Sashe 49
Dame Ake Ado Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Dole ga nana ya kai buk'atarsa. Wannan ya yiwa Nana dad'i, wannan abu da ma'un tayi mata ya sanya take girmamata k'warai da gaske, sannan ta rik'eta kamar 'yar uwa, za a gaisa ayi wasa da dariya dai-dai gwargwado. Ammam ranar da Ahmad zai koma 'Dakin Ma'u Nana ta raina kanta ganin yanda yake ta zumud'i da rawar k'afa har taji Kishi ya rufeta a ranta tace sai kace ba gurin tsohuwa zai je ba. Tun daga iri rigar baccin da Ma'u ta sanya ta tsokanoshi ya dinga binta da kallo tana wani kwarkwasa da yanga har dai ya gaji ya janyota yana fad'in, "Yarinya wallah baki isa haukatani ba. Ta fashe da dariya don ta gano ya shiga tarkonta.Ranar kam saida ta raina kanta don a daren nan saida ya fanshe watanshi guda, musamman da yaji ta kamar ba Ma'unshi ba ta koma masa wata 'yar Budurwa kamar daren Amarcinsu. Wannan daren kam sun k'arar da shi gurin nunuwa juna yanda suka yi rashin juna. AHMAD ya gama gano yanayin Matansa, don haka yaci Maganin zama da kowacce dai-dai halinta. Ita dai Nana tana da tsananin buk'ata, don haka kafin girkinta ya fita sai ta isheshi, ita kuma Ma'u shi ne yake da tsananin buk'atarta saboda gyara da kuma yanayin halintarta, don haka har Nana ta ganoshi dole ran Girkin Ma'u d'okin yake yi da zumud'i, ita kanta Ma'u ta gano hakan, sai dai yana iyakacin k'ok'arinsa gurin ganin ya kamanta gsky da adalci a tsakaninsu, sai dai bai isa ya 6oye soyayyar ma'u ba, duk da itama Nana yana bata wani matsayi na ita ce jininsa, 'yar uwarsa da yake sun fahimci juna sai suka zauna lfya. Cikin shekarar ne duk Allah Ya albarkacesu da smun juna biyu,
tsakaninsu wata guda ne kacal, Nana ce tafara haihuwar k'aton Namiji yaci sunan ABDULLAHI (Mujahid), Yaron da yaga soyaya da gata gurin dangin 'Yam Leman. Sai kuma Mau da ta kara haifo Mace. Itama ta sami gata, Ahmad dai shi ne mutumin da ya karya alk'adarin canfin danginsu na haihuwar d'a d'ya ko biyu, sai gashi da biyar cur! wannan ya sanya iyayensa jin dad'i. Adalci da Ahmad yayi a Gidansa da ya kwantarwa da Ma'u hankali shi ne hana Nana yin aiki ya ce shi ya dace ya nemo, duk da Nana ta damu da farko, rigima har gurin Babanta, amman da bata sami goyon baya gurin Iyayenta ba dole ta hak'ura, don Babanta yace ita kanta Mahaifiyarta digiri biyu gareta, kuma saboda k'warewarta a makaranta suka had'u suka yi aure, amman bata aiki saboda su Family d'insu suna da tsananin kishi, wanda tayi a baya ma Allah Ya amfana. Hakan ne ya sanyayar mata da guiwa, Ahmad ne yayi k'ok'arin k'ulla auren Mahaifinsa da Hajiya Amina don Mijinta shekaru biyu ke nan da rasuwarshi. Hakan ya yiwa kowa dadi Musamman kakarshi data damu yayi aure. Ita dai nana tun daga haihuwa 1 shiru babu k'ari da yake itama jinin iyalin ne suke ta6ata. GAME DA UMMI kam a yanzu ta yarda Ahmad yafi karfinta da ta gano matsayinshi dole ta samarwa kanta lafya, amman Iyayenta sun yi da sun sani da takaici, musaman da Mahaifin nata ya gano mahaifin Ahmad tsohon Ubangidansa ne, shi ke bashi kaya kafin kaninsa ya cigaba da bashi. wata rana kafin tayi aure ta hadu da Ahmad a Super Market ta gaya masa shi kadai take so amman ta hakura da shi zata auri wani ta bashi tausauyi kwarai da gaske, sai dai ya san bai isa ya karawa Ma'u kishiya ba, sai ya amshi lambar Accunt dinta ya tura mata kudi masu yawa wanda dasu ne tayi komai na auremta. WATA RANA sunje Gidansu da yamma ana ta hira sai suka jiyo kuka a harabar gidan, suka fito da sauri dasu Umma dasu Ma'un da Yaya Auwal da sauransu da yake duk ranar Lahadi da yamma annan ake hake had'uwa ayi ta hira. Lami suka gani dawata k'armasashiyar Mata kamar Fatalwa, Matar ta fadi Lami na kokarin tashinta tana kuka, ta lalla6a ta tasheta ta rungume a jikinta tana takawa da kyar! har ta isa kusa dasu ana tsaye cirko-cirko. Mal. Sulaiman ne yace, Lami wace ce kuma wannan? Cikin kuka Lami tace, "Yaya Raliya ce! Kusan Wata hud'u ke nan da aka kawota da cuta mai karya garkuwar jiki (H.I.V) dukkan abinda nake da shi ya k'are gurin Magani, kullun Mahaifinta idan zai zo gurinka sai nace ya gaya maka sai yace a'a shi ba zai fad'a maka ba, shi ne ni kuma da naga kamar zata mutu ne na kwasota tafiya bata iya yi don ku taimaka mata. Yaya Auwal yace, Raliya ce wannan Lami Subuhanallah!" Kowa ya tsorata da ganin yanda Raliya ta koma Yaya Auwal yace a kaita Asibitinshi zai yi mata komai kyauta, shi kuma Ahmad ya basu Kud'i mai yawa yace kuma duk k'arshen Wata ta dinga zuwa gurin Ma'u tana amsar Kud'i. Raliya da Lami suka fashe da kuka. Umma tace "Ato, duniya ke nan, tafi duk yanda ka d'auketa, sakayya ce take zuwar muku. Suka lalli juna da mamaki. TAMMAT BIHAMDILLAH!.
Surayya
6 November 2015 at 12:10 · Public
Save · More
Like
React
Comment
Share
Like35
Write a comment...
·
Saihanatu Umar Umar
Mun gode sosai
Like · React · Reply · More · 6 Mar 2019
Adama Abdulkarim Kiyawa
To alhmdllh mungode kwarai da gaske Allah ya kara daukaka da basira ubangiji yayi jagora Allah ya saka da alheri masha Allah
Like · React · Reply · More · 2 Sep 2018
Sa'adeeyer Zarah
Muna godia. Kuma muna jin dadin shi ...
Like · React · Reply · More · 6 Nov 2015
Muhd Suhunun Muhd
Tank

Maryam Abdul
tnx

Rahama Adamu
Allah ya taimaka

Bakura Sheriff Kayima
allah yabadasa,a
Like · React · Reply · More · 11 Nov 2015
Aisha Saleh Aliyu
TNX

Zaynarb Abdullahi

Amirah Muh'd
Tnx sury allah yabar zumunci
Like · React · Reply · More · 7 Nov 2015
View more comments…