← Book details Dame Ake Ado Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 49

Sashe 5

Dame Ake Ado Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

3⃣0⃣ Malam sulaiman yace to yaya koharyanzu sharri ake miki eye? Mijinta ya amshe don Allah yaya kayi hakuri kuskurene akasamu kuskuren gidanku nace kuskuren gidanku tun yaro nan yana wata guda matarka ke cutar dashi yanzu kuma abin yanzu kuma abinda zata koma yi kenan idan kinkwantar da hankalinki watarana zan sanarwa Ahmad wacece mahaifiyarsa kodon yadinga yimata Addu.a ma amma sai sanda ya mallaki hankalin kanshi yatara iyali yasami wadanda zasu debemasa kewar danginsa amman ayanzu banshirya sanardashiba don banason hargitsa masa rayuwa yakasa karatu da.anfanar rayuwarsa idan kuma bazaki daina ba zan saida gidan mukoma haya kowa ma yahuta don daki salwantarda rayuwa Ahmad gwara na kare rayuwata ahaya har Abada kana jina yanuna jibirilu kaine mijinta banason jin makamanciyar wannan magana a gidan don Allah yaya kayi hakuri wallahi tadaina insha Allah baisaurareshiba yakalli deeje yace maza wuce mutafi duk sanda yakuma sanardake irin wannan maganar datafito daga bakin Lami kisanar dani nikuma za.aga hukunci dazanyi wlh suka wuce suka fice Lami tabisuda harara tanafadin aikin banza ko kunya bayaji mace tasakoshi agaba yazo yana jaraba kaikuma takalli mijinta awulakance saiwani rawar jiki kake kana bashi hkr yana kara kumbura to idan ancemasa shege shin karya akayi? Yanada uban tsinanne dan mahaukaciya insha Allahu sainayi Ajalinsu aitsintacciyar mage bata mage yau tundasafe gidan babu dadi gurin samarin gidan dasuka fara mallakar hankalinsu domin tunsafe Ummansu batada lfy A Iyakacin shekarun Ahmad sha ukku da sani shabiyar da Auwalu shabakwai rabi.u shabiyu sunfahimci nakuda ce takeyi tunsafe yan uwan maman nasu mata keshige da fice anyi su tafi makarntar boko sunkasa zuwa alokacin Auwalu yanada shekar karshe sani yana aji hudu Ahmad yana aji daya hakama Rabi.u dayake kusan tard akemusu komai donsun tashi kamar yanbiyu cankamar daga sama suka farajin kukan jariri suka mimmike a rude suna lekawa amman sun kasa fita sunajiran Abasu izini saida aka kammala gyara uwar dajaririyata sannan akwala musu kira har rige rigen fita sukeyi ganin Umman tasu tana zaune akan filo afalo kamar ba ita ce tahaihu ba tayi kyau sai kamshin turaren wuta ketashi suna shiga ta washe baki cike da farinciki tana dariya inna balkisu kanwar tace tace Albishirinku samarin umma Atare sukace goro inna tayi dariya tanafadin yara saikunbani tunda nayi muku albishir yar budurwa da.aka haifa muku wacce kuke marmari amakota sasuka saka ihu atare saida umma ta kwabesu sannan suka natsu suka dinga amsar yarinyar suna kallo duk wanda ya.amsheta baison baiwa dan uwansa saboda kyan yarinyar Ahmad kam kamar jira yake su fito yakwasa dagudu yayi gurin Abokinsa musa yama manta shaf yana makaranta domin yanaimasa gorin kanne mata shi guda biyu yake dasu Raliya yarsheka shidda da Amina yar shekara ukku kofada suke saiyayi masa gori don haka yaga yashiga da ihunsa ko sallama babu yana fadin musa musa zokaga kanwata nima yau Ummanmu tahaifa mana mace mekyau datafi yan gidanku..... Yatsaya turus cike da tsoro sanda lami tafito daga daki tana muzurai kamar zata cinyeshi danye cikin tace shege meyakawoka gidanmu tsinanne yatsaya jikinsa yana kyarma bakinsa yana rawa yace daman..... Daman um Ummarmu ce tahaifi diya mace shine nazo nagayamasa takara dokamasa tsawa kaitafican banza shege ummanku ko ko ummansu kana murna anhaifi mace agidan wasu ko shashasha da baisan ko shi waye ba shege 3⃣2⃣ fice kabani guri kuma kaje kasanar da uwar rikon naka inci ubanka shege yajuya yafice dasauri jikinsa yana rawa yana jujjuya maganganunta aransa yakasa fahimtar abinda take nufi sukaci karo da musa azaure yakalleshh yana fadin Ashe ummanku tahaifi mace yanzu rabi.u yake gayamin Awaje yadaure yayi yar dariya ainashiga nagayama banganka ba dokin yarbudurwa yamantardashi Abinda innar musa tayi masa Ranar da hjy Amina tazo barka ranar kwana biyar da haihuwa sanda zata tafi mlm sulaiman yashigo dakayan lambu masu yawan gaske dayake sana.arshi kenan suyake saidawa kasuwar yankaba shagone dashi babba yasamya akadibarmata mai yawa tace yabarshi yace saita tafi dashi saidai motar haya tazo gidan domin motarta tana wurin gyara Ahmad yadaukar mata kayan yakaimata bakin titi suna tafe suna hirar makarantarsu dasauran Abubuwa saiyace mata Anti daman inason Intambayeki wani abu tatattara hankalinta agurinsa tace masa Uhum inajinka yagyara kayan dake kansa yace wai meye shege da Uwar riko kuma? Hjy Amina taja wani wawan birki tatsaya cike datashin hankali tace kai waye yake gayama wannan maganar badai ummar kaba ko ganin tarude yanda ummansa tayi idan yasanar mata yasanya gabanshi faduwa dan Allah kada kigayawa ummana zatamini fada daman Innarsu musa ce take gayamini kuma canake wani abune mai Amfani shine nake tambaya tayi ajiyar zuciya don zatonta deeje kefada masa haka tace lallai ta cika munafuka tunda take nuna batason kowa yanuna masa ba itace tahaifeshi ba amman duk da haka har lokacin ranta abace yake ta daure tace Agaban ummarka take gayamaka haka kuma yagirgiza kai yana fadin a.a saidai idan nashiga gidanta kuma ummana ma tahanani shiga ranar suna yarinya taci suna Asma.u sunan da deeje kenacin idantahaifi mace asanya mata saboda kaunarta ga mahaukaciya babar Ahmad tun washe garin suna tafara kiranta da ma'u kwanakinsu goma da haihuwa Hjy Amina tayomusu Asubanci sundan tsorata daganinta dasassafe amman ganin tanata wasa da dariya dayara yasanya suka fahimci ba wani abu ne yafaruba saida yaran suka wuce makaranta sannan suka kule adaki aka kara gaisawa suka nutsu sunajiran abinda ketafe da ita tagyara zama tace tabbas kunzama iyaye nagari masu rikon Amana kuma kuncancanci kuyi rainon kowane irin da banzo amatsayin shugabar gidan rainon yara ba domin nayi ritaya saidai nazo amatsayin inakaunarku dason danku Ahmad inafatar idan nafadamuku dalilin dayasa nakeson amsarsa bazaku bata rankuba tunda tafara magana suke kallonta jintazo wannan gaba yasanya deeje mikewa tana fadin tafdi jam ai wlh bazai yiwu ba koshugaban kasa bai isa ya.amshi Ahmad ahannunaba clkin matukar tashin hankali da kuka take maganar shikanshi malam din yakadu dayake namijine yasanya yadanyi karfin hali Yakwantar da kai yanafadin Adokar daukar yara agidan daman tanuna akwai wani lokaci da ake karbar yaro daga iyayen rainonsa ba.asanar damuba ko kuma rainonmu kikaraina kinaganin kinfimu iya raino hajiya takula dayanda suka shiga Rudu daman kuma tayi tunani haka zata faru dantasan yanda suke matukar son yaron takwantarda murya tana fadin kufahimci kamar yadda nasar da ku banzo da sunanan ma.aikaciya ba saidai yar uwa agurinku Ahmad bashida iyayen dasuka fiku saidai inason na rikeshi nawani lokacine har zuwa sanda zai iya daukar kowacce irin magana akwakwalwasa nasan kun san halin matar can Lami kumasha jin irin rigimar da kuke yi da ita akan yaron to abinnata yakiyin sauki donhaka mezaihana kubani aronsa haryagama Karatunsa na University insha Allah sannan nadawomuku dashi gabadaya suka sauka daga kan fushin nasu dansunsan inda maganarta tasanya gaba donhaka sungano magana tafimtar juna takawota mlm yace shin wani abune yafaru takwashe duk yanda sukayi da Ahmad tasanar dasu sanda zai rakata tahau mota sai deeje tasanya kuka tana fadin Ahaf ainasha gayawa mlm maganar nan matarnan batada mutunci wlh bazan yadda ba Hajiya kiyi hakuri wlh bazan iya rabuwa da Ahmad ba sai inmutuwa ce tarabamu kifahimci Abinda nake nufi Deeje bawai zankwacemiki Ahmad bane dawata manufa hjy Amina tafada da lallashi ganin yanda duk Deejan tabirkice mata mlm ne ya raba gardamar dafadin ke hajiya kiyi hakuri dan wlh rabamu da Ahmad babbar matsalane sannan hakan ma zai iya tona Asirin dakike son Rufewa indai lami ce matsala to zanyi maganinta ayau ba sai gobe ba dakyar suka shawo kanta ta amince zata barshi amman dole tace taza yiwa Lami kashedi da barazana don haka tare suka shiga gidan Lami da ita lami tamike jiki yana rawa tashimfida musu tabarma dan Allah yayita datsoron Hukuma tasan tsaf za.a iya daureta hajiya ce tafara magana cikin bacin rai kinfi kowa sanin laifinki bawai rarrashinki nazo yi ko rokon kiba a.a umurni ne nake baki abinda kikayiwa yaron nan yasarnar damu cikin rawar murya tace wai menayi mlm sulaiman ya yunkura da bacin rai zaiyi magana hajiya Amina datakatar dashi takalli lami tana fadin Kinmance sanda yashigo gayawa abonkinsa musa haihuwa abinda kikace to zakiyi bayani agaban hukuma tunda tunaninki rashin mutunci saita mike tsaye Hankali jibirilu yatashi yamike dasauri yana fadin a.ah hajiya baza.ayi hakaba tabbas tayi kuskure ayimata afuwa dan Allah yaya kasanya baki Lami kuwa tuni tafashe dakuka tagigice mlm sulaiman yayi dariya aransa yana fadin fitsarar riyar banza saida suka wanasu sannan tayadda tajanye sanarda hukumar yansanda wannan tasanya tadaina kiran Ahmad da shege koda sunhadu ahanya bata kyarar sa saidan harara kawai gabaki daya yaran sundauki soyayyar su sundora kan ma.u shekarunta biyar akasanxata aprimary saidai kullum sai dai kullum sai anyi dambe da ita kamar dage yawanfadan dasukeyi da raliya yasanya ummansu tayimasa kashedi akanta don kullum Dan kullum Lami ahanyar kawo kara take tayita zage zage da gore gore kalala dole tasanya yadaina kulasu Rayuwa yin Allah ayanzu haka Ahmad yana BUK takano inda yake karatunsa akan computar science Sani kam diploma yayi anan FCE sai yayi sa.a yasamu yasamu aiki awani kamfani maizaman kansa shikuwa Auwalu makarantar aiki tsafta yayi HND yabude chemist anan jikin gidansu yakuma samu aiki a temprary rabi u kam yanbokone nahakika ma.u kam ana aji daya a secondary school saikara firirita ake da iyayi da gwalli tafi kowa kokari a ajinsu gaba daya kai harma acikin tsaran ajinta itace kedaukar na daya wannan yake karamata soyuwa awurin yayyanta kafin ummansu ko babanta yayimata abu daya sunmata goma dominshi idan yatashi saiya hada dasu Raliya danhaka tafisu komai Raliya datake ganin itace budurwa dayadace tayi kwalliya sai taga ma.u tafita dawani yammaci lokacin ma.u tadawo hutu domin makarantar kwana take tataso daga islamiyya tana rike da kur.ani tahango lariya taci kwalliya tanufi shagon sisko wani dangayene a Unguwartasu da inmace kekulasu ake ganinta mara kamunkai dan haka tanaganin Raliya tashiga shagon sisko jikinta yadauki rawa hankalinta baikara tashiba saida taga saida ta hango sisko yadan leko yakalli gabas da yamma sannan yaja kofar shagon nasa dasauri ya kulle tayi dum dum cike da tsoro da fargaba tayi hanyar gidansu dasauri tasanarwa da yayyanta tayi sa.a ta tadda Ahmad da musa akofar gida zaune suna hira jikinta yana rawa idonta nazubda hawaye tanufesu Ahmad ne ya farga da ita yakalleta da mamaki yana fadin yadai ma.un baba lfy cikin
Chapter 5 · 0% Book details