← Book details Dr Khaleed Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 91

Sashe 67

Dr Khaleed Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

~Dr Khaleel~ By Khaleesat Haiydar
93.....
Tafiya kawae Ashnaah take ba tare da tasan inda xa ta ba gashi bata fito da kudi ba bare ta sami abun hawa ta hau, gajiya tayi ta nemi dakalin wani da shago ta xauna ta dalilin jirin da take ji ssae ga kasala, lkci daya taji xaxxabin ya dawo mata, wayar da ke hannunta ta kalla don ta ma manta ta taho da shi, nn da nn ta shiga neman layin Khaleel taji bbu kudi a wayar, dafe kanta tayi ta rasa me ke mata ddi ga wani aman da ke taso mata, gun kwanciya kawae take nema a lkcn, pls cal me ta tura masa da sauri bayan kusan minti goma ta ga bae kira ba, ta kuma tura masa ta jira still bae kira ba, ta kusa minti talatin a xaune kanta hade da gwiwanta can dae ta dago a hnkli tana tunanin abun yi, tasan ko taku daya baxa ta iya ba daga wajen faduwa kawae xata yi tsabar jirin da take ji, wasu hawaye ne su ka shiga bin kuncinta ita kam ko me yasa bata da sa'a a rayuwa, a hnkli ta shiga bin inda take da kallo tana tunanin to ko taimako xata nema don gun Akwae mutane da dama suna ta harkan gabansu, ji tayi baxata iya tashi ba kawae ta ci gaba da xamanta a gun, Sadeeq ne ya fado mata, ta dago wayar a hnkli tana kallon screen din, please cal me ta tura masa shi ma, Sadeeq dake xaune kasa falon Abba da dad dinsa ya ciro wayarsa jin alert din msge, ganin sakon yasa ya mike ya ce yana xuwa snn ya fita, kiranta yyi bugu daya Ashnaah ta daga da sauri, Sadeeq yace "ya aka yi Fateema," a sanyaye Ashnaah tace "kati xaka turo min don Allah" Sadeeq yace "me yasa kika yi abinda kika yi?" Ashnaah da hawaye ya shiga bin kuncinta tace "sbda mijina bae sake ni ba" Sadeeq ya dan yi shiru snn yace "kina ina ynxu?" A hnkli tace "gidan mijina xan je, ina son kiransa ne bni da card" Sadeeq yace "Shknn, Allah ya huci xuciyar Abban ki ya sassauta maki" kai kawae Ashnaah ta gyada masa kmr yana ganinta tana hawaye, yace "xan maki transfer ynxu" yana kai wa nn ya katse kiran, cikin minti biyu taga transfer din dari biyar ta tura masa da text din gdya, tana kkrin dailin nmbr Khaleel kiransa ya shigo, dagawa tayi bata ce komae ba, da damuwa yace "wife kiyi hkuri sae ynxu na ga text din ki, am srry I wasn't OK ne xuciyata na damuna shine nayi alluran bacci, I just woke up ynxu" kuka Ashnaah ta sakar masa, nn da nn ya rikice mata yana tambayarta me ya faru ta kasa cewa komae sae kuka, ganin ynda ya birkice ya sa a sanyaye tace "Ka kuma hada ni da parent dina hnklin ka ya kwanta, ba ka min adalci ba, sae in iya cewa ka cuce ni ma kawae, me yasa ka min hka doctor...." Kuka ne ya ci karfinta ssae, Khaleel da hnklinsa yyi mugun tashi duk da ya gano dalilin maganganun nata yace "plss ki gaya min me ya faru, kina ina ne?" Cikin kuka ssae tace "ba dole ka tambaye ni ina ina ba" kmr xae mata kuka yace "plss wife kar ki bari a cire cikin nn am beggin yhu ki tausaya min don't let dat plss, ki bari mu ga bbynmu" Ashnaah da mmki ya cika ta ta ma rasa me xa ta ce masa, wato ashe ya ma san tana da ciki knn, Shiru tayi tana naxarin magungunan da ya bata ranan har yana cewa kar ta kuma shan ko wani magani xa a bata a gida, kuka ta fashe da tace "wllh baka da imani, ka hada ni da iyayena kawae ka raba ni da su don son xuciyar ka, to bana son cikin xubar wa xanyi" kuka kawae take kmr ranta xae fita ta katse kiran, Khaleel da idanunsa suka kada suka yi ja ya dafe kansa da ke Sara masa xuciyarsa nai masa kuna. Kiranta ya kuma yi, Ashnaah da ke kuka har lkcin ta kasa kin daga kiran nasa duk da ta so yin hkn, ta dauka tayi shiru, a sanyaye yace "kiyi hkuri fateema xan cire maki cikin na maki alkawari tunda ba kya so, ynxu plss ki gaya min inda ki ke" taki cewa komae na wani dan lkci snn a hnkli ta gaya masa inda take, cikin mintunan da ba su wuce sha takwas ba Khaleel ya iso gun da ta gaya masa take, yana gama parkin ya fito ya nufi inda ya hangota da sauri ya durkusa gabanta ya kamo hannunta da damuwa yace "am vry srry wife, I caused all dis" kuka ta sakar masa, duk ya rikice yana lallashinta, ganin taki yin shiru yasa dago ta ya rungume abarsa, ta tsaida kukan da take da sauri ta kwace kanta ganin a titi suke, kama hannunta yyi tana ganin jiri har suka isa motarsa snn ya bude mata front seat ta shiga, ya xaga ya shiga shi ma ya tada motar suka bar wajen, ssae ta ba Khaleel tausayi ganin ynda ta da da ramewa da ganinta ka ga mai laulayi, ga kuma kukan da ta ci, kwantar mata da kujerar motar yyi ta kwanta, nn da nn bacci ya dauketa, gidansa ya nufa da ita, yana gama parkin ya fito ya dauki abarsa ya shiga ciki da ita, ta bude ido da sauri tace "meye hka" bedroom dinsa ya shiga da ita, ya cire bedsheet din kan gadon snn ya kwantar da ita.
94.....
Mikewa xaune tayi da sauri ta wani daure fuska don haushinsa kawae take ji, a sanyaye yace "srry na ga kina bacci ne" ta dauke kanta kawae har lkcn fuskarta a daure, mikewa yyi jiki ba kwari ya fita daga dakin ta bi sa da kallo, hawaye ne ya shiga bin kuncinta duk she is confuse fushinta xata nuna masa ko jawo mijinta xata yi jiki. Jinginar da kanta tayi jikin gadon tana tunanin rayuwarta tun daga ranan da ta fara haduwa da Khaleel, wasu hawaye masu xafi suka shiga sakko mata, tana nn a hka har bayan minti talatin ta ji an kira sllhn Azahar, mikewa tayi a hnkli don xuwa tayi alwala taji jiri ya debeta ta dafa bango da sauri kan ta kai kasa ta koma kan gadon ta xauna, kasa mikewa tayi har aka idar da sllh Khaleel ya shigo dakin, ba karamin tausayi ya bata ba yanayin da ya shigo, ya karaso gabanta ya duka ya ajiye mata ledan abincin hannunsa da plate yace "ga abinci na siyo maki ki sakko ki ci" kallonsa kawae take ya bude abincin ta ga dafa duka ne da naman kaxa, nn da nn cikinta ya hautsine aroma din abincin na bugar ta, mikewa ta shiga kkrin yi da sauri ya lura da hkn ya mike yace "me ya faru, amae kike ji" toshe bakinta tayi ta sakko daga kan gadon tayi baya xata fadi ya kamota da sauri ta durkushe kasan dakin ya bi ta har lkcn yana rike da ita ta shiga kwarara masa aman a jiki, ssae ta bashi tausayi ganin bbu komae cikinta, gashi she is too young ace tana da ciki ynxu, yana rike da ita yana mata sannu a sanyaye har ta gama ta fada jikinsa tana mayar da numfashi ya rungumeta, sun fi minti biyar a hka snn ya dago kanta a hnkli yana kallon idonta da yyi ja yace "Sannu wife" sunkuyar da kanta tayi kawae, mikewa yyi ya dauketa suka nufi bathroom, da kansa ya gyara mata jikinta bayan ya cire mata kaya, snn shima ya gyara nasa jikin ya daukota suka fito ya kwantar da ita kan gado ya lulluba ta da bargo snn ya shiga gyara dakin, ko da ya gama har tayi bacci ya xauna gefen gadon a hnkli yana kallon kyakkyawan fuskarta wani mugun shaukin sonta na fixgarsa, yasan he can't do without Fateema, daura hannunsa yyi a hnkli kan goshinta ya ji xafi ssae, ya mike ya fita xuwa kitchen ya hado Milo kawae ba madara ya dawo dakin snn ya shiga tashinta a hnkli, bude ido tayi tana kallonsa, ya dago ta yace "ki daure ki sha tea plss sae in ba ki magani, jikin ki yyi xafi" girgixa masa kai tayi da kyar tace "Amae xan yi" rungume ta yyi yace "A'a baxa ki yi ba ruwan tea ne kawae, ki rufe idon ki ki shanye ynxun nn" girgixa masa kai tayi alamar baxa ta sha ba don ta kasa mgnr ma gaba daya, ya dauko tean ya dago kanta, ta sakar masa kuka tana girgixa kai, da kyar ya lallabata tayi sip uku don bbu xafi, yyi yyi da ita amma ta ki karawa, rungumeta yyi ya shiga shafa bayanta a hnkli ganin amae take son yi, har sae da ya ga ya fada mata snn ya kwantar da ita yace yana xuwa, makullin motarsa ya dauka ya fita ya nufi pharmacy ya siyo magunguna da allurori ya dawo ya sameta tana bacci, yana cikin hada alluran wayarsa da ya ajiye gefen gadon yyi ring, ya dauko wayar yana kallon screen din ya ga Dad dinsa ne me kiran, gabansa ya fadi don har ya manta rabon da ya kirasa, 'karan wayar ya tada Ashnaah ta shiga juye juye don wani ciwo da taji cikinta ne ko mararta ne ta kasa tantance wanne ne ke mata ciwon, mikewa Khaleel yyi ya daga kiran, gabansa na ci gaba da faduwa yyi sallama a hnkli, "Maxa maxa ka xo ynxun nn ka same ni a gida duk inda kke" abinda ya ji dad dinsa ya ce knn ya katse kiran a take, Khaleel ya ajiye wayar a sanyaye ya juya yana kallon Ashnaah ya karasa kusa da ita da sauri ya dagota yace "me ya faru" ta fashe da kuka tace "wayyo Allahna ciwo yake min" da damuwa yace "ina?" Taki cewa komae sae kuka take tana yarfe hannu, allurorin da ya gama hadawa ya dauko don yi mata, da kyar ya samu yyi mata don ta basa wahala ssae, ya rungumeta yana lallashinta ta gaji da kukan tayi shiru don kanta daga karshe bacci ya dauketa.
18 mins · Khaleesat Haiydar...
Chapter 67 · 0% Book details