← Book details Dr Khaleed Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 87 OF 91

Sashe 87

Dr Khaleed Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

~Dr Khaleel~ By Khaleesat Haiydar116.......Ashfah ta kusa awa daya a xaune gefen yaran tayi tagumi tana kallonsu, mikewa tayi a hnkli daga karshe ganin sun fara bacci, ta gyara masu kwanciya snn ta cire kayan jikinta ta canxa xuwa gown na bacci, ledan da ya ajiye mata ta dauka ta bude fridge ta ajiye, snn ta dauki hijab ta sa tayi kwanciyarta gefen yaran. Can cikin dare Sultan me sunan Abbansu Ashfah ya farka ya fara kuka, lkci daya ya tada dan uwansa Sudais me sunan dad, suka hadu suka dinga kuka, Khaleel na xaune kan darduma ya idar da sllhn Nafila ya ji kukansu, sun fi minti goma suna kukan, Khaleel ya mike jin kukan nasu sae karuwa yake yana kallon agogo ya ga Karfe biyu saura, kofa ya nufa ya bude ya fita ya nufi dakin Ashfah, ya dde tsaye bakin kofar daga karshe yyi sallama yana tsaye bae shiga ba, sallama ya kuma yi, jin bata amsa ba yasa ya tura kofar a hnkli ya shiga dakin, ga mmkinsa kwance yasameta tana bacci ga yaran gefenta sae rusa kuka suke har da shure shure, kasa daina kallonta yyi yana ganin ta kmr Ashnaahr sa gashi exactly irin kwanciyar Ashnaah tayi, ya karaso gadon a sanyayeba tare da ya san lkcn da yyi hkn ba har lkcn idonsa a kanta, hawaye ne suka cika idonsa lkci daya xuciyarsa ta raya masa ba fa fateemarsa bace wnn wata ce daban kawae kama suka yi, juyawa yyi da sauri hawaye na sakko masa ya nufi kofa xae fita jinkukan yaransa ya sa ya dakata a bakin kofar ya juyaa hnkli yana kallonsu, share fuskarsa yyi ya karasa gadon ya dauki sultan dake kusa da ita, sae a snn Ashfah ta farka a dan firgice ta mike xaune da sauri tana gyara hijab dinta ta koma baya tana mitsika ido, Khaleel dae bae ce mata komae ba ya dauki duk yaran yana lallashinsu, Ashfah tayi mmkin irin baccin da tayi don rabonta da bacci irin hka tun kafin Abba yace xae hadata da Khaleel, kullum cikindare bata da aiki sae na kuka da tunane tunane, mikewa tayi da sauri ba tare da ta kallesa ba tace"in hada masu madara ne?" Shi ma bae kalleta ba yace "eh" ta fita da sauri daga dakin ta shiga neman kitchen don samo ruwan xafi, Eva water ta daura a gas ya dan yi xafi snn ta dawo dakin ta shiga hada masu madaran cikin feedern su, tana gamawa ta mika masa daya feedern tace "kawo dayan in basa" ya mika mata sudais ta karbe shi ta xauna gefen gadon ta shiga basa feedern, Khaleel kam bae xauna ba daga tsayen da yake ya shiga ba Sultan dake rungume jikinsa, lkci daya yaran suka koma bacci, Ashfah ta kwantar da Sudais da ke hannunta a hnkli, shi ma ya kwantar da Sultan gefen Sudais ba tare da ya kalleta ba yyi mata sae da safe ya fita.Washegari da safe Ashfah ta rasa ta ynda xa tayi ma yaran wanka, ga dae ruwan xafi ta sirka a bayi amma bata san ta ina xa ta fara wankan ba don gunMomyn Meenah yaran suke tun suna jarirai, ta fito daga bayin a sanyaye ta xauna gefen gado tana kallon yaran da ke ta wasa abunsu, a hnkli ta shiga cire masu kayan jikinsu gaba daya har ta gama snn ta dauki Sultan ta nufi bayin da shi tana kallon ruwan dake sirke cikin bahon wankansu kmr xata yi kuka, ga sabulu da soso ta ajiye gefe, Muryar Khaleel ta ji a bayanta ta juya da sauri ta rungume yaron a jikinta don har lkcn nyt gown ne jikinta, ya kauda kai yace "xa ki iya masu wankan ne" ta juya masa baya tayi shiru, a hnkli tace "ni ban iya ba" yace "OK kawo in masu" juyawa tayi ta mika masa yaron hannunta ta fice da sauri ta je ta sa hijab dinta, shi yyi masu wankan gaba daya ya shirya su, ita kuma ta hada masu abincin su ya ba daya ita mata ba daya. Hka Ashfah ta wuni ranan daga ita sae twins a daki gashi basu da rigima ko kadan sae in sun ji yunwa, Rukayya ce ta kawo masu abinci throughout ranan, Khaleel kam na dakinsa tun bayan da ya taimaka ma Ashfah ya shirya yaran bae kuma fitowa ba yana aikinsa da ya saba kullum na tunanin Ashnaah, bbu ranan Allahn da baxae wuce ba da baxae bata awa biyu xuwa uku cikin lkcn sa ba yana tunanin irin rayuwar da suka yi tun daga farkon haduwarsu da Ashnaah har xuwa rananda xata bar duniya, hkn kan sa shi kwalla ba kadan ba, kullum Addu'arsa bae wuce na Allah ya rahama mata ba ya bata gidan aljanna, Da daddare Rukayyana komawa gida bayan ta taimaka ma Ashfah ta yi ma yaran wanka Khaleel ya shigo dakin da sallama ya tsaya daga bakin kofa yace "bbu matsala ko?" Ashfah ta gyada masa kai ya juya ya fita tare da yi mata sae da safe ya rufe masu kofar.Satin Ashfah biyu knn gidan Khaleel amma ko gaisuwa baya hadata da shi in ka ga sun yi magana to ya shigo daki taimaka mata ya basu abinci in ya jisun hade mata kae suna kuka ne ko kuma ya taimaka mata ya wankesu da safe don sun ma daina tashi cikin dare in har suka koshi da daddare, shknn iyakar abinda ke hadasu knn, kwata kwata ya daina yini a gida ynxu, ita dae bata san inda yake xuwa ba amma da Karfe shidda yyi xae dawo gida da yan kayan ciye ciye ya ajiye mata, tuni ta fara girki a gidan kuma duk girkin da xata yi xata xuba masa nasa ta ajiye kan dinnin kuma yana ci ba laifi idan ya dawo, wani lkcn yace mata "thank yhu" in yashigo taimaka mata da twinz, ita dae bata cewa komae. Yau da daddare Ashfah na gama shirya su sultan da daddare ta basu abincin su suka yi bacci lkci daya ta kwantar da su, ynxu kam ta fara sabawada iya rainansu ita kadae ba sae an taimaketa ba, sae dae tana shan wahala ssae don rainon yan biyu ba abu me sauki bane da daya ya fara kuka daya zae amshe ko wasa yake su hadu suyi tayi duk su rikitata wataran ma ita ma ta sa masu kukan, ssae take son yaran kmr xata hadiyesu, tana kwantar da su ita ma ta kwanta nn da nn bacci ya dauketa, can cikin dare suka tashi gaba daya suka fara kuka, ta mike xaune da kyar tana kallonsu don da wuya ka ga sun tashi cikin dare ynxu gashi ba su barta tayi baccin rana ba ranan, kan fridge ta nufa ta dauko Goran ruwansu don tasan ba yunwa a tare da su saedae kila kishin ruwa amma kmr ta kuma sa su kuka da ta basu ruwan, ta shiga hada masu madara da sauri, ta daukesu a tare tana basu nn ma suka ki karba kmr sun hada baki, sae kuka suke, ita ma ta fashe da kuka tana kallonsu tace "toh me ku ke so?" Tura kofar da taji anyi tare da sallama yasa ta dauki hijab dinta da sauri ta sa, ya karaso cikin dakin yanakallon twins din ya duka ya dauki sultan snn Sudais duk ya rungumesu yana lallashi, jin basu yi shiru ba yasa ya xauna gefen gadon ya dauki feeder yana basu, nn ma dae ba su wani karba ba, ya gane to kila basu da lfya ne, yan dubaru yyi masu ya basu magunguna, yana ta lallaba su har dae ya samu duksuka koma bacci, daya a kafarsa, yana rungume da daya kuma, juyawa yyi yana kallon Ashfah ya ganta xaune can karshen gadon wae don ya xauna gefen gadon, ta jinginar da kanta jikin gadon tana bacci daga xaunen da take, duk lkcn da ya kalleta sae gabansa yyi mugun faduwa lkci daya kuma Ashnaah ta fado masa gashi yana ddewa kafin ya daina tunaninta, meyasa xa a basa mata me kama da fateemarsa hka, juyawa yyi ya kuma kallonta jikinsa a sanyaye yace "ki kwanta" bae ga alamar ta san yana yi ba don da gani tayi nisa da baccinta, ya mike a hnkli ya nufi dakinsa da yaran gudun kar su tashi duk ya kwantar da su a dakin snn ya dawo dakin Ashfah ya kuma ce mata ta kwanta daga bakin kofar da yake tsaye amma shiru, yw fi minti biyar a tsaye snn ya karaso cikin dakin ya dan buga gado ko xata tashi nn ma bata tashi ba, but ko kadanAshnaah bata da nauyin bacci hka da ta ji motsi take farkawa, ya dan yi murmushi jikinsa a sanyaye ya dan dafata.117.....A tsorace Ashfah ta farka tana kkrin mikewa ya koma baya da sauri yace "No nace ki kwanta ne" mikewa tsaye tayi ta koma jikin gado kanta a kasa, ya juya da sauri ya nufi kofar xae fita, da sauri tace"yaran fa" ganin bata gansu kan gadon ba, ba tare daya kalleta ba yace "suna daki na" yana kai wa nn ya kulle mata kofarta. Washegari Ashfah ta gama shirin ta da safe ta gyara dakin ta snn ta sauka downstairs don hada break fst, ko da ta gama har tara yyi, ta haura sama don komawa dakinta taji kukan su sultan, kasa shiga dakinta tayi ta tsaya bakin kofa, don da taji kukansu hnklinta ke tashi ta rasa sukuni barin ynxu da tasan ba su ci abinci ba tun wayewar gari, can dae ta gaji da tsayuwa ta shiga dakinta, ta fi minti biyar da shiga amma har lkcn sae karuwa kukansu yake, ta kasa daurewa ta mike kmr xata yi kuka ta fita da sauri ta nufi dakin, tana shiga dai dai lkcn da Khaleel ke fitowa daga wanka knn daure towel a waist, da sauri ta juya masa baya a mugun tsorace sae kuma ta nufi kofa ta fice daga dakin da sauri har tana tuntube, Khaleelya dauki yaran yana lallashinsu har suka yi shiru snn ya xaunar da su tunda sun fara iyawa ynxu cikinkekunansu da fanz suka kawo masu as gift ranan da aka rada masu
Chapter 87 · 0% Book details