← Book details Dame Ake Ado Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 49

Sashe 6

Dame Ake Ado Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

rawar murya tace Raliya Raliya ce tashiga dakin sisko suka mike atare arude suna fadin Raliya zomuje saidai wani Abin bakinciki sanda suka isa kofar shagon suka hango cincirindon mutane ashe wani saurayi yaga sanda tashiga darufe kofar da akayi ya gayyato wasu matasa aka balle kofar dakyar suka barta tadaura zani suna mata ihu suka fito da ita tanufi hanyar gida tana kuka shikuwa sisko rufeshi sukayi da duka Ahmad da musa suka isowurin cike da bacinrai tundaga nan suka zare belt dinsu suka fara narkarta tana ihu tanufi gida da gudu Ahmad yarufamata baya shiko musa takaici ya isheshi yaga garayaje yakoyawa sisko hankali tashiga gidansu dagudu tana ihu daga itasai daurin kirji yankayanta data dauko duk tawatsar dan zafi duka yabita hargidan nasu yana dukanta tana ihu lami tafito daga daki arude tana fadin meyene yake faruwa tatsaya turus ganin Ahmad nadukan Raliya har cikin gida wata zuciya ta ciyota ta isa dasauri 3⃣5⃣ ta angajeshi tana fadin shege dan iska mediyata tayimaka dazaka biyota kana dukanta tamike cike damamakin ganin diyar tata daga ita sai daurin kirjg Ahmad yamike yataso daga cikin kwanikan wanke wanke data hankadashi yana karkade jikinsa ya isa kusa da ita yana fadin inna wannan yarinyar yau ta tona asirin gidannan ta tozartamu ashagon sisko aka kamata yara suka rakota suna mata ihu meyafi wannan takaici da tozarta sunan gidannan yakarasa maganar da kunan rai Lami takalleshi cike da wani irin bakin ciki data kasa rikewa tace Ahayye yaufa karin maganar hausawa tafito SHEGE YANA YI DAMAI ZINA don ankama Raliya ashagon sisko zaka biyota kana mata wannan dukan kaine kafi cancanta da adaka ba Raliya ba Shege irinka ne zaitonawa maiyin zina asiri cikin tada jijiyar wuya take magana musa dayashigo bakomai ahannunsa ya isa cike da bacin rai dadamuwa ganin yanda Ahmad ya tsaya sororo yana kallonta cike da madaukakin mamaki donshi sam baifahimci tana daurewa diyarta gindi ne akan abin da ta.aikata musa ne yace haba inna baidace kidaurewa yarinyar nan gindiba har kidinga ciwa Ahmad mutunci ba kai rufemin baki da.ace kai ko Auwalu ko sani suka kamo yarimyar nan dawani banzan damuba tunda ku kowa yasan "ya"yan halak ne ba shegu ba amman wannan yaron shege ne zai aibata diyar da akahaifa tahanyar Auren sunna ta Nuna Ahmad gaba daya suka tsaya suna kallonta cike da fargaba tashin Hankali musa yafara magana cikin kaduwa da gigita inna kazafi baida kyau kada tunanin nemawa Raliya kariya yasanya kifita daga haiyyacinki harkije ki fadi abinda baidaceba ninasan Ahmad dan gidan baffa sulaiman ne kuma...... Kai tafi can toyau zanfasa kwan da.akajima ana kiwonsa yau zansanarda kai abinda bakusaniba saunawa nake gayamuku kudaina damuwa dan Ahmad yafiku wani abu kasha damuwa danyafika kokari kasha damuwa danyafika kaya nasha gayamaka duk dayafika aikin banza ne tunda ku kunada abin ado wato uba shikuwa shege ne dan mahaukaciya wacce ba.asan daga inda ta fitoba ........ Innalillahiwainna ilaihi rajuun lahaula walakuwati illah billah muryan Ummansu Deeje ta ankardasu wacce ta shigon gidan gigice jiyo hayaniyar da akeyi taleko taga abinda ke faruwa Ahmad kam mutuwar tsaye yayi yakasa motsawa daga inda yake tabbas yasha tunanin maganganu Lami dake fada akansa Ummansa da Hjy Amina suna tauye masa tunaninsa wannan ne yasanya hankalinsa ketashi aduk sanda sukaji ance masa shege faduwar da Ummansa tayi jib dafasa ihun ma.u ne yadawo dashi cikin hayyacinsa Yanufeta da gudu kamar yanda yaga musa yayi idonta yabirkice yajuye da alama banumfashi a tattare da ita cikin karaji ma.u kefadin umma kada kimutu kibarmu dan Allah Umma kitashi shikam gaba daya tunaninsa da basirar sa suntushe yakasa cewa komai sai hawaye da idonsa keyi musa ne yamike dagudu yadebo ruwa abuta ya yayyafa mata amman abanza bata ko motsi sai asannan ya iya bude baki yana fadin Umma kada kimutu kece Uwata maisona idan kika mutu zankasance banida kowa kitashi Umma kici gaba darikeni a matsayanin danki na cikinki kada ki mutu Umma na yana kuka da majina yake wannan magana musa ne yayi dabara fita dagudu yanufi gurin Auwalu dake chemist wanda bai san wainar da ake toyawaba Lami kam tayi tsuru tsuru tsaye da fargabar da tashin hankalin abinda zaije yazo Raliya kam sai sharbar kuka take yi cike da takaici da dana sani Auwalu yashigo aguje hannunsa rike da fanfon auna jini ya isa gurin mahaifiyar tasa yahada bakinsa danata yafara bata taimakon gaggawa da ake kira da mouth to mouth yatallafo kanta cikin ikon Allah saiga numfashin nata yadawo tabude idonta dasauri saita mike zaune kamar ba itace tasuma ba yanzu takamo Ahmad tana fadin karya take nice nahaifeka ba mahaukaciya ba ranar dana haifeka ne tazo nan gidan katambayi malam kaji ainasha gayamaka Lami makaryaciyace tana kuka take maganar shima Ahmad kuka yakeyi Auwalu da baisan abinda ke faruwa ba yamike cike da mamaki yana fadin wai meye yafaru me yasameki Umma? Arude yake maganar saita mike cikin karfin hali tana fadin babu komai kuzo muje gida banason kara kallon fuskar Azzalumar matarnan tanuna Lami da hannunta Ahmad yarirriketa dakafarsa suka nufi gidansu harlokacin musa Ahmad da ma.u kuka suke Lami ji take yi kamar maganar tadawo tamaidata cikin ta donbatasan abinda zaibiyo baya ba amman saboda tsabar taurin rai saida taga sunfice eh gaskiya ce nafada sai dai Akasheni wallahi haka kawai shege zaitonawa diyata Asiri yanda yatona m ini asiri nima natona masa 3⃣7⃣ koda suka iso gidan abin datake maimaitawa kenan Auwalu yace Umma mema tacene? Meyafaru ne? Cikin kuka tace Azzalumace Lami waicewa tayi Ahmad shege ne bayan nice nahaifeshi da cikina cewa tayi dan mahaukaciyane bayan gashi dana ne ranar dana haifeshi ranar mahaukaciya tazo nan gidan bari kuganima na dauko muku takaddar dazaku san danane saita mike jiki yana rawa takama lalube saidai abinda batasaniba shaidar datake son kare ta itace zata kara sanyawa abin yafito fili tunda duk mutumin dayakasance danka dakahaifa aibabu bukatar wata shaidar takarda arubuce gashi ita batasan abinda akarubuta na yarjejeniya bace baiwar Allah saida tafito dakayan wata tsohuwar adaka sannan takwakulo wata takarda acan kasan jikinta yana rawa tamikama Ahmad tana fadin karanta kagani karya takeyi nice babarka ya.amsa yafara karantawa bawani abu Acikiba illah yarjejeni sun amsheshi zasu rikeshi kuma duma duplicate ce aka basu da.alamu original din tana can inda suka basu shi kukansa yakuma karuwa hankalinsa yakuma tashi tabbas ba sune iyayensa ba Auwalu ya warce takardar yafara karantowa yakalli mahaifiyar tasu datausayi datashin hankali rashin ilimi datayine yasanya batasan Abinda takardar takunsa ba data sani data kara boye takardar cikin sheshshekar kuka yake fadin Umma wannan takardar tana nuna yarjejeniya dakukayi ne asanda zaku amshi wani yaro nasan ba Ahmad bane mantawa kikayi kika fito da ita sai asannan tagano wautar datayi amman taji dadin yanda Auwalu din yakawo mata mafita dasauri tace ahaf namanta wannan ajiya ce akabani bari nazakulo wancan bani na adana wannan din kafin masu ita suzo nema ta.amsa dasauri tanufi akwatin tana cigaba dalalube tsanananin tausayin dasoyaryar Ummansu tashigeshi yakula da idan baiyi wani abuba zata iya rasa hankalinta ko wani yashigeta yanufeta inda take tazakulo kaya daga cikin tsohuwar adakar yadafa bayanta yana kokarin kwantar mata da hankali yace Umma kidaina lalube nifa nasan kece mahaifiyata bakece kikasha gayamin innarsu musa karya ne da ita ba tayaya zanyadda damaganarta dake ba uwataba ce ba saikin nunamini watarana dakuma saiwani yayi mini gori acikin layin nan kishare maganarta ki kwanta ki huta tana son bata miki raine don ankamo diyarta dakin sisko suna iskanci tadago cike da matsananci farinciki tana fadin haba ainasan saboda mugunta take son rabani dakai tahadda samaka wani ciwon dazan rasaka bakayadda da abinda taceba kenan? Yadaga mata kai yana kokarin kakalo murmushi wannan yasanya tadan sami sassauci aranta daga wannan karon anyita takare ko ita ko lami dole dayan yabar gidan dakyar ta iya kyalesu suka tafi masallaci bada farali gani take yi kamar daga can bazata koma ganin Ahmad dinta ba saidai shi yana sallah yana kuka ransa yayi baki ashe shi yanata barankadama da homa ashe shi shege ne bashida kowa aduniya shin wacece mahaifiyarsa datayi shegensa koda yake ance mahaukaciya ce to waye mara imani dayayi mata ciki har kawo shi duniya 3⃣8⃣ tana ina ita mahaukaciyar ta warkene kohar yanzu tana cikin haukan? Yakasa natsuwa daga masallaci yalallaba yafice yayi gabas yana ta tafiya baisan inda zaidosaba Anshirya cin abinci yanda aka saba amman babu Ahmad tun Ummansu nasanya rai zaishigo har tafara karaya bacin rai datake kokarin boyewa yafara yabaiyana tadinga sanyawa ana nemansa sam tahana kowa cin Abinci nan malam yashigo cike da taikaci yana fadin wai Ahmad yaro ne dazaki sanya ayi ta wani nemansa saika ce wanda zaibata kinsa dai bazai wuce yana gidan yaron Abokinsa Abdullahi ba cikin sheshshekar kuka basan abinda nasaniba tabbas idan Ahmad bai bata ba to zaigudu kuwa saita fashe dakuka cikin mamaki yakd kallonta hasken wutar lantarki da.aka kawo yanafadin wace irin magana kike yi khadijatu kamar wacce tayi gamo memukayi masa da zai gujemu cikin kuka tace yau Lami tasanar da Ahmad shi shege ne tasanar da shi banice nahaifeshi ba tagayamasa shidan mahaukaciyane baniba... Kuka take yi sosai kamar wata karamar yarinya malam yamike cikin tashin hankali yana fadin mekikeson sanar dani khadija inanilillahi wainna ilaihi rajuun yanzu ina Ahmadu bari nanemoshi... Baijira yi jin abinda zatace ba ya fice sani da salisu da rabi.u ne agurin sunkuma riga sun fahimci abinda ake anufi saidai harkarfen dayan dare babu Ahmad babu labarinsa hankalin kowa yatashi sanda malam sulaiman yashigo gidan Umma Deeje tamike tana fadin yaya dai malam kungan shi yagirgiza kai cike da damuwa mai tsanani takuma wurga masa tambaya hargidansu Abdullahi mlm kunje munje taredashi muke ta nemansa ma yanzu haka nabarsu shida Auwalu suna ta bin gidajen Abokanansu Akanme zaku wahalarda kanku wanda yabata ake nema bawanda yagudu ba Ahmad bazaije inda zaku ganshi ba abinda najima ina nusar da kai kenan wlh Lami bamasoyiyar mu bace ko Ahmadu yadawo ko baidawoba nagama zama a gidannan yanda Ahmad yatafi haka nima zatasalwantar min yarana tana magana tana kuka ya hasala matuka gaya yama rasa hukunci dazaiyanke sai kawai yamike cikin fushi yanufi gidansu Lami Yanashiga yakama kwada sallama kamar zaitsaga gidan dafarko sunyi shuru adaki don lami tagayamasa tabargazar
Chapter 6 · 0% Book details