shiga tsakaninmu, ni dae nasan I only romance her once or twice, ta min yarinya da yawa nd beside wahalar da kaina kawae xan yi, in ma ka ga nayi sha'awarta to I saw half naked ne amma hka kawae bata bn sha'awa, ka bar big gals irinsu Ameesha da sauransu" Najeeb ya dan shafa gemunsa yace "to ka saketa Khaleel, stop wasting ur tym wllh" Khaleel yace "dats d lst thing I wil do onearth a ynxu dae" Najeeb bae kuma cewa komae basae tsakin da yyi. Karfe sha biyu da rabi Najeeb ya bar gidan, Khaleel ya rakasa har gun motarsa snn ya dawo ya nufi dakinsa ya bude ya tura a hnkli ya shiga, kwance ya sameta kan 3sitter ta juya baya a falo, ya karasa kusa da ita a hnkli ya duka yana lekan fuskarta don duk a tunanin sa bacci take, ido hudu suka yi ya koma baya da sauri ta mike xaune fuskarta a daure tace "meye kke wani lekana" daukekai yyi ya nufi kofar falon ya bude yana nuna mata waje yace "xo ki fita" mikewa tayi ta fice daga dakin kmr xata tashi sama ya bita da kallo har ta sauka kasa snn ya dan yi murmushi ya kulle dakinsa. Washegari Ashnaah na kitchen da rana tana girka shinkafa da miyar da xata ci, sae gunguni take ita daya a kitchen kmr xata yi kuka tana cewa ni dae nagaji da wnn wahalan yaushe rabon mutum da ya ci nama kullum abinci lami to Allah ya Isar min tunda ba hka ake yi a gidan mu ba naga, jin an bude kofar falon yasa tayi shiru tana sauraro taji wnda xae shigo, shirun da taji yasa ta dan leka falo taga Meenah tsaye, da sauri ta fito tana washe baki tace"lahh ashe ke ce Meenah sannu da xuwa" Meenah tace "baya nn dae koh? Don bn yrda da masu gadin nn ba" Ashnaah tayi dariya tace "baya nn wllh" Meenah ta xauna nn tsakiyar falon ta shiga bude Jakarta ta ciro kwalin wata yar karamar waya me kyau techno, da dan envelop fari karami tace "ga wayar da na siyo maki, wnn kuma maganin da kika tambaya ne gashi" Ashnaah ta galla mata harara tace "bayan har na gama period din ma, ae mutuwa kadae ne bnyi ba wllh" Meenah tace "eyya, wllh momy ce ta hanani fita, ki ce daurewa kawae kika ta yi" Ashnaah tayi dariya tace "yayanki ne yyi min allura wllh" Meenah tace "Ahh anyi abun arxiki su Khaleel" Ashnaah tayi dariya ta dauki wayar tana dubawa tace "amma yana da kyau wllh, bari in dauko nmbr mu gwada kira, kin dae sa min kudi koh" Meenah tace "ke Zeenat fa ta koma gidansu tun shekaranjiya" Ashnaah ta dafe kirji tace "ki ce wllh" Meenah tace "wllh kuwa, bn san ynda suka yi ba ni ma, duk bin kwakkwafi na ban gano komae ba wllh" Ashnaah da har jikinta yyi sanyi ta maxa tace"to ae bae baci ba, still sae na kirasa wllh, ae baxae san khaleed din ne ya sace yar sa ba" Meenah ta fashe da dariya tace "ke khaleel sunansa ba khaleed ba" Ashnaah tace "ayyo" bell suka ji an danna duk suka mike a tsorace lkci daya tace"waye?" Murya masu gadi taji, Ashnaah tace "ya aka yi?" Suka ce kaya ne oga yace a shigo da, Meenah tace "ya dawo ne" suka ce "ehh" sama ta nufa da gudu har tana faduwa, Ashnaah ta dauki wayarta da sauri ita ma ta nufi sama don ta boye, sae da ta boye snn ta sauko ta bude masu kofar ta ga akwatuna hudu a bakin kofar, dae dae lkcn da Khaleel ya karaso balconyn yace "ku shiga da su mana" waje ta basu suka shiga da akwatunan tana binsu da kallo, Khaleel ma ya shigo falon yana bin ko ina da kallo yace "me ke konewa hka" da gudu Ashnaah ta nufi kitchen tana cewa "innalillahi wa inna ilai hi raji'un" ya bi ta a baya da sauri, tana shiga kitchen din ta fasa wani ihu bayan ta sauke miyar ta durkushe kasa da sauri tana ci gaba da ihun, ba karamin tsorata shi tayi ba ya durkushe gabanta ya dagota duk a tunanin sa abu ne ya shiga idonta, a rude yake tambayarta "menene?" Kin bari ya daga fuskarta tayi, yace "wait don Allah ki gaya min me ya shiga idon" da kyar ta bari ya daga kanta,yana kallon idonta da ko digon hawaye bbu yace "to me ya shiga idon" kmr xata yi kuka tace "miyar da na sha wahala nayi ya kone"
Chapter 33 · 0% Book details