← Book details Dame Ake Ado Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 49

Sashe 24

Dame Ake Ado Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

· Rahma Hussain Mai Doki Thanks Like · React · Reply · More · 30 Apr 2015 Ra'idatu El Kabeer Tnx Like · React · Reply · More · 30 Apr 2015 Sa'adatu Ibrahim Panda tnx Like · React · Reply · More · 30 Apr 2015 Kabiru D Shagari Tnks. Like · React · Reply · More · 30 Apr 2015 Azinatu Umar TNX Like · React · Reply · More · 30 Apr 2015 Siyama Auwal munajin dadi Like · React · Reply · More · 30 Apr 2015 EL-Mansoor Mancy Dulo 10nks u Like · React · Reply · More · 30 Apr 2015 Shahara Na Suleiman Good Like · React · Reply · More · 30 Apr 2015 Aliyu Ibrahim Tanxx Like · React · Reply · More · 30 Apr 2015 Mukhtar Moh'd Mopol Muna godiya Like · React · Reply · More · 30 Apr 2015 View more comments… Free Mode See Photos Facebook logo Go To Home Jamila Umar Tanko Books DAME AKE ADO part 16. Inaji ajikina aikin danakeyi yanacikin kaddarata sukuma wadanda basu samu ba hakan aka rubuta alittafin kadararsu dan haka zaka iya yanke kowane irin hukunci akaina babu tsoro balle fargaba Ahmad yasake fadar maganganunsa manaja yakara fusata dajin abinda Ahmad din yafada masa batare dawani shakkarsa ko fargaba ba gurin kowa yayi tsuru tsuru cike da tsoro masamman isuhu abokinsa manaja yanuna Ahmad da dan yatsa cikin tsananin fushi da fusata kaikada kasake kayiman rashin kunya daman najima daganin take takenka dan matsiyata ba,za...........kai manaja dakata Alhaji nura kwangila yadoka masa tsawa jikin manaja yadauki rawa yaguntse baki da sauri domin yau dai asirinsa yatonu duk yanda yaso kuma yakare abin yafaskara Alhaji nura yana huci yakalli ma aikatan yace Acikinku waye yasamu manaja damaganar yanaso abarshi anan idan har za adinga bashi alawus din dazairika aikawa iyalinsa? Kowa yayi shiru ana kallo kallo manaja yafara hada gumi jiyake kamar kasa tatsage yashige cikinta saboda tsananin kunya Alhaji nura yabisu da kallo daya bayan daya yace babu sukayi shiru wanda yatabbatar masa da babudin yakada kai cikin takaici Nayi matukar bakin ciki da manaja ya aikata wannan zalunci da sunana tun lokacin dakuka wata ukku nasameshi damaganar komawarku ga iyalinku idan kuma da maibukatar zama ana legas yacigaba zamansa amman sai mutumin nan yace min aiduk kunce anan zaku zauna indai za adinga baku alawus kuna turawa iyalinku nace yaware wasu kudi yadinga baku dukkan sati ashe karyace yashirya min bahaka bane gaskiyar lamarin ba naji dadin wannan maganar dakayi Ahmad inason mutum irinka dabayajin tsoron fadin gaskiya duk dacinta kai manaja katafi gida nadakatar dakai tsawon wata ukku babu Albashi mataimakinka zaimaye gurbinka!!! Kukuma dukan maibukatar tafiya gida saiyafara shiri cikin satinnan saikuwuce sannan albashinku yana nan yanda yake dakarin danayimuku nagode manaja yadafe kai da tsananin tashin hankali dakatarwa wattani ukku babu Albashi dame zaidinga ciyarda iyalinai har wannan lokacin balle kuma kudin dazainemi mata domin duk abinda yake samu jikin matan banza yake karewa Ahmad kam yafi kowa farin ciki saigashi yafara shirya jakarsa domin babu komai acikinta sai tsarabar kayan ma'u isuhu yana zolayarsa yanda yayi magana da babban manaja babu tsoro mutumin da kowa yakejin tsoronsa da shakkarsa baisanarda kowa zai komo cikin satinba domin yanaso yayi musu bazata ne kawai Ranar assabar da daddare suka bar garin legas wajen karfe tara da rabi nasafe suka iso garin kano motarsu natsyawa yaji wani farin ciki yacikashi aranshi umma da ma'un sa kawai yake son gani yana kokarin shigowa gidan yaci karo da Amina kanwar raliya taci kwalliya tayi bilicin kamar wata karuwa gabansa yafadi domin kallota da kamannita sun tunomasa da raliya gabadaya takoma kamar raliya cikin rawar baki tace masa Ahmad sannu da zuwa batare da ya kalletaba ya amsa da yauwa yashige ciki dasaurinsa tabishi da kallon mamaki baki abude gaba daya yasauya yakara haske da kayau kamar bashiba saitakoma ciki dasauri domin tabaiwa babarta labari itada kullum take addu a Allah yasanya jirgin kasa ko mota yatakeshi yamutu koyanfashi sutaresu su harbeshi domin tafara kishi daganin yanda ma'u take komawa kullum kuma agidan ba ada magana saita Ahmad saikace shikadai da aduniya ma'u tana durkushe tana wanke wanke da T. Shirt ajikinta da dogon siket tana yar wakarta tajiyo sallamar Ahmad tadaga kai dasauri da mamaki saita fasa ihu dajindadi tana fadin yaya Ahmad dagaske kaine dan Allah tawurgarda kwanon dake hannunsa tanufeshi dagudu ta kankameshi tana ihu umma dake kicin tajiyo tafito fasauri ta leko dadi damamaki yacikata tayi wurgi da ashana tana fadin Ahmadu kaine da tsakiyar ranar nan kesakeshi mana kinbi kin kankameshi kamar zaki kadashi kunya takama ma'u tasakeshi dasauri shi kam ji yayi kamar sudauwama ahaka 1⃣5⃣ DAME AKE ADO 3 Amman dai yadake ya ajiye jakar hannunsa dasauri ya isa ga ummansa yadurkusa yana gaisheta umma tadinga kallonsa cikin farinciki dajin dadi tana amsawa jitakeyi kamar tagoya shi abayanta don dadi ma'u kuwa tsaye tayi tanata kallonsa gaba daya yayan nata yasauyamata yini akayi damurnar dawowar Ahmad su ma'u ankulle cikin daki sai hada kaya takeyi gaba daya zaman gidan umma datake doki yanzu ya isheta domin shagwabar datakeyiwa umma da yanzu duk tadaina kuma tanason gwada irin abinda take koyo alittafi agidan mijinta musamman girke girke data kware yanzu akanyinsu umma tashigo dakin daukar wani abu tahango ma'u anata hada kaya dariya taso kwace mata amman saitadake tace Asma'u menene kikeyi haka kuma? Babu kunya tace Umma kayana nake hadawa koba yanzu zamu komabane ? Umma tarike haba damamaki tana kada kai Au har zaman gidan namu ya isheki kenan? Ma'u tarufe fuska kunya takamata tana dariya umma tayi murmushi aisaiki huta da hada kaya domin bayau zakukomaba saigobe anje angyara gidan tafice tabarta murnar ma'u takoma ciki taturo baki gaba shikansa Ahmad abinda yake bukata kenan yakoma gidansa yakebe damatarsa kohira suyi amman yaya ya iya da hukunci ummansa dole yayi shirin kwanciya adakin gwaurayen gidan amman ba sukwanta da wuri ba anatashan hira dasafe kamin kowa yafito ma'u tasalara wankata sanda umma tafito domin dama koko taci karo da ita anata shafa hoda da fesa turare umma tatabe baki nashiga ukku Asma'u badai nan shirin tafiya gidan mijinki kikeyi haka da sassafe ba? Malam yadaga labule yana kallonsu bayan yadawo daga masallaci yayi murmushi tolaifi tayi kenan kefa kikaimata gori kullum yaukuma saikidamu Amman dai tabari ayi karin kumallo ko? Shima Ahmad tun da sassafe yashirya yabaiwa kowa tsarabarsa sai tamatarsa kawai yabari acikin jakarsa Umma da malam sunata zolayar ma'u da Ahmad dasuketa hada kayansu suka fice suna dariya shatar mota taxi suka dauka har kofar gidansu gidan yayi futu futu cike da tsananin kura kamar anyi shekara ba ashiga cikiba ma'u tacire gyalenta tasakale ajikin igiya tafara karewa gidan kallo tana tunanin ta inauadace tafara gyarawa ne? Ahmad yabita da kallo tunda yadawo yake mamakin irin girma da cikar da ma'u tayi saikace yayi shekara rabonshi da ita kamar ance takalli inda yake tajuya tanafadin yaya ta ina zanfarane takasa karasa maganar saboda irin kallon dayakemata tadauke kanta dasauri domin yamzu tasan irin ma anar kowane irin kallo shima yadanji kunya amman saiya dake yace wannan aikin yafi karfinki kekadai ma'u dole saina taimakamiki bari kigani saiya fara kokarin cire kayansa yana ajiyewa shima akan igiya yarage daga shi saigajeren wando da singileti tasanya hannu suka cigaba da aikintare saikarfe hudu sannan gidan yadawo hayyacinsa yanda suke bukata sunyi butu butu da kura shiya fara shiga toilet yayi wanka bayan yafito yasanya kayan da yabari akan igiya yafice domin yaje yasiyo musu take away saboda yamma tayi babu damar yin girki ayanzu yana fita itama ma'u tafada wanka bayan tafito tafara gyara jikinta dayin turare masu kamshi domin Umma wannan karon batayi sanya gurin hada mata kayan kamshi da gyaran jikiba wata kila tahimci har lokacin ma'u budurwa ce ita kamin kace wani abu gidan ya dauki wani irin kamshi maidadi dasanyaya zuciya tafara duban kayan da yayan nata yakawo mata tsaraba dukansu kananan kayane saikuma rigunan bacci saikuma kayan gyaran gashi kala kala da mayuka komai maikyau tasan yayan nata danayune amma batayi tsammanin ya iya zabe kamar hakaba saiyanzu da idanunta suka ganemata tama rasa wanne kaya yakamata tasanya domin kowanensu yanada tsananin kyau daga karshe dai ruwan idonta yakare akan wani dogon siket mai roba da alama idan akasanyashi zaikama jikin mutum rigar kuma maikama jikice kwarai dagaske koda tasaka kayan sun Amsheta kwarai da gaske kitson kanta shikune don haka yadace da kwalliyarta kasancewar tanada gashi tayi dauri dawani gyale kitson yafito tatsakiya yasauka abayanta tasanya wani dogo dankunne wanda shima yanadaga cikin kayan dayayan nata yasiyomata bayan tagama tsantsara kwalliya takoma falo tana kallo domin ankawo wutar nepa alokacin saibayan sallar magriba Ahmad yashigo gidan domin yabiya tawurin abokinsa ishak sungaisa sannan yayi yanbiye biyensa dai bata damuba domin bayan kallon datakeyi yan matan unguwar su A'ilo sunata shigowa dagaisawa suna murnar dawowarsu kaitsaye falonsa yanufa domin can yaji motsinta baifita da babur dinsaba domin yasan shima yana bukatar gyara saiwashe gari zaikaishi aduddubashi tukunna hakan yasanya ma'u batasan yadawoba saida yashigo dasallama tadago kanta dasauri ta kalleshi saitamike daga zaunen datake tanufeshi tanafadin sannu dazuwa yayana ta amshi kayan dake hannunsa tanufi cikin daki domin ajiyewa Ahmad yabita!da kallo komai najikinta juyawa yake yabude baki saikace wani sauna ANYA KUWA WANNAN MA'UNSA CE BASAUYAMASA ITA AKAYIBA ? Batasan yanayiba harya isa yazauna jikinsa yayi sanyi abinda yakeji gameda ita yadinga dawo masa ko acan legas yayi fama da irin wannan matsalar saidai yadinga dagewa da addu'a donkada shaidan yayi galaba akansa komai na ma'u yasauya cikin dan wannan lokaci kodayake kokamin yatafi yafara fuskantar wasu yansauye sauye atare da ita amman basu kai nayanzuba tamike tashiga kicin tadauko babban faranti tajuye musu Abinci dayayimusu take away takawo gabanshi ta ajiye yaya sauko muci nifa yunwa nakeji yasauko yanafadin nima haka Amman dai abaki zaki bani ko mamata? Tayi dariya takauda kai kunya tarufeta azuciyarta cewa tayi mezaihana nabaka nagwada yanda Alhaji bashir yayiwa fauziyya akanka ( TACIKIN LITTAFIN SAWUN GIWA) Amman afili bazata iyaba yayi murmushi yafara cin abincinsa yadinga janta dahira yanabata lbr abinci ikko itama tanabashi lbr abubuwan dasuka faru ahaka harasuka kammala cin abincin dukkan hankalin Ahmad yanakan ma'u ayau
Chapter 24 · 0% Book details