← Book details Dr Khaleed Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 91

Sashe 56

Dr Khaleed Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

~Dr Khaleel~ By Khaleesat Haiydar
78.....
Washegari da rana Ashnaah na fitowa daga lecture da frnds dinta ta hango motar Khaleel, dauke kai tayi da sauri, tayi kmr bata gansa ba tana ci gaba da tafiyarta kawayenta na biye da ita a baya, khaleel ya bi ta da kallo ya ga ta nufi wani cafeteria ta xauna ta ciro littafinta ta ajiye gabanta su ma duk frnds din nata suka xaxxauna, kasa fitowa yyi daga motar don ba habit dinsa bne bin mace but ya xama dole ya bi fateema, bude motarsa yyi daga karshe ya fito rike da wayarsa ya nufi cafeterian da suke xaune cikin tafiyarsa ta kasaita, da yake duk yawanci an fito daga lecture duk yan mata suka rakasa da kallo tsabar haduwarsa gashi kananan kaya ne jikinsa, ko kadan Ashnaah bata lura da ya fito ya biyota ba, don idonta na kan littafin hannunta duk da hnklinta gaba daya ba kan littafin yake ba, muryar Aisha taji tace "waow waoww kun ga wani hadadden guy, kai wllh wnn yyi ba karya" da sauri Ashnaah ta dago kai don ganin wani guy ne wnn sanin halin Aishan don da wuya ka ji ta ce namiji na da kyau kullum cikin kushe duk saurayin da ta gani take, wani mugun faduwa gaban Ashnaah yyi suna hada ido da Khaleel daga nesan da yake, yyi mata wani mugun kwarjini, bata taba tunanin Khaleel ya kai hka wajen haduwa ba, tasan dae yes he is handsome but bata yi tunanin to this extent ba don Khaleel ya hadu ne ba karya, da kyar Ashnaah ta iya dauke idonta daga kallon da take masa, hka kawae taji ranta ya baci ganin ynda yan Mata ke ta wani kallonsa, wae har da su Ummi abinda ya kuma kular da ita knn, ta sunkuyar da kanta ta hade rae ta ci gaba da kallon littafin gabanta, da kyar Khaleel ya iya karasowa inda suke don shi kansa sae ya ji wani iri ynda ake kallonsa da rana tsaka, Maryam tace "kai gun wa xae xo a nn" Ashnaah dai bata tanka su ba don ranta ya gama baci tunda tasan sun san shi ae, Khaleel ya karaso yana kirkiran murmushi yace "sannun ku ladies" duk suka amsa mashi bnda Ashnaah, kallonsa gaba daya suke da mmki don sae a lkcn suka ganesa, Ummi tace "lah ashe kai ne ina yini" ya amsa da fara'a yana tambayarta ya karatu, Aisha da ta ji kmr ta nutse kasa don kunyan Ashnaah tana sussunkuyar da kai ta gaishesa ya amsa yana mata murmushi, Haba no wonder shi yasa Ashnaah bata tanka su ba, mikewa duk suka yi sbda kunya xa su bar wajen, Khaleel yace "haba ku yi xamanku ni ba dde wa xan yi ba, I will b off soon" Aisha dae taki xama tace xata dauko abu a class ta samu ta bar wajen da sauri, Ummi da Maryam ma cikin dubara suka bar wajen, sae a snn Ashnaah ta dago kai fuskarta a daure sae taga wae duk yan matan wajen kallonsu suke, wasu na gulma, mayar da kanta tayi kan buk dinta don bata son su hada ido da Khaleel da ya kafa mata ido, a hnkli taji yace "ina yini" kasa amsa masa tayi ta dago tana kallonsa suna hada ido ta sauke idonta da sauri, taji yace "u re uncomfortable ryt?" Bata ce komae ba ta kuma kallonsa, murmushinsa mai kyau ya sakar mata murya can kasa yace "me yasa ba ki sa Nikaf ba yau" nan ma bata ce masa komae ba, bae kuma cewa komae ba har na kusan minti takwas, mikewa yyi a hnkli yana kallonta a sanyaye yace "shknn bari in tafi, seems ina damun ki koh Fateema" daga kai tayi tana kallonsa ita ma jikinta yyi sanyi, murmushi yyi mata yace "gobe xan xo" bae jira cewarta ba ya juya da sauri ya bar wajen, mikewa tayi jiki ba kwari ta dauki jakarta ta bi bayan sa, kusan a tare suka iso motarsa, ya juya yana kallonta, bata Bari sun hada ido ba ta xaga ta bude bck seat shiga, shima ya bude seat din bayan ya shiga yana kallonta, da kyar ta iya bude baki tace "ina yini" murmushi kawae yake, hkn yasa ta dago kai ta galla masa harara fuskarta daure, dariya ya shiga yi yana kallon cikin idonta, Ashnaah tayi shiru tana kallonsa a sanyaye don bata taba ganin dariyarsa ba sae wnn vry moment din, lkci daya shima ya daina Dariyar yyi shiru yana kallon cikin nata idon, murmushinta mai kyau tayi lkci daya ta sauke idonta kan long fingers dinta ta shiga wasa da su, bae taba ganin murmushinta ba shima sae wnn vry moment din, a hnkli ya matso kusa da ita ya dago kanta yana kallon kyakkyawan fuskarta, rungunmeta yyi murya can kasa yace "I love yhu wife" lumshe idonta tayi ta daura kanta kan kirjinsa tana shakar kamshinsa me ddi, kmr warce ta tuna abu kuma ta janye jikinta daga nasa tana kkrin bude mota ta fita tace "drivernmu xae xo daukana ynxu" ya rikota da sauri ya marairaice mata yace "plss ki kawo mana solution fateema am lost, nobody is willin to blive me, nt even my parent, ke kadae ce kika yrda da ni" Ashnaah ta sunkuyar da kanta don kar ya ga hawayen idonta da kyar tace "nima ba yrda dani xa ayi ba, gwara mu hkura kawae, dama ae ba son juna muke ba, so wats there don mun rabu..." kuka ta fashe da tana kallonsa, shi kam rasa ma me xae ce mata yyi, dae dae nn drivern gidansu ya iso, Ashnaah ta shiga share hawayenta da sauri ta bude motar ta fice.

~Dr Khaleel~ By Khaleesat Haiydar 79..... Ashnaah na bude dakinsu bayan ta dawo daga sch ta samu akwatunan ta gaba daya da kayayyakinta a dakin, kayan gado ne kadae bata gani ba, kasa karasawa cikin dakin tayi Ashfah da ke xaune tana ta kwafan note ta kalleta tace "har kin dawo" Ashnaah ta karaso cikin dakin a sanyaye tana ci gaba da kallon kayayyakin tace "waye ya kwaso min kayana" Ashfah tace "ni ma nn na same su" Ashnaah bata ce komae ba jiki ba kwari ta nufi kan gado tayi kwanciyarta kmr me shirin yin bacci don bata son yar uwarta ta lura da halin da ta shiga a lkcn. Har aka kira magrib Ashnaah bata shiga kitchen ba bare ta dauki abincin ta kwata kwata bata da appetite ta rasa me ke mata ddi kawae, Ashfah dae na ta harkar gabanta, da kyar ta mike ta nufi bathroom don yin alwala, tana xaune kan darduma bayan ta idar da sllh momy ta shigo dakin, tana kallonsu tace "waye ya bar min abinci har ynxu a kitchen a ajiye" Ashnaah ta mike tace "na ci abinci a sch ne momy shi yasa bn dauka ba" kallonta kawae momy ke yi, hkn yasa ta sunkuyar da kai momy ta juya ta fice daga dakin, Ashnaah ta mike ta shiga bayi don yin wanka, ana idar da isha Ashfah ts sauka downstairs ta dauko dinner dinta a kitchen ta dawo dakin, Ashnaah ta mike gudun kar momy ta kuma dawowa ita ma ta sauka kasa ta dauko nata abincin a kitchen ta fito, falo ta nufa ta gaida Abbanta dake xaune yana kallon news, bbu yabo bbu fallasa ya amsa ba tare da ya kalleta ba ta mike a sanyaye ta nufi sama rike da abincin ta, tana xaune tayi jigum ta sa abincin a gaba ta kasa ci wayarta da ke gaban madubi ya soma ring, Ashfah da ke kusa da wajen ta juya don dauko mata, da sauri ta mike har tana tuntube ta riga ta dauke wayar, Ashfah ta juya tana kallonta da mmki snn ta tabe baki ta ci gaba da abinda take, Ashnaah ta daga wayar ta kara a kunne bata ce komae ba, can tace "toh" snn ta katse kiran, hada ido suka yi da yar uwartata ta dauke Kai da sauri ita dae Ashfah bata ce komai ba, Ashnaah ta mike cikin dubara ta dauki hijab dinta ta nufi window ta bude ta jefar waje snn ta rufe windon ta nufi kofa rike da cup kmr xata debo ruwa ta fice daga dakin. Kitchen ta nufa Abba ya bi ta da kallo hkn yasa gabanta yyi mugun faduwa ta debo ruwan kawae ta fito ta koma sama ta shiga dakinsu, gefen abincinta ta ajiye ruwan snn ta xauna ta dauki spoon kmr me shirin cin abinci, ta dae jujjuya shinkafar kmr ta ci snn ta kuma mikewa bayan kmr minti biyar ta nufi kofa don kai kwanon kitchen, Satan kallon Abba kawae take har ta shige kitchen ta ga kallonsa kawae yake wnn karan. A hnkli Ashnaah ta bude kofar kitchen dinsu ta fice snn ta kullo ta nufi inda ta jefa hijab dinta ta dauka ta sa, tana waige waige ta fice daga gate. Yana jingine jikin motarsa ta karaso ba tare da ta bari sun hada ido ba tace "ga ni" yyi shiru bae ce komae ba hkn yasa ta daga kai tana kallonsa, yyi mata murmushi a sanyaye yace "tnxx 4 cumin sweetheart" bata ce komae ba ta sunkuyar da kanta, yana kallonta yace "Abba na ciki koh" kai ta gyada masa kawae, yyi shiru snn a hnkli yace "I knw yhu re taking a risk by comin out, forgive me for dat" bata ce komae ba nn ma, ya karaso kusa da ita ya marairaice yace "ina son ganin Abba plss xan iya shiga, I need to tok to him may b he will get me" ta xaro ido a tsorace tana kallonsa tace "A'a bbu ruwana" a hnkli ya dafa shoulders dinta xae yi magana aka bude gate, duk suka juya da sauri barin Ashnaah da xuciyarta ya kusa shigewa cikinta don tsoro, ido hudu tayi da Abbanta, ta fasa ihu a tsorace tana cewa "wayyo na shiga uku na lalace" lkci daya jikinta ya dau rawa.
Chapter 56 · 0% Book details