Sashe 15
Dame Ake Ado Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
babu wani abu dazaibiyo baya insha Allah sai Alkhairi nayi imani zaikoyarda ita komai tunda kinkoyamasa kokin manta da dannaki ya iya girki kala kala ne? Yakarasa yana dariya abinda yasanyata darawa itama ya dinga zolayarta haryasamu ta sakko Suka fahimci juna sannan suka kwanta baccinsu sunawa yayansu addua tunda asuba yatasheta tayi sallah shikuma yawuce massalaci bayan yadawo yazarto dakin yazauna yacigaba da lazimi itakam baccinta takara komawa aranta tanaganin babu abinda yafi gadonta dadi kamar wacce akatasa karfe bakwai tafarka ta tadda yayan nata har lokacin yana lazimi tamike tsam tanufi kofa ya bita da kallo kamar zaiyi magana saikuma yafasa don yayi zaton bandaki zatashiga itakam kicin tawuce tayi zaune tanasakawa da warwarewa akan abinda yakamata tayi domin sanda yatafi masallaci umma takira wayarshi tadauka umma tace waye tace nice tace yauwa daman kedin nakeson kidauka domin nasan yanzu Ahmad yana masallaci kinaji idan gari yawaye kishiga kicin ki girkamuku abinda zaku karya sannan kishare gidan kigoge ko ina nasan kin iya shara daguga dan kinayi amakaranta ko dasauri tace eh inayi tace to kitabbatar kinyi kinjiko? 2⃣2⃣ DAME AKE ADO 2 Takoma amsawa da to shine yanzu tana tsaka da bacci maganar Umma tatasheta tadauko doya tafara ferewa bayan takammala tayankata gutsi gutsi kamar zatayi faten doya sannan tadauki kwai ukku tafasa akan doya ta kunna risho tadora mai kozafi baiyiba takama kwan da doyar ta zuba tana jiran su soyu daga can acikin daki yafara jiyo kauri dasauri yamike domin zuciyarsa tabashi ma'u ce yanufi kicin din dasuri saiyaga doya da kwai da mai sunata zabalbala yarike baki damamaki yana fadin Nana mezakiyi? Mekike dafawa? Tayi firgigit ganin kallon dayake mata tace doya da kwai zanyi sai akacemiki kuma haka akeyi waye yasanyaki girki kuma baki iyaba cikin zafin rai yake maganar tayi kwal kwal da ido tana jada baya domin tana gudun kada yadoketa tace Umma ce tace nayi abincin Kari kuma............kuma..........yadoka mata tsawa get out mekika iya bayan shirme yadauko kaskon suyar daga kan wuta yayi waje dashi sukaci karo abakin kofa tana tsaye tana gunguni yayi baya dasauri dan sauran kiris yakifamata yakoma kuluwa yace Amman bakyajin magana nana bance kibar gurinnanba dasauri tawuce tabar wurin takoma gefe tatsaya yanufi gindin rariya da abinci yasamu kwano yazuba yasanya ruwa yawanke kaskon sannan yanufi kicin din tana tsaye tana kallonsa yadauki wata tukunya yazuba ruwa yadaura shayi duk tana tsaye tana hangensa yanata kaiwa da komowa acikin gida harya kammala dafa shayin yajuye aflask yanufi kofar gida tana ganin yafice tanufi kicin Don ganin abinda yayi bata hango komaiba tafara bubbude kwanika cikin tsautsayi bataga flask din yazuba shayinba tabangaje yafado jikake tush flask din yafashe shayin yazube atsakar kicin din tarike baki cike da tsoro dafargaba saita kasa gaba takasayin baya kamar ancilloshi yashigo gidan tundaga nesa ya hangota akicin yakarasa da sauri yana fadin nana meyakawoko kicin dinnan bance kada kisake kishigaba tayi tsuru tsuru daidai lokacin daya karasa yadauki dogon salati sanda yaga flask din shayi duk kwance akasa yana ambaliya ya kalleta yama rasa abinda zaice cikin rawar murya tace Allah yaya bangani bansan da flask agurinba yayi ajiyar zuciya yayi kokarin hadiye fushin shi domin ma'u yargaban goshin shice duk da banzan rawar kanta yanunamat kofa zokiwuce daki maza tataho tana rakube rakube tana goge ido tana gudun kada yadoketa har ta isa bakin kofa data samu tafice ta falla da gudu saida tadire acikin daki sannan tazaya tana haki da dariya wai Allah nagodema da yaya Ahmad ya mini irin ko rankwashinsa ne aida naga takaina tarike haba tana haki shi kam kada kai yayi da takaici sannan ya shiga yashare kicin din yakara dora wani shayin yazuzzuba akofi yakaimata nata hardaki ta amsa tana fadin nagode yaya 2⃣3⃣ DAME AKE ADO 2 yadaga kai kawai sannan ya zauna yafara shan nasa ma'u tadubeshi yana shan shayin tace yaya don Allah zankoma makaranta kaga ranar monday za afara jarrabawa kuma Abba yace saikayadda zankoma yadaga kayi yakalleta saiyaga ikacin gaskiyarta take maganar babu wani bayani dazaiyi uagamsada ita saiyace aibazakiyi wannan jarabawarba kihakura kawai tawaro ido cike da fargaba yaya kanufin nadaina karatu kenan kainefa kace zanzama likita yajijjiga kaida damuwa ma'u tayi kankanta da Aure tayi kadan dafuskantar irin wannan matsalolin donhaka gara yasanar da ita gaskiyar komai yadubeta da nutsuwa yace nana kinsan yanzu ke matar aure ce ko? Tadaga kai alamar eh yagyara zama yauwa kinga ai makarantarku ta yanmatace babu matan aure ko? Towannan dalilin yasanya bazaki kara komawaba kinkammala makarantar kenan yanzu zakizauna zaman aurenki kinemi Aljannarki tamike atsorace cike dafaduwar gaba yaya zakace haka yaya Ahmad shikenan niyanzu bazankoma zuwa ko inaba sainan gidan kuma bazan zama likitaba......yaya bakayin karya amman yanzu kayi meyasanya tambayar tacazamasa kwakwalwa harya rasa amsar dazaibata saiyasake hade ransa yace kincikani dasurutu nana tashi maza kiyi wanka kishare gidan kiwanke kwanika tayi narai narai da ido domin tana matukar son karatunta tace amman yaya...............yadaka mata tsawa isaid get out ma'u jikinta yadauki yadauki rawa hawaye yamakale ido yafara tafice dasauri ta nagoge idonta tana aiki tana kuka yanajiyo sautin kukan nata bashida zabi babu yanda zaiyi abba yagama yanke hukunci daga karshe ma saiyayi wanka yafice yabar gidan wannan shune yakara dagamata hankali saitaji gidan yakara mata girma tazauna tsuru babu abinyi sai tsoro yafara shigarta tamike tanufi soro takama leken waje tana hango mutane dake kaiwa da komowa saitaji sanyi aranta donhaka saita zauna akofar gidan tana kalle kalle dakaramin hijab akanta idan taga abin dariya tayi idan taga abin mamaki tayi mutane suna wucewa suna kallonta babu wanda yayi zaton matar gidance domin komakota basusan ankawo amaryaba sunyi zaton Raliya ce itakuwa daga yanayin kawayenta da gantalin datake fita kullum yasanya suka gano bamatar arzikiceba donhaka babu wani wanda yarabeta tsawon lokaci tananan zaune tana cike da nishadi shikam Ahmad gidansu yanufa kaitsaye yatadda yan uwansa sunzo dayake ranar assabar din karshe sati ce anata cafta saiyazauna anatayi dashi Umma saishige dafice takeyi wurin ganin takammala kirkin rana kunya da nauyi sunhana ta tambayi ma'u takula shima Ahmad kunyar yimata maganar ma'u yake amman daga yanayinsa talura babu wata matsala anan sukaci abinci lokacin da inna tazuba abincinne ma yatuna da ma'u da abinda zataci saidai Allah yataimakeshi umma tacika flask din da dambu datayi tadire tace gana yar gidanka Ahmadu yaji dadin hakan danyana kammala cin abincin yadauki flask yahaye babur dinsa yanufi gidanshi abinda ybashi mamaki da tsoro baiwuce hangon ma'un shi zaune akofar gida daramba tana hirarta da wasu yara da alama yayan makota tasamu tabiye musu yanacigaba da karatowa mamakinsa nakara linkuwa harzuwa sanda ya iso indatake da babur dinsa tadaga kai takalleshi saitadan firgita masamman yanda yanayinsa yacanza lokaci guda takalli yaran dake gabanta tayi duru duru sai tamike ta shige cikin gida dagudu batayi birki ko inaba saibayan gado tana huci talabe cankurya tana maida numfashi yashigo gidan ransa yana suya ya iso harbayan gadon yajawo kunnenta tafasa ihu jikinta naci gaba da bari dan Allah yaya Ahmad kayi hakuri Uban wa yace kifita waje kizauna komunkoya miji wannan tarbiyar agidane? Cikin sheshshekar kuka tace A ah gidan ne shiru ga tsoro shine naleka waje don Allah kayi hakuri tafashe dakuka yadunkule hannu ya rankwasheta yana fadin koda zanhakura saikinji ajikinki kifita kofar gida kizauna kamar wata sokuwa inakikakai aurenki yakoma rankwashemata kai kwas akanta takuma sanya ihu saida yajeramata guda hudu sannan yasakarmata kunne takuma fashewa dai kuka lokacin yafice daga cikin dakin yanufi shago domin yasanya uniform dinshi yatafi wurin aiki saidai yanashirin kukan ma'u yana dukan zuciyarshi tuncan baya bayason bacin ranta yakanyi komai dankar abatamata rai balle dayaji sunan mahaifiyarsa ne akasanya mata hakan yakara soyayyarta acikin zuciyarsa yanzu kuma gashi tazama matarsa wato yanzu soyayyarta agareshi hawa ukku ce don haka dole intana kuka yarikaji harcikin bargonsa da kyar yakammala shirinsa yanufi soro da zummar yafice saikuma yaga rashin dacewar hakan dan haka yajuya cikin gidan yanufi dakinta tana rakube a inda yabarta abayan gado tana kuka ya isa inda take tahada kai da gwiwa tana sharbe yakira sunana tadago takalleshi dafaduwar gaba don batasan yadawo dakinba tayi zaton kara dukanta zaiyi donhaka tafara ja dabaya tana sharbe majinarta tana kuka