← Book details Dr Khaleed Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 91

Sashe 65

Dr Khaleed Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

~Dr Khaleel~ By Khaleesat Haiydar
91.....
Cikin minti talatin da yan mintuna likita ya iso gidan, har lkcn Ashnaah na bacci a daki, Ashfah ta shigo dakin ta xauna gefenta ta shiga tada ta, mikewa xaune Ashnaah tayi da kyar, Ashfah ta mika mata hijab dinta tace "ga likita ya xo, Abba yace ki sakko kasa in xa ki iya" Ashnaah ta girgixa mata kai kawae don bata son mgna, Ashfah tace "to ki sa hijab bari likitan ya shigo" da taimakon Ashfah Ashnaah ta sa hijab dinta snn Ashfah ta fita don cewa likitan ya shigo, da sallama likitan ya shigo dakin Abba na biye da shi a baya, Ashnaah ta sakko da kafafuwanta kasa daga kan gadon, likitan da baxae wuce shekaru 38 ba ya karaso yana kallonta yace "sannu," sunkuyar da kanta tayi, likitan yyi shiru yana kallonta, hkn yasa ta daga kai ta kallesa, Abba dae na tsaye Kansu, "ina ke maki ciwo?" Tambayar da likitan yyi mata knn, da kyar ta iya bude baki tace "ni ma bn sani ba" likitan ya juya yana kallon, Abba yace "in baku waje ne?" Murmushi likitan yyi tare da gyada masa kai, Abba yace "OK" snn ya juya ya fita, da mugun mmki likitan ke kallonta yace "Amma an mayar da auren ku da mai gidan ki koh? I mean kuna tare da mijin ki ynxu?" Girgixa masa kai Ashnaah tayi, ya dan xaro ido yana kallonta xae yi mgna sae kuma ya fasa ya shiga fiddo da kayan aikinsa a dan 1st aid box din da ya xo da don yana son tabbatar da abinda ya gani tukun, ita dae Ashnaah sae kallonsa take, cikin mintuna da ba su wuce sha biyar ba yyi duk abinda ya kamata snn yace mata xae je lab ya dawo, falo ya samu Abba yana cin fruit salad, ya karaso cikin falon yace "Alhaji bari in je inyi test na dawo ynxu, na dibi jininta ne" Abba yace "to amma kadda ka dau lkci Dr, I want her to get well soon don in 2dayz tym she will be wedded" likitan yace "in sha Allah" Bayan minti talatin likitan ya dawo gidan, A balcony ya samu Abba yana waya, Abba ya katse wayar yana kallon likitan yace "me sakamakon ya bada" likitan da duk ya daburce yace "bari dae ina xuwa Alhaji" cikin gidan ya nufa ya haura sama, da sallamarsa ya shiga dakin ya sameta ta dukunkune cikin bargo ta rufe har kanta, su Ashfah da Salma duk suna dakin suna gwada ankon da aka fidda na bikin Ashnaah da xa ayi jibi an karbo masu daga gun tela, Ashnaah na jin an shigo dakin ta bude kanta a hnkli, ganin likita ne yasa ta Mike xaune, kallon su Ashfah ya tsaya yi sae kuma yace "xa ku dan ba mu waje yan Mata" duk suka fita daga dakin, ya karaso ciki yana kallon Ashnaah ya ja stool din gaban madubi ya xauna har lkcin bae daina kallonta ba yace "Me yasa kika xabi lalata rayuwarki ki ba iyayenki kunya Fateema" Ashnaah ta daga Kai da mmkin jin furucinsa tana kallonsa, ya girgixa kai yace "kin ce min ba a mayar da auren ku ba, na kuma ji dad din ki na cewa jibi ne auren ki, sae ga shi sakamakon gwajin da nayi maki ya nuna kina dauke da cikin sati biyu da kwana shidda, hw is dat?" Ashnaah da komae nata ya tsaya ta gwalalo ido a mugun tsorace tana kallonsa, lkci daya abinda ya faru tsakaninta da Khaleel ya fado mata, a rude tace "Ni doctor" ya ajiye mata result din test din gabanta yace "yes! Check for ur self" Ashnaah ta daura hannu a ka cikin tashin hnkli tace "wayyoo Nashiga uku na lalace ciki kuma Doctor" wani matsanancin kuka ta fashe da ta sakko da sauri don kawae ji tayi karfi ya xo mata ta durkushe gabansa cikin kuka tace "don Allah don Annabi don darajan iyayen ka kayi min rai ka rufa min asiri doctor ka taimaka min" kuka ssae take a gigice, likitan ya girgixa kai yace "taya xan taimaka maki a nn fateema, ynxu dae who is responsible" Ashnaah ta kuma fashewa da wani sabon kuka ta ma rasa me xata ce masa shknn Khaleel ya cuceta ya kai ta ya baro ta, ita kam tasan bata da sa'a a rayuwa, likitan dae sae kallonta yake yana jiran amsa, cikin kuka tace "doctor mijina ne wllh, ni bn taba iskanci da kowa ba" likitan yace "wani mijin kuma, kin kuma aure ne" rasa abun cewa Ashnaah tayi sae kuka take ssae, shi dae sae kallonta yake, can dae ta gaji ta tsaida kukan tace "doctor ka tausaya ma rayuwata ka cire min cikin nn kashe ni wllh Abba xae yi, help me plss" likitan ya mike yana girgixa kai yace "of course bna hka, ynxu dole in kai ma dad din ki result din don abinda yake jira knn, I was called to check on wats wrong with yhu, xuwa xan yi ince bbu komae?" Ashnaah ta fashe da kuka ta tsaya gabansa a rikice tace "wayyo doctor help me plss kasheni xae yi kace masa malaria ne plss" likitan ya dan yi murmushi yace "its nt possible, a bakin aiki na fa nake kuma kudi xae biya ni sae in masa karya, to wae ma wa yyi maki cikin nn ki gaya min?" Cikin kuka Ashnaah tace "nace maka mijina ne wllh bae sakeni ba, set up aka yi masa, but no one is willin to blive dat" likitan yyi shiru duk da ba yrda yyi ba yace "meyasa xa ki amince masa batun kin san da hka," Ashnaah ta durkushe kasa tana rusa kuka tace "he forced me wllh" Likitan ya sauke ajiyar xuciya snn yace "amma kinsan dole in kai result din nn dae ko" shiru Ashnaah tayi tana hawaye, likitan yace "shknn let me c if I can cool ur dad down nd explain thingz to him, don dole in kai masa sakamako ya gani" kasa cewa komae Ashnaah tayi, duk jikinta yyi sanyi ta ji kmr Yau ce ranan mutuwarta, likitan yace "ki kwantar da hnklin ki xan yi kkrin ganin na nuna masa mijin naki bae sake ki ba as u said" yana kai wa nn ya juya ya fice daga dakin, Ashnaah ta Mike da kyar tana hawaye ta shiga tunanin abun yi hnklinta a tashe don tasan ko ruwan sanyi xae xama baxae taba convincing Abba ba, Likitan na shiga falon Abba ya samesa yana kallon news, momy kuma na xuba masa abinci kan centre table, Abba na kallon likitan yace "me sakamakon ya nuna doctor, har ka gama treatin din nata ne" likitan ya sauke ajiyar xuciya yace "Sorry to say Alhaji sakamako ya nuna yar ka na dauke da juna biyu na sati biyu da kwana shidda" mikewa Abba yyi tsaye da sauri ya saki remote din hannunsa ya xare glass din idonsa da karfi yace "wat?" Momy kam sake ruwan glass din hannunta tayi ba tare da ta sani ba, likitan na gyada kai yace "hka sakamakon gwajin da nayi Mata ya nuna Alhaji In'sha Allah"
Chapter 65 · 0% Book details