← Book details Dr Khaleed Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 91

Sashe 77

Dr Khaleed Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

104.....
Mikewa yyi jikinsa a mace ganin har lkcn aman bae tsaya mata ba ya nufi bathroom din, dukawa yyi ya dafata ta turasa da sauri alamar ya kyaleta, komawa gefe yyi yana kallonta har ta gama ta mike ta wanke bakinta da mouth freshner ta fice ta bar masa aman a gurin. Gyara gurin ya shiga yi har ya gama snn ya hada ruwan wanka ko xae ji karfi a jikinsa, bakinsa ya soma wankewa snn yyi wanka ya fito daure da towel a waist dinsa, xaune ya sameta ta jingina jikin gado, suna hada ido ta dauke kanta da sauri don tun da suke bae taba fitowa hka daga wanka gabanta ba, kwanciya tayi ta shige cikin bargo ta rufe har kanta, ya gama sa sleepn robe dinsa yana kallon empty kwalaban da ta ajiye masa gefen fridge, dauke kai yyi da sauri don ko ganinsu bae son yi, agogo ya kalla yaga biyu saura, ya kashe wutan dakin ya kwanta yana kallonta, a hnkli ya birgina inda take ya cire bargon jikinta gaba daya, ta shiga turasa alamar ya rabu da ita, ya rungumeta a hnkli yace "Haba bbyna, am so srry plss" kuka ta sakar masa ya shiga lallashinta ta gaji don kanta tayi shiru, a sanyaye yace "wllh bana kara shan any Alcoholic drink wife, kin ma ga ya fitar min a kai ynxu, da na sha xan yi amae" shiru tayi bata ce masa komae ba, shi ma bae kuma cewa komae ba duk jikinsa yyi sanyi, a hnkli ta xame jikinta daga nashi ta juya masa baya.
Washegari karfe goma suka gama shirin komawa gida, falo Ashnaah ta samu dad xaune ta durkusa ta gaishesa snn tace xa su tafi, dad yace "da wuri hka xa ku tafi" tayi murmushi bata ce komae ba, ya mike yace "to ina xuwa" sama ya nufa dae dae stairs suka hadu da Khaleel da ke sakkowa, Khaleel bae bari sun hada ido ba ya basa hanya da sauri, a sanyaye ya karasa sakkowa downstairs yana kallon Ashnaah yace "mu tafi" tace "Abba yace in jira shi" bae ce mata komae ba ya fita falon don yasan ko ya tsaya yi masa sallama ma ba tanka sa xae yi ba tunda bae amsa gaisuwarsa daxu ba, Dad ya sakko rike da kudi ya mika ma Ashnaah yace "to gashi ki siya duk abinda kike so" kasa kin amsa tayi ta karba a kunyace tayi masa gdya ta mike yyi mata Allah ya kiyaye hanya snn ta fita don sun yi sallama da Ummi, xaune ta tarda Khaleel cikin mota yana jiranta, tana shiga motar ya tada mai gadi ya bude masa gate ya fita. Karfe sha daya saura suka isa gida, Khaleel ya juya yana kallon Ashnaah yace "ki shiga ciki wife, xan je siyo maki magunguna kafin su kare daga nn sae in siyo abinci, me kike son ci?" Ashnaah ta girgixa masa kai tace "ba komae, xan sha kunun da Ummi tayi min" kudin hannunta ta mika masa tace "ga shi Abba ya bani" yyi murmushi yace "to kin gode wife" tace "to ka karba mana" ya girgixa kai yace "ae ke ya ba ma wife ki rike kayan ki kawae" bata rae tayi har lkcn tana mika masa, yyi murmushi yace "to ki shiga sae na dawo ki ban" ba musu ta bude motar ta fita ya bi ta da kallo har ta shiga gidan, snn ya juya ya fice da motar, kwanciya Ashnaah tayi kan kujera a falo, wayarta taji yana vibrate ta bude jakar ta ciro da sauri ta ga Ashfah ce ke kiranta, daga kiran tayi Ashfah tace "sister ba ki turo address din ba kuma, ya jikin?" Ashnaah tace "lah gashi ban tambayesa ba kuma baya nn, Bari in tambayi mai gadi," da sauri ta fita ta tambayi mai gadi address din layin ya bata snn ta gaya ma yar uwartata, Ashfah tace to ga ta nn xuwa. Cikin minti ashirin Ashfah ta iso gidan, Ashnaah ta ji ddin ganinta ssae ta rungumeta tana tambayarta momynta fa, Ashfah ta ajiye ledan abincin hannunta tace "ta ce a gaishe ki" a sanyaye Ashnaah tace "Abba ya dawo?" Girgixa kai Ashfah tayi, Ashnaah tace "to inna fa" Ashfah tace "tana nn" shiru Ashnaah tayi bata ce komae ba, can ta mike tana kallon yar uwartata tace "mu tafi sama" mikewa Ashfah tayi ta bi bayanta ta kai ta dakin da take. Hira suka dinga yi har kusan karfe daya suka yi sllh, Ashnaah da kasala da tashin xuciya ya isheta tace ma yar uwarta bari ta dan kwanta don ta gaji, tana kwanciya nn da nn bacci ya dauketa. Ashfah bata xauna ba ta shiga gyara ko ina na gidan, tana kitchen tana wanke dan kwanukan da ta gani Khaleel da Najeeb suka shigo gidan, kin fitowa tayi daga kitchen din har ya suka shigo falon da mmki Khaleel ke kallon ko ina na falon, bbu abinda ke tashi sae kamshi Mae ddi, ya kalli kofar kitchen jin karan ruwa ya nufi kitchen din da sauri, daga bakin kofa ya tsaya yana kallonta da mmki ganin ynda tayi kwalliya, ko kadan bae lura ba Ashnaah ba ce don mugun kamar da suke, Ashfah taki juyowa jin bae ce komae ba ta ci gaba da wanke wankenta, karasowa cikin kitchen din yyi yana murmushi yace "waww wife duk ke kika yi wnn aikin," da sauri Ashfah ta juya ganin ya nufota xae rungumeta tace "ba ita bace" cak ya tsaya yana kallonta, ta dauke kanta tana ci gaba da dauraye plates din hannunta tace "ina yini" Khaleel ya koma baya da sauri ya fara kame kame "ohh srry sister, lfya lau, sannu da aiki, yaushe kika xo"
Chapter 77 · 0% Book details