← Book details Dr Khaleed Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 76 OF 91

Sashe 76

Dr Khaleed Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

~Dr Khaleel~ By Khaleesat Haiydar
103.....
A hnkli Ashnaah ta daga kai a sanyaye tana kallon Khaleel da ke tsaye har lkcn, suna hada ido ya dauke kansa, Dad kam ci gaba yyi da shan fruit dinsa, Khaleel ya juya ya koma sama da ganinsa kasan jikinsa yyi sanyi, a hnkli tayi ta shan water melon din har ta kusa shanyewa bata ji ya isheta ba, dad yace "yaushe ku ka xo?" Ta daga kai tana kallonsa tace "daxu da yamma" yace "shine xa ku koma ynxu?" Shiru Ashnaah tayi bata ce komae ba, dad yace "ku bari sae da safe ku tafi" kai kawae ta gyada masa, ya dauki wayarsa ya kira driver yace ya shigo falo ya samesa, ko minti biyar ba ayi ba drivern ya shigo dad ya ciro dubu biyu ya mika masa yace "kankana masu kyau xa ka siyo mata" kunya ya kama Ashnaah don ko kadan bata lura da har ta shanye kankanan gabanta gaba daya ba, da sauri tace "A'a Abba ni na koshi" Dad yace "bari dae ya karo maki ki kara" bata kuma cewa komae ba, dad ya canxa tasha xuwa news ya maida hnklinsa. Bayan minti sha biyu drivern ya dawo rike da ledan water melon, ya ajiye ma Dad kan center table, ya mika masa canjin dubu daya yace "na ga dayawa oga" dad yace "to rike canjin kai ma sae ka siya ka sha" gdya yyi ya fita daga falon, dad ya mike da kansa ya nufi kitchen ya dauko wuka da plate ya dawo ya dauki kankanan daya ya yanka snn yyi slicin dinsa kan plate din ya dauki toothpick ta saka ya mika ma Ashnaah da ke ta kallonsa, a kunyace ta ce "lahh Abba ni ya isheni fa" Dad yace "A'a ki dae kara" karba tayi tayi masa gdya kuma, har kusan Karfe goma da rabi Ashnaah na xaune falon da dad, ta dae ji ta fara jin bacci ta mike tana kallon dad tace "Abba bacci nake ji" yace "to tafi kiyi kwanciyar ki," ledan sauran kankanan ya mika mata yace "ga shi ki tafiya da sauran, Wanda aka yanka kuma ki saka a fridge" gdya tayi masa ta karba snn ta dauki plates din da tasha fruit din da nasa da wukan ta kai kitchen, tsaf ta wankesu ta ajiye snn ta fito ta kuma yi masa sae da safe ta nufi sama ina ma Abbanta ne hka da ta more rayuwa, dakin Ummi Ashnaah ta nufa, ta tarda Ummi xaune suna kallo da rukayya, Ummi tayi mata murmushi tace "sae ynxu" Ashnaah tayi murmushin ita ma, ta ajiye ledan hannunta xa ta xauna kasa Ummi tace ta dawo kan gado, ta xauna gefen gadon, Ummi tace "yana can dakinsa in kina jin bacci ki tafi ki kwanta kar ki takura kanki" Ashnaah ta sunkuyar da kanta tace "to ga fruit Abba ya siya min" Ummi tace "to kin gode" mikewa Ashnaah tayi ma Ummi sae da safe xata fita daga dakin Ummi tace "to kin bar fruit din" Ashnaah tace "A'a na sha da yawa Ummi, na koshi" Ummi tace "to dauka ki kai ma Khaleel" bbu musu Ashnaah ta dauki fruit din snn ta kuma yi mata sae da safe ta fita ta nufi dakin Khaleel, a hnkli ta tura kofar dakin ta same shi durkushe kusa da fridge dinsa, gabanta yyi mugun faduwa ganin abinda ke hannunsa yana dubawa, tasan baxae wuce expire date yake dubawa ba, yana ganin ta ya mayar da sauri ya fiddo ruwa, ta dauke kanta ta ajiye ledan hannunta ta nufi kan gado, ya bi ta da kallo yace "yhu re back wife" kai kawae ta gyada masa ta kwanta gefen gadon ta juya masa baya kmr bata son mgna rufe fridge din yyi ya dawo kusa da ita ya xauna yace "jikin ne wife?" Girgixa masa kai tayi da kyar tace "bacci xan yi" yace "OK wife, amma bari ki fara shan drugs dinki" girgixa masa kai tayi da sauri tace "amae xan yi" bata jira cewarsa ba ta juya masa baya, mikewa yyi ya dauko blanket ya rufa mata, ta lumshe ido kmr me bacci, gefen gadon ya xauna ta daya side din yana danna wayarsa, har kusan sha daya Ashnaah bata yi bacci ba amma bata bari ya gane ba, mikewa ta ga yyi yana kallonta, ta rufe idonta gaba daya kmr me baccin gske, fridge ta ga ya nufa ya bude ya fiddo kwalban daxu yana kallonsa rabon sa da shan giya tun ran da ya sha a birthday, ganinsa yasa yaji kmr ya shekara goma rabonsa da sha, Ashnaah taji kmr tayi masa mgna amma ta kasa sae taji hawayen takaici na sakko mata, budewa taga yyi ya koma bakin gado ya xauna ya kai bakinsa ya shiga sha, ko second talatin ba ayi da kai shi bakinsa ba ta ga ya cire da sauri, juyawa tayi tana kallonsa don yasan ma ba bacci take ba, ya ajiye kwalban hannunsa kasa gefensa ya rike kansa, mikewa taga yyi da hanxari ya nufi bathroom ta bi sa da kallo, amae ta ji ya shiga yi, ko motsawa daga inda take bata yi ba, amae ssae yyi a bayin, daga karshe ya fito da kyar bae bari sun hada ido ba ya nufi can gefen gado ya kwanta ba tare da ya kalli kwalban da ya ajiye kasa ba don ko ganinsa ma bae son yi, nn da nn bacci ya daukesa. Ashnaah tayi murmushi ta mike ta dauki kwalban taga har ya kusa rabi, bayi ta shiga da shi ta toshe hanci don ko warin bata son ji, ta tuttular da giyan snn ta dawo dakin ta bude fridge ta fita da sauran ma gaba daya duk sae da ta tuttulesu a bayi hancinta a toshe snn ta wanke bayin da kyar don duk tayi weak, wanka tayi da ruwan dumi ta fito da kwalaban ta ajiye su dakin tayi kwanciyarta da xanin jikinta, nn da nn bacci ya dauketa ita ma, can cikin dare ta farka ta dalilin aman da ta dinga ji, ta mike xaune da kyar ta jingina jikin gadon xuciyarta na tashi, juyawa tayi tana kallon Khaleel taga baccinsa yake, mikewa tayi ganin aman na neman taho mata ta nufi bathroom da sauri, ta durkushe ta shiga kwararo aman, hkn ya farkar da Khaleel ya mike xaune da kyar ya rike kansa da ke juya masa.
Chapter 76 · 0% Book details