← Book details Dr Khaleed Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 91

Sashe 32

Dr Khaleed Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

~Dr Khaleel~ By Khaleesat Haiydar
49......
Khaleel ya kasa daina kallon Ashnaah da taki kallon
inda yake, duk da bae yi wani mmkin abinda tayi ba
yasan xata iya aikata fiye da hkn dama, da kyar ya
iya maida dubansa ga Ummi ya ga kallonsa kawae
take, ya sunkuyar da kansa, ummi tace "to tashi ka
bar min dakina" bbu musu ya mike yana kallon
Ashnaah ya fice daga dakin, sae a snn Ashnaah ta
dago kanta tana kallon ummi, kmr xata yi kuka tace
"momy dukana fa xae yi in mun koma gida wllh, ki
ce ya bar ni a nn" da mmki ummi tace "duka
kuma?" Ashnaah ta gyada mata kai, ummi ta ma
rasa me xata ce mata can dae ta mike ta fice daga
dakin, Ashnaah ta bi ta da kallo tana murmushi.
Goma saura ummi ta dawo dakin har lkcn Ashnaah
kallo take, ummi tace "tashi ki dauki hijab din ki ku
wuce gida" Ashnaah ta dan xaro ido tace "gida ynxu,
na tsamman a nn xa mu kwana ae" Khaleel ne ya
shigo dakin yana kallon Ashnaah yace "tashi mu
wuce ke nake jira" Ashnaah ta juya da sauri tana
kallon ummi kmr xata yi kuka, ummi tace "gobe xa
da safe xa ku dawo" mikewa Ashnaah tayi ta dauki
hijab dinta ta sa, tuni gabanta ya soma faduwa, tayi
ma ummi sae da safe ta fice daga dakin ya bi
bayanta. Har suka isa gida Khaleel bae ce mata
komae ba, har karkarwan sanyi ta shiga yi don tsoro
amma ko kadan hkn bae nuna a fuskarta ba, sae da
ya jira ta fito snn ya kulle motarsa ya nufi cikin
gida ta shiga jan kafarta da kyar tana bin sa a
baya, oh ko wani irin duka kuma xae mata yau, kin
shiga falon tayi ta tsaya daga bakin kofa tana
kallonsa fuskarta daure, bae ma san tana yi ba din
jira kawae yake ta shigo ya rufe kofar sa, ganin
bata shigo ba ya sa ya daga kai yana kallonta,
dauke kanta tayi da sauri still ta ki shiga falon, ya
juya ya nufi stairs kawae ya haura sama, ta kusa
minti talatin bakin kofar taki shigowa falon ga wani
mugun bacci da take ji, daga karshe dae ta gaji don
kanta tayi shahada ta shiga falon kmr xata yi kuka
ta rufe kofar ta nufi cikin falo ta xauna, har bacci
ya samo dauketa daga xaunen da take taji kmr
motsi kusa da ita ta mike tsaye a tsorace ta gansa
a gabanta ya duka, da sauri ta bar wajen ta ga
remote din dake kan kujerar da take ya dauka snn
ya mike tsaye yana kallonta yace "ni bani da lkcn ki
ynxu, i mean ban gama gather din tym dinki ba"
kashe tv dinsa ta ga yyi snn ya kashe wutan falon
ya nufi sama ta bi sa da kallo snn ta yi murmushi a
xuciyarta tace ko dae momy tace kar ka taba ni ba,
sama ta nufa xuciyarta fal murna ta bude dakinta ta
shige. Washegari da safe Khaleel ya kai ta gida gun
Ummin sa kmr ynda ta umarce shi, bbu yabo bbu
fallasa ta amsa gaisuwarsa ya juya ya fice daga
dakin, ummi na kallon Ashnaah tace "kina ji na
fateema, ki kwantar da hankalin ki, in dae har ina
Raye a doron kasa baxan taba barin Khaleel ya
walakanta ki ba, ki kyalesa yyi auren sa kar ki tada
hankalin ki kin ji" da mmkin ummi sae gani tayi
Ashnaah tayi murmushi ssae tace "to momy dama ni
bn daga hnklina ba" Da rana Khaleel ya xo tafiya da
Ashnaah gida, ko kadan bae ji ddin irin ynda
umminsa ke amsa masa gaisuwa ba, Ashnaah tayi ma
Ummi sallama ta sa hijab dinta ta bi bayan Khaleel,
yana gama parking a gida ya bude motar ya nufi
cikin gida ba tare da ya tsaya kulle wa ba ya bar ta
nn ciki. Washegari lahadi yana kwance dakinsa idonsa
lumshe kmr me bacci ya ji an danna bell, ya mike
xaune yana kallon agogo ya ga goma da kusan rabi
to waye kuma wnn, tashi yyi ya fita daga dakin don
xuwa ganin Wanda ke bakin kofar. Najeeb ne tsaye
yana kkrin kiransa, Najeeb yace "bacci kke ne"
Khaleel yace "aa na tashi tun safe" hanya ya basa
ya shigo falon snn ya shiga tambayarsa daga inda
yake, Najeeb yace "gida mana" Ashnaah ce ta fito
daga kitchen sanye da dogon rigan baccinta har kasa
pink colour me tsantsi, gashin nn nata me kyau na
daure da ribbon baki, hannunta rike da cup din tea,
Khaleel ya juya da sauri da kuma mmki yana kallonta
don bae san tana kasa ba da baxae bude kofar ba,
kallonta kawae Najeeb yake ko kiftawa baya yi, wani
irin tsawa da ya raxanata Khaleel ya daka mata ba
tare da yasan yyi hkn ba yace "me ya sauko dake
nn" tsayawa kallonsa tayi kmr wata sha sha sha don
ita dariya ma ya bata, Khaleel ya juya yana kallon
Najeeb da har lkcn bae kifta ido ba yana kallon
Ashnaah, a fusace Khaleel yyi kanta, ta fasa ihu ta
juya xata koma kitchen da gudu, ya cafkota don
tsabar tsoro hka ta sake cup din hannunta tana
kwala ihu, janyeta yyi daga wajen da sauri ganin cup
din ya tarwatse da ruwan tean ciki, bata ankara ba
taji ya dauketa kmr wata yar bby ya nufi sama da
ita, dakinta ya bude ya jefata ciki yana nuna ta da
dan yatsa yace "wllh wllh kika sauko min falo sae na
kusan fasa maki kai" bae jira me xata ce ba ya fice
daga dakin ya sauka kasa, sae a snn Najeeb ya
sauke ajiyar xuciya ya xauna, Khaleel ya hade rae ya
nufi kitchen ya dauko broom da packer don kwashe
kwalaben da ke kasan falon, sae da ya gama tidy
din wajen snn ya xauna yana kallon Najeeb yace "ya
aka yi guy any prblm" Najeeb ya sauke ajiyar xuciya
yace "wae wnn ita ce yarinyar Khaleel" Khaleel xae
yi magana ya ji muryar Ashnaah a bayan su.
Chapter 32 · 0% Book details