Sashe 9
Dame Ake Ado Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read
1⃣ DAME AKE ADO 2 Uban waye yagaya muku wane munafuki ne yasanar daku wannan magana Umma tafadi ahasale batabar sunce komai ba tadora da masifa to duk wanda yagayamuku karya yake yi hassada ce kawai nice nahaifi Ahmad nice uwarsa Afusace take maganar Daya daga cikinsu takuma amshewa haba baiwar Allah kiyi hakuri munriga munji komai zance duniya fa baya buya Idan har danki ne mai yasanya aka cireshi daga lissafin sunan yayan gidan kinada Auwalu da sani da rabi'u yaya akayi shi yafita daban? Mu kinga yansako ne kiyi hakuri sai anjima tadire kudin sadaki akan kayan suka juya suka nufi kofar fita Umma tabisu dasauri tana fadin don Allah kudawo nayi muku cikakken bayani don Allah kudawo Basu saurareta ba suka nifi kofa suna ficewa suna ganin Ahmad suka kalleshi suka wuce kawai Umma data biyosu da sauri arude taci karo da Ahmad tsaye ta yi turus cike da tsanani tashin hankali tana kallonsa Ahmad yana tsaye idonsa yana zubda hawaye cikin muryan kuka yake fadin kirabudasu Umma ki kyalesu gaskiya suka fada munyi laifi dabamu gayamusu gaskiya tun farkoba wannan wace irin masifa ce wane irin cin mutunci ne wannan don cuta sai da muka gama komai harmun raba katin biki zasuzo mana dawannan maganar wane irin Abin kunyane wannan shikam tsananin tausayin Umma yafi komai yawa aransa wane irin so ne wannan baiwar Allah take yimasa ina ma itace tazo a matsayin mahaifiyarsa inama ana komawa baya asauya Uwa daya koma yafita daga cikin mahaukaciya yakoma cikin Ummansa mlm sulaiman dake sallama yashigo da hanzari jin kuka matarsa a rude yake yakalli deeje dake kuka yakalli Ahmad cikin tsananin damuwa yace lfy deeje meke faruwa haka kike kuka subhanallahi Dahannu ta nuna masa tulin kayan lefe dake jibge yakallesu yadawo da kallon kanta yakuma shiga rudu kansa ya kulle yace banfahimta ba deeje ? Cikin kuka tace daga gidnsu Ummi wacce Ahmad zai aura waisun fasa auren ...... Takuma fashewa dakuka yawaro ido waje da wata irin kidima mara fasaltuwa gabadaya jijiyoyin jikinsa sun janye saiji tamkar yadaskare dakyar ya iya karfin halin kakalo wani zancen bangane sunfasa Auren ba wani abu akayimusu tadansausata kukan tana goge hawaye
2⃣ tace ba.ayimusu kome ba mlm saidai munafukai sun shiga ciki lamarin anje angayamusu Ahmad wai shege ne ba shida uba banda wulakacin mai yasanya tunfarko basu ce haka ba saida aka kammala komai malam yayi shiru yama rasa abinda zaice domin iliminsa da tunaninsa suntsaya gabadaya na wucin gadin Lami dake labe tana jinsu tadaka tsalle cike da tsananin murna har da daga hannu sama ta fadi Alhamdulillahi da.anayimin wata fuffuka kullum yaro yana shiga manyan riguna shiga masu gida daman nafadamasa ba da riga ake ado ba da uba ake ado ehe! Takuma zuro kanta tana jiran jin abin da mlm din zaice tasami nadorawa sai jiyo shi yana fadin kunga kuwuce ciki muyi maganar kantabarma suka zauzzauna mlm yadubesu da damuwa yace duk Abinda Allah yakaddara babu makawa sai ya sami bawa daman can Allah baikaddaro ummi matarka bace Ahmad don haka babu yanda za.ayi ka aureta Umma tace Amman mlm baka ganin anbata masa suna kana ganin ko wata diyar yaje aure zata yadda ta aureshi malam ? Ahmad yadafe kai yana kallon umma tausayinta yana kuma karuwa aransa da kyar ya iya bude baki saboda nauyinda yayi masa yace Umma kiyi hakuri kiyi hakuri .......kuka yaci karfinsa malam yadube shi da tausayawa wato Umman yake baiwa hakuri Umma tace Ahmadu kai ya dace mu baiwa hakuri tunda mun kasa kareka daga wannan suna mummuna mun kasa cire kalmar shege daga jikinka Balaifinku bane ba Umma bakuda laifi kunyi duk wani yunkuri na boye wannan mummunan suna daga gareni Amman Allah yakaddara sai najishi Umma idan wanka ba.aboye cibifa malam yakalleshi da hanzari yace kaga tashi kawuce dakinka zansan yanda za.ayi idan takama aje a sulhunta nema zanyi zannemeka yamike dasauri yana tangadi iska naneman kayardashi saboda juwa akarshen kwanar gidan yaci karo da Lami tana lekensu takalle shi da hanzari saita juya tayi cikin gidanta yabita ka llo cike da mamaki mai tsanani bai san abinda yayima matar nan ba tasanyashi agaba yanufi gidansu Ummi yayi shiru yana tunanin idan yacemata shine zata iyakin fitowa kokuma iyayenta suhanata don haka yace da yaro kace Abdul ne bayan tafiyar yaron da kamar sakan talatin saigasu tare da Ummi fuskarta dauke da tsananin mamaki waye kuma Abdul yake sallama da ita mamakin ta yadada karuwa sanda takula bakowa bane sai Ahmad tsaye ya hade hannuwa akirji gabanta ya yanke yafadi tayi dan dum dum kamar zata koma sai kuma ta dake ta bata rai tace gani yaya akayine ? Tana magana babu ko fara.a
3⃣ tsananin mamaki yacika Ahmad yau Ummi ke masa haka yadaure da kyar yace Ummi babu gaisuwa kenanko? Takara hade rai tana fadin baikamata nagaida mayaudari ba kacuceni matuka Ahmad kasanya nabata lokacina daduk wani tunanina akanka Ashe kai shege ne bakada Asali maganar tadakin kirjin kwarai dagaske idonshi yakuma cikowa da kwalla kamar zaifashe da kuka yakwantar da murya cikin lallashi yana fadin
Ummi yanda muka gina soyayyarmu cikin aminci banyi zantan dan Abu kalilan irin haka zai iya mana itaba...... Takalleshe afusace tana fadin Au kai agurinka wannan yar karamar matsalace kenan amman ka bani mamaki matuka to idan kai ta zama karamar matsala a gurinka kana ganin doka kasance shege bawani abu bane to nikam Allah yasani babbar matsala ce bazanso nahaifi ya ya adinga cewar Ubansu shege ne mara asali ba maganar mungina soyayyarmu kuwa daman can akan tubalin toka da karya muka ginata don laillai dana san kai shege ne da banta lokacina akanka ba na soka Ahmad ashe kai mara asali ne ka boyemini kacuceni wlh kayaudaran .... Saita fashe dakuka 4⃣ DAME AKE ADO ....... Ahmad yaji duk yatsani kansa da rayuwarsa tabbas Ummi tayi gaskiya waye zaiso hada zuri.a da shege mara.asali hawaye dayake ta hadiyewa suka ci gaba da biyo kuncinsa yakasa cewa komai domin bashida sauran abinda fada din Ummi ta kalleshi afusace tace idan abinda ya kawoka kenan nizan koma domin inada abinyi a gida yayi dum yana kallonta da tsananin mamaki da damuwa jiyake kamar ya bita yakamota shikenan Ummi tayimasa nisa haka yajuya yanufi gida baisan yanda akayi yajeba yasandai Allah ne yakaishi Acikin gidama duk wanda akasanar da shi abinda yafaru cikin yan uwansa sai hankalinsa yatashi abinda suke tambaya shin Uban waye yaje yafada duk yanda sukaso ganin Ahmad sulallasheshi abin yatura don ya kargame kansa acikin daki Malam sulaiman kam yajima yayi shiru akan dakali yana tunanin mafita har zuwa lokacin da ya cimma burin tunanin nasa yasanya yaro yakira masa dan uwansa mlm jibril bada jimawa ba ya fito ya zauna kusa da yayansa yace malam gani naji ance kana kira na yakalle shi tsahon lokaci sannan yace kaji abinda yafaru da Ahmad kuwa? Dasauri yace naji wlh dazu na shiga gida Lami take sanar dani Abin kam baiyi dadi ba mlm sulaiman yanisa yace tunda abin nan yafaru nake tunanin mafita har Allah yasanya tunanina yafado kan diyarka Raliya da hanzari yadubeshi yace Raliya kuma mlm yagyada kai yana fadin ita kuwa kamar yanda kasani nima nasani Raliya tazama gagararriya wacce duk wani kokari namu dana yan uwanta yagagara gyara ta saidai addu.a gashi tayi girman daya dace ace tafidda miji amman anrasa wanda zaifito dagaske yace yana sonta saboda sanya shashanci datayi agabanta hakan nakeganin abune mawuyaci Raliya tasamu miji nutsattse don haka tunani yasanarda ni mezai hana tunda anyi haka amaida ranar auren Ahmad kanta kada acanza komai ayinan da wata gudan amman kai yakagani domin ka fini hakki akanta yayi shiru tsawoh lokaci yana nazari can yadaga kai yakalli yayanasa yace yaya duk abinda kayanke yayi saidai kana gana ganin Ahmadu bashida wata illah da zata iyayiwa rayuwar Raliya illah ? 5⃣ mlm sulaiman yaduberhe da sauri yace kada kace mini kacikin mutane masu jahilci dakama wani da laifin wasu wlh bagori zanyiwa kaina ba Ahmadu yafi duk yayanda muka haifa nagarta balle Raliya da kai kanka kasan irin abubuwan kunyar da ta daukowa gidan nan auren nasu shi zai zama rufin Asirinsu baki daya jibril ya girgiza kai yana fadin wannan haka yake to Allah yasanya Alkhairi mlm sulaiman yayi murmushi cike dajin dadi yace Amincewarka tafi komai agareni kuma koda hakan batafaruba kayan dakin raliya daman akaina suke tunda dai nine waliyinta dahaka suka rabu ran malam yahaskake yasan yana da damar kara kyautatawa Ahmad da mai dakinsa Adaki yatta Umma tana lazimi da alama addu.a take yiwa danta yasami guri yazauna yana murmurshi yace Allah dai ya.amsa Addu.arki saiki kwanta ki soma bacci Umma tadubeshi damamaki
Fuskarta babu yabo ba fallasa tace malam kenan kana zaton hankulanmu zasu kwanta cikin sauki kuma wannan kankanin lokaci ? Yakuramata ido yana karantar yanayinta yace Amman ai tunda abin nan yafaru Allah muke gayawa ba kyazato zai kawo mana mafita cikin gaggawa tayi saurin yadda da batunsa har daga fuskarta yafimci hakan ta hanyar yin murmushinta tana fadin duk abinda da akace Allah magana takare Amman taimakeni sanar dani wannan Abin dadin yayi dariya yana kokarin tattaro farin cikinsa suyi rabonshi tare yace danki dai yasami matar aure kuma awannan rana za.ayi bada fashi takalleshi datsananin murna da mamaki wacce tagaza boyuwa akan fuskarta tace najima banji labari mai dadin wannan ba dan Allah mlm wacece dan Uwanane ya.amince da baiwa Ahmad auren diyarsa Raliya kinga Asiri yarufu ko ?
7⃣ DAME AKE ADO Anacigaba dagudanarda sha anin biki Abba duk yaraba iv ga dangi da abokansa abin mamaki har sanarwa yasa agidan radio itama Umma tadauki dukanin burinta tasanya akan bikinnan hakanne yasanya yadanne zuciyarsa da damuwarshi ake gudanarda komai cikin farinciki duk da bahakanne akasan ranshiba Abinda yabashi mamaki da tsoro ya kuma sanya Raliya tafita daga ranshi baiwuce rashin mutunci datayi mashi cikin soron gidanba malam yayi matukar kokarinsa domin shine yayi duk wasu kayan daki na Raliya akaje akayi jere hatta kayan daya dace ace uwa tayi shine yayi domin lami cewa tayi Auren da akayiwa diyarta na dole ne donhaka ko tsinke bazatayi ba wadanda suka haka suzasuyi komai saidai mutane dayawa sungane borin kunyane domin babu tsiyar dataaje domin Auren diyarta tuncan baya kudinta wurin bin malamai yake karewa balle yanzu datake iyakacin kokarinta na wannan Auren baitabbataba domin acewarta diyarta kalar masu kudice da Asali ba kamar Ahmad fakiri ba Ranar kamu amarya ba yabo ba fallasa tayi kwalliya kamar gaske koda yake yayyanta sunyi mata fada harda mahaifinta da Abban duk da Ahmad duk da Ahmad bahalarta wurin kamun ba yayi farinciki kwarai dagaske da lbr dayaji gurin yara na yadda Amarya ta cashe rawa