← Book details Dame Ake Ado Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 49

Sashe 7

Dame Ake Ado Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

dayayi duk da lika abin asharri yayiwa diyarta ammam duk da haka mijin nata yabata rashin gaskiya don yana tsoron abin da zaije yazo can dai sai ga mlm jibiril yabayyana cike da tsoro mlm sulaiman yagalla masu harara yana fadin Barkanku Ahmad yagudu yabace mana yarabu da mu saidai kusani jibril yanda Ahmad yarabu damu tokaima karabu da komai nawa kashirya kayanka agobe zansanya gidan kasuwa tunda dai zamanmu tare baida Amfani sai haddasa masifa nima nahakura dazaman gidan gabadaya hankalin jibril yatashi idan yarabu dan uwansa inazaisoma rayuwarsa waye zai iyaciga dabashi taimakon dayake bashi tabbas shikansa yanzu lami ta isheshi yabi dan uwansa yana bashi hakuri amman ina tuni yafice yadawo tsakar gidan yayi duru duru cike da tashim hankali saiyafada dakin dasauri yatadda lami zaune tayi wuki wuki tana zare ido yana shiga tafara magana ka kwantar da hankalinka malam indai akan gidane muje mukama haya tunda ai....... Rufemin baki munafuka sau nawa nake cemiki kicire hannunki daga kan maganar yaran nan yaji koshi waye aduniya amman saida kika fadamasa to tsaya kiji banida wani gata dayawuce na Allah da dan uwana daya daukoni daga cikin wahala yanemo mini aurenki yaci gaba da dawainiya dani kisani idan na bar nan banida wurin zuwa don haka kedai da kika janyowa kanki kece zakibar gidan dolenki kuwa takalleshi damamaki matuka tana fadin malam akanfadin gaskiya kake wannan furucin kinga banja dagon zance dakeba kiwuce kawai nasakeki yana kaiwa nan ya fice daga dakin .......4⃣0⃣ Lami tafashe da kuka tana fadin na shiga ukku yanzu akan dan shege har akasane natsani wannan yaro daman nasan zuwanshi gidannan Annoba ce kuma harzuwa yanzu banyi nadamar fadin cewar shi shege neba dawannan tadinga sambatu tana kuka Sunwayi gari cikin tashin hankali kam tun Asuba tabar gidan saboda yanda jibril ketayimata kwakwazo hankalin yayanta yatashi matuka musamman Raliya da Amina musa kam yanajin ciwo sakin mahaifiyar tasa Amman yanajin takaicin Abinda ta.aikata gaba daya gidan angaza karyawa kowa yanacikin damuwa ma'u kam kuka takeyi tana fadin danasani dabangayawa yaya Ahmad abinda raliya keyiba duk da deeje tana cikin tashin hankali hakan baihanata rarrashin diyar tata ba tunda suka dawo daga masallaci jibril yatare malam yana kara bashi hkr dasanar dashi hukunci daya yanke tun dare jiya malam sulaiman yakalli dan uwansa cike da tashin hankali yace subhanallahi meya sanya ka.aikata haka nima bacin raine yasanya fadin abinda nafada kayi hakuri da abinda nayimaka dankai dan uwa nane jinina daban isa nasakakaba Dejee kam bataji ko dar da mutuwar auren lamiba tunda tarasa danta komaima yafaru wajen misalin karfe goma sai Hajiya Amina ta iso akidime don yan dubo Ahmad sun iso hargidanta duk yanda deeje kekorin taddanne zuciyarta saida ta fashe dakuka ganin hjy Amina tana fadin yagudu hjy bamusa inda yashigaba danasani munbakishi ina zankai hakkin yaron nan tadafa kafadarta cikin kwantar da murya take fadin kidaina wannan maganar deeje ko ina yake aibazaiwuce kaddararshi ba Nakuma tabbata duk inda Ahmad yake zaidawo inda kuke muyi Addu.a kalaman hjy ne suka dan kwantar mata da hankali tace kuma adaina zuwa nemansa zaidawo dakanshi tasoyin maganin lami saidai tasamu lbr sakin da.akayimata kwanaki ukku suka cika cikin tashin hankali abincin kirki babu maici agidan Ranar kwana na hudu datafiyar tasa ma.u tadawo daga kai markaden gero na kokon da yamma sakaliya tana tafe tarera wakokinta tahangoshi tafe da kayansa tunna ranar dayatafi yarame yayi duhu dakyar yake tafiya kamar me ciwon kafa batasan sanda ta watsar da robar markadan ta falla gida dagudu tana fadin Umma gayaya Ahmad umman dake tukin tuwo tafito da.azama jikinta sai kyarma yake harzaninta yana neman faduwa darawar baki tace A ina kikanshi gashinan zaishigo gidannan yashigo gidan dasallama 4⃣1⃣ yatsaya turus cikeda farin ciki ganin ummansa itama tsayawa tayi turus tana kallonshi kuma kome tatuna saita nufeshi da sauri ta wanka masa mari sai kuma tafashe dakuka tajuya gida da sauri ma.u dake tsaye ta zuba masa ido wanda ya ciko da kwalla shima idon ya zubamata yana hawaye shida kansa yasan abin da yayi bai kyauta ba cikin kuka tace yaya Ahmad mai yasanya ka gudu ka barmu Umma ta daina bacci tadaina cin Abinci baba yadaina fita kasuwa yaya Auwalu yadaina zama a chemist sani yadaina zuwa kasuwa ni idan akaturani makaranta bana zuwa sai intafi nemanka ranar har gwammaja naje dakafuna nemanka memukayimaka kagudu kabarmu yakamo yarinyar maicike dawayo ya rungume yana kuka yafadin ba gudowa nayiba tafiya nayi nasamu natsuwar zuciya ta saidai bansamuba zama daku shine nutsuwar zuciyata yamike hannunta suka nufi cikin gida saidai duk yanda yaso yayi wa Umma magana taki sauraronsa tayi fishi dashi maitsanani wanda yakara tada masa hankali Malam sulaiman yagyara zama yana fadin tabbas hjy Amina tayi gaskiya tace mini Ahmad bazai iyabarinmuba munyi masa rikon dako mahaifiyarsa ce tadawo duniya bazatayimasa irinsa ba saidai nayi mamaki dakabarmu Ahmad shinkanaganin kayimana adalci yadukar dakai cikin kuka yake fadin kuyafemin baba tabbas nasan na.aikata muku laifi mai girma wani irin tausayi yakama malam mai tsanani shikadai yasan Abinda yakeji Azuciyar sa game da yaron 4⃣2⃣ kwanaki sunja ga Lami tun tana ganin abin kamar wasa har karamar magana tazama babba domin sam mlm jibril yaki zuwa biko sai abin yazamomasa kamar gaba takaishi domin daga gidan yayansa yayansa akefitomasa da girki maidadi wanda yafi namatar sa Su raliya kam kullum saita saci jiki ta tafi gurin uwarta suyita ta kitsa mugunta dadai lami ta kula abin bana wasa baneba hankalinta yafara tashi ga wahalar gidan tafara damunta da yunwa don haka tafara bin kan mahaifinta ABDULLAHI YUSUF MAITAMA 09034598552 @whatsapp
Chapter 7 · 0% Book details