← Book details Dame Ake Ado Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 49

Sashe 44

Dame Ake Ado Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Alhaji Nura ya mik'e yana musmushi ya ciro Hoton Asma'u wanda take mace ya nufi Alhaji Abdullahi da shi ya nuna masa ya ce, Yaya ka shaida wannan wace ce? Alhaji Abdullahi ya kar6i Hoton ya k'ura masa ido, sai ya hau Salati yana fad'in, Subhanallahi! Wannan ai Asmu'u ce Nana Ma'una ce!
Hajiya Ruma ta mik'e da gaggawa ta amshi hoton, sai ta koma ta zauna tana salati tare da fa'in, Nura ina ka samo Hoton Gawar Asm'u, Yarinyar da aka ce mana ta rasu cikin Mota ta k'one k'urmus! ko Tokarta ba asamu ba?" Alhaji Nura yayi murmushi yana kallonsu ganin duk sun gigice sannan ya fara basu labarin abinda ya faru da Asma'u da d'an da ta haifa har zuwa yau. Yana kaiwa k'arshe Alhaji Abdullahi ya kalli Ahmad ya ce, Wlh wannan shi ne d'ana! kai jinina ne!! Zo nan na rungumeka naji dad'i don Allah!!!" Ahmad ya mik'e da sauri yaisa ga Mahaifinsa ya d'ora kansa bisa cinyarsa yafashe da kuka yana goge kan kamar wani k'aramin yaro. Alhaji Abdullahi ya shafa kansa yana hawaye shima. Ahmad ke fad'in, ashe inada Iyaye masu daraja haka na dinga shan gori da hantara sboda rashinsu? Ashe nid'an gatane gaba da baya? Amma na godewa Allah da Ya sanya Iyayena dana rayu a gurinsu basu tagayyara rayuwata ba! Na godewa Allah da ya had'ani daku sanda nake tsananin buk'atarku. Maganganunsa sai da suka dinga sanya kowa kuka.
Alhaji Abdullahi yace, Ka daina kuka Ahmad, wallahi ban ta6a jin dad'i da jin jinin jikina yana tafiya dai-dai kamar na yau ba. 'Dana ina jin kamar zan iya mik'ewa tsaye yanzu, kamani na gani zan tashi, domin naji kamar na warke babu rauran wani ciwo a Jikina! Ahmad ya mik'e da sauri ya kama Mahaifin sa, sai ya mik'e tsaye da k'yar! Amm ya kasa tsayuwa sai ya kwanta jikin d'an nasa yana fad'in, ashe zuciyata ce ta mik'e ba gangar jikina ba, Nayi zaton na tashi daga yau. Alhaji Nura ya isa kusa da shi ya kamoshi zai zaunar da shi, sai Ahmad yace, "Barshi Kawu zan iya. Wannan kama da ya gayawa Alhaji Nura Kwangila ya sanya shi jin wani irin dad'i da nishad'i. Yace, "Lallai yaya yanda zuciyata ta warke insha Allahu k'afafuwanka ma zasu warke da yarda Allah. Hajiya Ruma da Ma'u sun kasa koda mutsi sai hawaye. Ita kuwa Nana kallon Ahmad kawai take yi da jin dad'i. Dukkan sakwan sonshi na k'ara shiga ranta. An jima ana hira Sallah ce kwai ke tashinsu, sai da dare yayi sannan kowa ya nemi Makwancinsa. Alh Abdullahi yana jin kamar ya lashe Ahmad da Iyalans. Hajiya Ruma kuwa ta rik'e Ma'u katamau a jikinta suna jin kamar su cinyeta saboda kasancewarta Mata mai son d'ansu, don Ahmad ya basu labarin irin son da Umman Ma'u da Iyalin Gidanta ke masa. Sai dare kowa ya nemi makwancinsa. Cikin gidan nan kowa ya koma sashinsa da yake babban Gida, Ahmad ba zai iya rabuwa da Ma'unsa ba, don haka sashi d'aya suka d'auka, amman yaran runa gurin Hajiya Ruma, amman yini suke yi gurin Alhaji Abdullahi. Su kansu Likitoci sun yarda Alhaji Abdullahi ya sami lfya, daman sun san ba ainahin Ciwonshi ya hanashi tafiya ba sai bak'in ciki da CIWON ZUCIYA ne wacce ta warke yanzu garas! Babu sauran rauni a tattare da ita. Kafin sati guda sai ga shi ya fara k'ok'arin mik'ewa tsaye. Ahmad ya maida rayuwarshi gaba d'aya ga Mahaifinsa yana taimakmsa, shi ke yi masa komai, wanda hakan kullum ke k'ara faranta masa ranshi yana sanyashi nishad'i da sa samun suk'i, Ga Ma'u kuwa, tun bata sakin jiki da Nana har ta hak'ura ta sakar mata. saboda yanda take k'aunar 'ya'yanta da janta a jikinta, da taga kuma kowa ya gane tana kishin mijinta ne, bayan ko babu komai k'anwar Ahmad ce wacce ta dalilinta Mijinta ya gano dansa. Kuma taga babu wani aibu na soyayyar da Ahmad ke yiwa Nana, ko ita keyi masa, hakan ya sanya ta ga babu amfanin cigaba da shariyar. Nanan ce ta dinga janta zuwa Harami suna Addu'a da Salloli. Cikin zuciyar Nana Addu'a take yi akan Allah ya sassauto zuciyar Ma'u ta bata aron Mijinta ko da sau d'aya ne cikin sheka. Ita kuma Ma'un godiya take yiwa Allah bisa rahamar da yayi musu. Wai yau ita ce a gaban 'Dakin Allah mai girma, ne yafi wannan dad'i? Satin su uku suka fara shirin komawa Nigeria, amma Alhaji Abdullahi da Hajiya Ruma suka dage suma sun gama zaman Saudiyya tunad mai jinyar ya sami sauki yanxu har yana tafiya da sanduna biyu irin na masu kud'in larabawa, don haka tare suka tattara suka dawo Nigeria.
Dayake Alhaji Abdullahi yana da Gidanshii bai sauka a can ba, sai ya sauka a Gidan d'an uwanshi aka bada umarnin a gyara mashi nasa. Cikin kwanaki biyu aka sauya komai na Gidan, xa koma sabo dal! hatta Fenti suka koma shi da Mahaifiyarsu da masu Aikinsu wad'anda daman dasu suka tafi can K'asa mai Tsarki (Saudiyya). Lokacin da aka had'u da su Malam Sulaiman da Alhaji Abdullahi kuka kawai Alhaji Abdullahi ya fashe da shi, don ya rasa bakin da zai yi godiya gasu Malam Sulaiman, k'arshe yace dole zasu bar wannan Gidan nasu cikin sati guda su koma wani sabo cikin rukunin Gidajen da ya gina.

26 October 2015 at 11:15 · Public
Save · More
Like
React
Comment
Share
Like37
Write a comment...

·
Muazz Alawo
tnks
Like · React · Reply · More · 26 Oct 2015
Salisu M. Mu'azu Dankado
Gud
Like · React · Reply · More · 27 Oct 2015
Khadija Mohammed
Tanxs
Like · React · Reply · More · 26 Oct 2015
Amirah Muh'd
Tn
Like · React · Reply · More · 26 Oct 2015
Ibrahim Ubali
GD
Like · React · Reply · More · 26 Oct 2015
Maryam Abdul
Tnx
Like · React · Reply · More · 26 Oct 2015
Usman Aliyu Taller
Allah ya kara basira
Like · React · Reply · More · 26 Oct 2015
Ahmad Sabo
Yayi kyau
Like · React · Reply · More · 26 Oct 2015
Abubakar Ibrahim
good
Like · React · Reply · More · 26 Oct 2015
Balkisu Muhammad Bashir Bashir

Free Mode See Photos
Facebook logo
Go To Home
Jamila Umar Tanko Books
DAME AKE ADO.. 4**20
Chapter 44 · 0% Book details