← Book details Dr Khaleed Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 91

Sashe 66

Dr Khaleed Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

~Dr Khaleel~ By Khaleesat Haiydar
92.....
Juyawa Abba yyi yana ma momy wani irin kallo har lkcn mmki bayyane a fuskarsa, kuka momy ta saki tana kallon likitan tace "ciki fa kace doctor" likitan ya mika masu takardan hannunsa snn ya kara da cewa "amma ta nuna min auransu da mijinta na nn, don hka kar kuyi saurin yanke hukunci, bincike shine abinda..." Wani kallo kawae Abba ke masa, bae Bari ya Kai aya ba yace "ka gama aikin ka yallabae, xan turo driver da kudin ka anjima, tnx 4 ur help" Ashnaah kam tun bayan fitan likitan take ta rusa kukan tashin hnkli ta rasa abun yi, tasan yau kila sae dae wata ba ita ba, duk sae ta nemi xaxxabi da kasalan da take ji ta rasa, mikewa tayi xuciyarta na bugawa ta dauki hijab din ta tasa snn ta dauki wayarta ta fice daga dakin, su Ashfah da shigowarsu knn suka shiga tambayarta lfya amma ko ta Kansu bata bi ba, sakkowa kasa tayi ba tare da ta kalli kowa na falon ba ta nufi kitchen da sauri, dai dai lkcn da Abba ke sallaman likitan sa knn fuskarsa a daure jin maganganun da yake kkrin kawo masa, juyawa Abba yyi ganinta ya daka mata wani mugun tsawa yace "ina xa ki," Ashnaah bata ko kalle inda yake ba ta shige kitchen a guje ta bude kofar da xae sada ta da garden ta fice, Abba na ganin hka ya bi ta gaban gidan da sauri shi ma, likitan ya bi bayan sa, momy kam xubewa kan kujera tayi tana kuka ssae su Ashfah suka sauko suna tambayarta lfya amma ba bakin mgna, tunda Ashnaah take bata taba irin gudun da tayi ba ranan don kan kace kwabo har ta isa gate, dai dai sanda Abba ya fito knn cikin tsawa yake ce ma mai gadinsa ya rufe masa gate kar ya bari ta fita, kuka Ashnaah ta saki ganin mai gadin ya kulle gate din ga Abba na tahowa, ta durkushe gabansa tana rusa kuka hnklinta a tashe tana cewa "don Allah don annabi kayi min rae ka bude min, kashe ni xae yi wllh" Tahowa kawae Abba yake fuskar nn tasa bbu alamar rahama idon nn nasa ya kada, hkn ya kuma tada hnklin Ashnaah ta shiga kwala ihu, tun kan Abba ya karaso mai gadin ya shiga basa hkuri duk da bae san me ke faruwa ba, amma ko kadan Abba bae Ma san yana yi ba, likitan ya sha gabansa da sauri yace "Haba Alhaji kar ka ce xaka taba ta don Allah, consider situation din da take ciki kar ka ji ma yar ka ciwo, ka kwantar da hnklinka ka saurari bayanin ta tukun" Abba ya tura likitan daga gabansa cikin tsawa yace "gwara in kasheta kawae yau in huta" Ashnaah na jin hka ta shiga gudu tana xaga gidan tana rokon Abbanta cikin kuka, tana ganin momynta ta fito ta nufeta da gudu ta tsaya bayanta tana cewa ta taimaka mata don Allah, Ashfah da tuni ita ma ta fara kuka ta nufi Abbansu ta durkushe gabansa cikin kuka take cewa "don Allah don Annabi Abbanmu kayi hkuri" cikin kuka momy tace "wllh Adam kar ka kuskura ka taba min 'ya ta da ka taba ta gwara ka Kore mu gaba daya gidan yau" Abba ya tsaya kallonta can yace "hka kika ce koh" kai tsaye momy tace "ehh hka na ce" Abba yace "fine, Ni baxan ma Fateema baki ba amma daga yau na cire ta cikin 'ya ya na, wato na yafe ta, kar ta kara tunanin tana da uba a duniya, ba ita ba gidan nn, snn idan ta kuskura ta sa kafa ta taka gidan mahaifiyata bn yafe mata ba, ta tafi duk inda xa ta bnda gidan uwata, bn haifi yar da xata ja min abun kunya a duniya ba" cikin tsawa Abba yace "ta xo ta fice min a gida" Momy tace "in har Fateema ta bar gidan nn to ni ma na bar gidan nn" Abba ya daga kafada yace "fine! Ki tafi amma a bakin auren ki" Abba na kai wa nn ya nufi cikin gida da sauri, Ashnaah ta kuma fashewa da wani matsanancin kuka tana kallon momynta tace "A'a momy kiyi hkuri,
Kar ki ce hka, amma ki yafe ni don Allah nasan tun tasowa ta na kasance warce bata jin maganarku amma momy ni ban taba bin maxa ba duk rashin ji na, ki yrda dani momy mijina bae sakeni, tun daga ranar da na ga takardan nn nasan bashi ne ya rubuta ba don ba ma shi da lfya ranan da na ga takardan, snn ya sha gaya min baxae taba saki na ba idan na bukaci hkn tun farkon aurenmu lkcn ma ba ddin xaman gidan nake ba, amma da yake na dde ina son ya sakeni shi yasa na dauka takardan kawae na dawo gida duk da raina bae so hkn ba, nasan ko min daren ddewa gskya xata bayyana kuma Abbana xae yafe min." Ashnaah tayi shiru tana kallon momynta da ke hawaye har lkcn, can ta juya ita ma tana hawayen tace "ki daina kuka momy xa mu dinga waya, amma ki taimaka min ki ba Abbana hkuri" Ashnaah na kai wa nn ta soma tafiya ta nufi gate, Ashfah ta bi ta da sauri tana kuka tace "ina xa ki sister" Ashnaah ta share hawayenta tace "gidan mijina xan koma" tana fadin hka ta bar gun da sauri ta bude gate ta fice daga gidan.
Plss sisters ku bar ni in rubuta littafina ynda na tsara, wnda ya ga littafin nn yyi masa ya karanta wnda kuma ya ga bae masa ba ya bar shi kawae, nt dat xa ayi ta min complain ace hka ya kamata in yi ba hka ya kamata in yi ba, hkn bbu ddi Sam, hka aka min lkcn littafin Ikram, gskya ni dae bna jin ddin hka.
5 mins · Khaleesat Haiydar...
Chapter 66 · 0% Book details