← Book details Dame Ake Ado Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 49

Sashe 36

Dame Ake Ado Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka ranar ya koma gida sukuku ba walwala har sai da ma,u ta fahimci yana cikin wani hali, bata matsa masa da tambaya ba don ya sanar da ita tuntuni akwai matsala a ofis dinsu, don haka addu,a kawai takeyiwa mijin nata. Duk yadda taso faranta masa ta sanyashi cikin farin ciki ta kasayi dole ta barshi shi daya cikin daki don ta kula abinda yafi bukata kenan.
Nana kam da kyar takai kanta gida domin kanta wani irin ciwo yake yi da juyawa. Tana yin parking ta nufi gidan da gaggawa, amma bata kai ga ainihin sashinta ba ta yanke jiki ta fadi kasa. A dai dai lokacin hajiya batula mahaifiyarta ta fito daga sashinta ta hangota. Hajiya batula ta fasa kara ta nufeta da gudu tana salati, ta kamata ta dagota sai taga idonta ya juye alamar ta suma. Ta fasa ihu tana kwallawa masu aikin gidan kira. Da gudu suka iso kowa a rude jin kiran da hajiya batulun ke musu, ganin halin da nana ke ciki ya kara daga musu hankali suma. Hajiya batulu cikin kuka take cewa kubani ruwa na yayyafa mata, daga daga cikin matan ta kwasa da gudu sakwanni kadan ta dawo dauke da ruwan robar swan mai sanyi.. Hajiya batulu ta karba saboda tsabar gigicewa ma kurzawa nana shi tayi ajikinta gaba daya. Nana tayi wata doguwar ajiyar zuciya ta bude idonta a hankali. Hajiya batula tayi doguwar hamdala sannan ta kalli yan aikin tana cewa ku taimaka mini ku kamata mu kwantar da ita akan kujera. Suka ciccibi nana aka kwantar da ita ta dauko wayoyinta ta fara neman layin wayar mijinta wanda yake abuja. Bugu daya ya dauka, cikin tashin hankali hajiya batulu tace masa Alhaji nana bata da lafiya, yanzu ta fadi har da suma. Alhaji nura kwangila ya gigice yace, suma kuma me ya sameta? Ta kalli nana dake kwance akan kujera tana kallonta tace bansani ba, dama cikin kwanakin nan na kula bata jin dadi, amma danayi mata magana sai tace babu komai..........Kinga bar bayanin nan haka zanyiwa likita waya yanzu yazo ni kuma zan hayo jirgi na taho yanzu, ki kula da ita kafin nazo. Ya kashe wayar da damuwa a take a lokacin yayi waya a tanadar masa ticket mai zuwa kano.
Like· Report·Jun 14
Nusaybarh Mustapha Ibraheem
127. Hajiya batula ta isa ga nana ta zauna ta dora kanta bisa cinyarta tana shafa kanta. Sannu nana, meke damunki? Nana ta rintse ido hawaye ya zubo mata , batason tunawa amma bazata taba mantawa ba domin soyayyar Ahmad ta zame mata masifa, bazata iya rayuwa ba Ahmad ba. Ganin tana hawaye ya kara tayar da hankalin mahaifiyarta ta tace shikenan ya isa daina kukan. Mintuna goma baya sai ga likita ya iso gidan masu hidima sukayi masa jagora har cikin gidan da yake kowa ya sanshi a gidan. Hajiya batula na ganinsa ta mike da sauri tana fadin yauwa karaso doctor ka dubamin ita. Likitan ya isa da sauri ya sauke jakarsa da yake rataye da ita ya fara fiddo kayan awo kala kala. Cikin yan mintuna kadan ya kammala auna nana yayi mata wasu yan tambayoyi ta bashi amsa, daga karshe yace da hajiya batula dole sai sunje can asibitinshi anyi mata wasu gwaje gwajen. Hankalin hajiya batula ya kara tashi sosai ta dubi likita tace likita gaya min meke damun diyata? Cikin kwantar da murya likitan yace kwantar da hankalinki hajiya ba wani abu bane ba, ina dai so nasami sakamakon da nake bukata ne. Babu musu ta fara shiryawa aka dunguma zuwa asibiti.

11 October 2015 at 16:52 · Public
Save · More
Like
React
Comment
Share
Like26
Write a comment...

·
Salisu M. Mu'azu Dankado
Gud
Like · React · Reply · More · 12 Oct 2015
Ummu Khadijah Ummu Adnan
Weldon
Like · React · Reply · More · 11 Oct 2015
Asabe Ali
10x
Like · React · Reply · More · 11 Oct 2015
Abubakar Ibrahim
pls continue
Like · React · Reply · More · 11 Oct 2015
Usman Aliyu Taller
Nice
Like · React · Reply · More · 12 Oct 2015
Dauda Yahaya Masanawa
Madalla
Like · React · Reply · More · 11 Oct 2015
Adamu Safeeyarh
tnx
Like · React · Reply · More · 11 Oct 2015
Tahir M. Kaumi
Next pls
Like · React · Reply · More · 11 Oct 2015
Azinatu Umar
TNX
Like · React · Reply · More · 11 Oct 2015
Muhd Dawud Rano
Muna tare
Like · React · Reply · More · 11 Oct 2015
View more comments…
Free Mode See Photos
Facebook logo
Go To Home
Jamila Umar Tanko Books
DAME AKE ADO 4**9

daga karshe yace da hajiya batula dole sai sunje can asibitinshi anyi mata wasu gwaje gwajen. Hankalin hajiya batula ya kara tashi sosai ta dubi likita tace likita gaya min meke damun diyata? Cikin kwantar da murya likitan yace kwantar da hankalinki hajiya ba wani abu bane ba, ina dai so nasami sakamakon da nake bukata ne. Babu musu ta fara shiryawa aka dunguma zuwa asibiti, Acikin mota tayiwa Alhaji nura kwangila bayanin sun wuce asibiti, alokacin shi kuma yana cikin airport hankalinsa ya kara tashi kwarai da gaske amma ya dake. Dukkan gwaje gwajen daya kamata anyiwa nana, sai dai sakamakon ya dan girgiza likitan don haka yaja bakinsa yayi shiru don bai kamata ya sanar da mace wannan labarin ba. Ana kiran sallahr isha,i alh nura kwangila ya iso garin, kai tsaye asibitin dr musa ya wuce har dakin da nana take ciki lokacin anyi mata wata allurar barci idonta yana rufe, hajiya kuma tanayin sallah. Alh nura ya isa gadon da nana ke kwance ya tsaya yana kallonta sai kuma ya fara lalubar wayar Dr. musa daya tabbatar masa yana cikin asibitin sai ya fita ya nufi ofis dinsa. Yana shiga Dr. musa ya mike cikin girmamawa yana gaisheshi amma bai kula da wannan ba cewa kawai yakeyi Dr meke damun diyata me ya faru da ita? Dr. musa ya jinjina kai yace kwantar da hankalinka alh zauna na maka bayani.
Alh nura kwangila kamar bazai zauna ba amman dai ya hakura ya zauna yana kallon likitan. Dr. musa ya zauna ya dakko masa envelop a rufe kamar guda uku ya fara dubawa yana kallon alhaji nura wanda ya kagu yaji abinda zaice. Dr. musa ya fara bayani. Da farko na fara yiwa nana gwajin jini ne na tadda jininta ya hau........... Nanar me zai sanya jininta hawa kuma? Alh nura kwangila ya tambaya a gigice. Dr. musa yace wannan shine abinda ke bani mamaki. Sannan yanayin bugun zuciyarta ya sauya yana dudu fiye da yanda ka,idarsa take wannan dalilin ya sanya nace mu taho asibiti don ayi mata sauran gwaje gwajen, ga mamaki na sai naga zuciyarta ta dan sami matsala don ta buga fiye da yanda ya kamata ta buga musamman lokacin da ta fadi, Allah ya taimaka anyi gaggawar kawota asibiti da wani mummunan abu ya faru da ita. Hankalin alh nura kwangila ya kuma tashi yace. Abin mamaki meye zai sanya zuciyar diyata bugawa har akusa rasa rayuwarta? Kwantar da hankalinka alh, wannan ba wata matsala bace insha Allahu komai zai zama dai dai zata dawo dai dai musamman idan anyi gaggawar gano abinda ke damunta an kuma magance mata shi da wuri. Alh nura kwangila ya gyada kai yana fadin, na gode Dr. bari naje wajen mahaifiyarta. Ya tsare hajiya batula da tambayoyi, abinda ta fada masa yana can kafin yazo shi ta kara fada masa yanzu ma, dole dai su bari diyar tasu ta sami lafiya. Washe gari tunda safe Ahmad ya sami labarin abinda ya faru, hankalinsa yayi matukar tashi, don haka da wuri ya wuce asibitin ya tadda mutane anyi dandazo kama daga kan yan fadanci zuwa dangin hajiya batula dana alhajin, amma ba,a barin kowa ya shiga sai dai ko su gaisa da mahaifan nata ka juya ka tafi. Shima Ahmad din sun gaisa sai dai bai samu ganin hajiya batula ba tana ciki da yake dakin irin na masu kudine har da wani katon falo. Nana tana barci kamar cikin mafarki ta dinga jin muryar Ahmad. Nana tana bacci kamar cikin mafarki ta dinga jin muryar Ahmad lokacin da yake sallama da alh nura kwangila. Da sauri ta bude idonta ta kalli mahaifiyar ta da ke zaune a kusa da ita tayi tagumi cikin sanyin murya tace mummy ba Ahmad ne yazo ba? Hajiya batula tace bansani ba ko kinason ganinsa ne? ta gyada kai alamar eh da sauri hajiya batula ta mike ta nufi falon. Alh nura ya kalleta da sauri ganin ta fito arude yace yaya dai lafiya hajiya? Cikin karewa mutanen wajen kallo tace nana ce tace taji kamar muryar Ahmad wai. Ba wai bane shine yanzun nan ya fita bari na kirashi idon tana son ganinsa ne. Ya dauko wayarshi ya fara neman layin Ahmad bugu daya ya daga har ya tayar da motarsa, amma yace masa ya dawo maza maza nana nason ganinsa. Gaban Ahmad ya fadi yaji kamar kada ya koma din, amma bazai iya kin zuwa ba, don haka dole ya fita daga motar ya nufi dakin gabansa na faduwa yana ta addu,a a cikin ransa. Kai tsaye Alh nura ya shige dashi cikin dakin da nana ke kwance , mutanen dake zaune agurin suka dinga mamakin irin matsayin da Ahmad yake dashi a gurin Alh nura kwangila din daya samu shiga gurin nana. Nana ta kurawa kofar dakin ido dai dai lokacin da Ahmad ya shigo sukayi ido hudu, tayi doguwar ajiyar zuciya murmushi ya bayyana akan fuskarta. Ahmad ya matsa kusa da gadon nata ya tsaya da damuwa akan fuskarshi yace sannu hajiya nana, yaya jikin? Tayi murmushi da sauki nagode da kazo dubani ka kula da komai kafin na koma. Azahiri kowa zai zaci tana magana ne ko taso ganinshi don kamfani da gaske sai dai kasan zuciyarta tayi hakane don ta ganshi kawai. Alhaji nura kwangila da hajiya batula suka kalli juna da mamakin abinda tace.

Surayya

11 October 2015 at 18:02 · Public
Save · More
Like
React
Comment
Share
Like26
Write a comment...
Chapter 36 · 0% Book details