← Book details Dr Khaleed Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 91

Sashe 34

Dr Khaleed Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

~Dr Khaleel~ By Khaleesat Haiydar
51.....
Kallonta kawae Khaleel ya tsaya yi, ta xame jikinta daga rikon da yyi mata ta shiga komawa baya a hankali tana hararansa, mikewa yyi a fusace yyi ball da ita ya fice daga kitchen din, dariya ta saki har da kyakyatawa tana bin sa da kallo snn ta mike, sae kuma ta ja tsaki ita ma ta fice daga kitchen din, falo ta same sa yana kwantar da akwatunan da masu gadin suka ajiye cikin falon, ta karaso cikin falon tana kallon akwatunan, ba tare da ya kalleta ba fuskarsa daure yace "gashi nn kayan fadar kishiya, ba don kin isa na maki ba sae a bisa umarnin mahaifiyata" murmushi kawae Ashnaah take har da washe hakora, ya dago yana kallonta ganin abinda take yasa ya tsaya kallonta, ta dan tabe baki tana daga kafada tace "ni na yafe, ka kara ma warce xaka aura kawae" tsawa ya daka mata yace "to ki xo ki sani nayi hkn" tace "to dolene? Nace bana so ko" ta karashe mgnr tana hararansa, ficewa yyi daga falon don xuwa gun masu gadi ya sa su kwashe akwatunan su mayar masa su cikin mota, takalma ya gani bakin kofar, da mmki yake kallonsu, can dae ya kwashe su yana kallonta yace "takalman waye wnn" da sauri fuskarta daure tace "na wa" wani irin kallo ya shiga mata lkci daya yana bin falon da kallo kmr me son gano abu, dawowa cikin falon taga yyi ya nufi sama, da gudu ta bi bayansa tana cewa "ina xaka" bae ko kalleta ba ya shiga haura stairs din, ta hau saman ita ma da gudu ta sha gabansa tana xaro ido tace "wae ina xaka" hankadeta yyi da karfi tayi baya xata fadi yyi saurin rikota kan ta kai kasa ta fado kansa, ba karamin tsorata tayi ba ta saka kuka, ya matsar da ita gefe xae wuce ta kuma shan gabansa cikin kuka tace "Allah sae ka fada min inda xa ka" a nutse yana kallonta yace "ina ruwanki," bae jira me xata ce ba ya kuma turata daga gabansa ya haura sama, dakinta taga ya bude ta fasa ihu ta kuma bin sa da gudu, da sauri ya shige dakin ya kulle ya shiga bin dakin da kallo a nutse, ido hudu suka yi da Meenah dake bayan kofar dakin kmr munafuka tana kallonsa, juyawa yyi yana kallonta da kyau yace "me ya kawo ki gidana" ta daure fuska tace "momy ce ta aiko ni gun fateema" wayarsa ta ga ya ciro, ko ba a gaya mata ba tasan momyn xae kira gashi bata ma san ta fito ba don bata gidan, da sauri tace "ni fa bbu Wanda ya aiko ni, na xo gaida fateema ne" Ashnaah ta shigo dakin tana hararansa tace "to meye don ta xo gidan nn, xaka wani...." Bata rufe baki ba taji saukan mari lafiyayye, ta dafe kuncin a gigice tana kallonsa, sum sum Meenah ta nufi kofa xata fita da sauri, ya fixgota yana mata mugun kallo snn ya shiga janta tana bin sa a baya har suka sauka downstairs, ita dae binsa kawae take bata ce komae ba don mugun tsoron Khaleel take tun da can, gate ya nufa da ita ya bude ya jefata waje, ya juya yana kallon mai gadi yace "don me xa ku dinga barin mun mutane na shigar min gida" mai gadin da tuni ya mike tsaye da ladabi yace "Ca tayi ita yar uwarka ce oga" cikin tsawa Khaleel yace "ta ina ta xama yar uwata? To daga yau kar ku sake barin ta ta shigo min gida, ban san ta ba" da sauri mai gadin yace "an gama oga" Meenah dake tsaye har lkcn wajen gate tana ma Khaleel wani matsiyacin kallo tace "Da yau ubana bae da gida ne xanyi kuka , amma ynzu kam sae dae inyi shewa, kana talaka da kai har ka isa ka gaya min gida, kasan waye ubana kuwa, u re decievin ur self with dis hel yhu cal home" tsaki ta ja tana masa wani matsiyacin kallo tace "nonsense" tana kai wa nn ta nufi titi abun ta da sauri da sauri, bin ta kawae Khaleel yyi da kallo, lkci daya ya saki murmushi yana gyada kai yace "xan yi maganin ki yarinya, sae kinyi da kin sanin sani na" kashedi ya kuma yi ma masu gadin kan kar su bari ta kuma shigo masa gida snn ya nufi balcony, xaune ya tarda Ashnaah a bakin stairs tana ta aikin rusa kuka har lkcn yana dafe da kuncinta, wani raxanannen tsawa ya daka mata yace "bar min falo na kar in taka ki" ganin bbu wasa tattare da shi yasa ta mike tana ci gaba da kukanta ta hararesa ta haura sama. Da daddare tana kwance daki taji an tura kofa ta juya tana kallon kofar ya shigo dakin rike da leda a hannunsa, kallo daya yyi mata ya ajiye ledan nn bakin kofar ya fice daga dakin, sae da ta ji ya shiga dakinsa snn ta sauko kasan dakin ta bude ledan taga abinci ne.
Chapter 34 · 0% Book details