← Book details Dame Ake Ado Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 49

Sashe 22

Dame Ake Ado Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read

·
Adama Abdulkarim Kiyawa
Mungode Allah ya kara basira thanks
Like · React · Reply · More · 20 Aug 2018
Adama Abdulkarim Kiyawa
Masha allah
Like · React · Reply · More · 20 Aug 2018
Atika A Umar
thank you so much
Like · React · Reply · More · 24 Apr 2018
Faisal Sa'ad Isma'il
Mun gode
Like · React · Reply · More · 29 Apr 2015
Azinatu Umar
TNX
Like · React · Reply · More · 29 Apr 2015
Mujaheed Ummi Ummi Mujaheed
dai dai kenan
Like · React · Reply · More · 29 Apr 2015
Fatima M Bello
Mun gode
Like · React · Reply · More · 29 Apr 2015
Ra'idatu El Kabeer
Tnx
Like · React · Reply · More · 29 Apr 2015
Maryam Saleh
tnx u
Like · React · Reply · More · 29 Apr 2015
Mujaheed Ummi Ummi Mujaheed
dai dai
Like · React · Reply · More · 29 Apr 2015
View more comments…
Free Mode See Photos
Facebook logo
Go To Home
Jamila Umar Tanko Books
DAME AKE ADO part 15.
Umma kam tana bayan ra ayin Ahmad amma tagaza cewa komai Don kada malam yayi zaton hada baki sukayi Amman acikin ranta tana addu'ar Allah yasa ya amince din hakan ne kadai mafita malam yace tau shikenan tunda kana ganin hakanne mafita baijima agidanba yayi sallama dasu domin hankalinsa yanakan ma'u daya baro akwai yankallo agidan yabarsu dan haka yatada babur dinsa yanufi gida yana isa yahango kofar soron ansakayota saidai wurin bakikirin kasan cewar andauke wutar nepa yakafe babur dinsa agefe yasauka domin yatura kofar yashiga yatabbatar babu wani abu akan hanya cikin soro saida ya isa cikin soro yafara kokarin kunna yar cocilan din dake hannusa dai dai lokacin dayaji wata uwar kara yarude yafara kallon inda karar kefitowa acikin soron ne daga gefe kuma muryan ma'u ce cikin sauri yace ke menene ma'u nine Ahmad cocilan din dake hannunasa wacce yake kokarin kunnawa tafadi saboda damkar datayi masa tana sheshshekar kuka kamar zata shide cikin firgita yace ke menene meyafaru tana kankame ajikinsa take fadin wlh kamar tafiya akeyi acikin gidan nakasa zauna..........ina A'ilon take? Anadauke wuta kanenta sale yazo kiranta nayita magiyar tatsaya tace wai dukanta za ayi shine nabuya abayan gado saina dinga jin tafiya nagudo nadawo soro naboye cikin kuka take bayanin yakasa cewa komai domin rikon datayimasa tasaukarmai kasala dawani iri shauki da kyar yadake yace shikenan sakeni nashigo da babur dina babu komai tsorata kawai kikayi taki sakinsa takuma kiyin magana har lokacin jikinta rawa yake yakara kwantar da murya yace bari badauko cocilan din tadan sakeshi amman tana gabansa yasunkuya yafara laluban cocilan harya samu yakunna yahaske fuskar ta dariya takamashi ganin tayi miyau da majina yakauda da kai yana dariya Ho ma'u hankalinki saike bari nashigo da babur din nifa tsoro nakeji Allah kuwa yaya yamikamata tocin rike harnashigo dashi haka tatsaya badon tasoba haryashiga da babur din yashige gaba tana biye dashi abaya suna shiga aka kawo wuta yakalleta yana rike da babur din haryanzu yanayinata dariaya togashinan babu komai agidan matsoracya kawai itadai batace komai komaiba yadauki buta yanufi bandaki saita tashi dasauri harda dangudunta yawaigo dasauri malama bandaki zakibini kuma A a tafada dasauri yakuma fashewa dadariya kinga dun Allah kikwantar da hankalinki kiyita addu'a babu komai bari nafito dahaka yasamu yashiga bandaki yanaci gaba da dariya a zuciyarshi daren ranar tana gado shiyana kasa kwance takundundune kamar za ashigo adauketa ma'u akwai kurciya da shiririta yanason yayi maganar tafiyarsa da ita amman yanda take afirgice dinnan yasan bazaisami komai agareta ba don haka ya kyaleta dasafe baijima dafitaba yadawo domin manaja gidan man yace sudawo gida kowa yayi shirin tafiya gobe sannan yadan basu kudaden dakowa zaibarwa iyalinsa ma'u anmike kan kujera anata karatu Allah yasanya takammala aikinta gabadaya tajiyo sallamarsa tadago da mamaki tana kallon kofar dakin tamike dasauri taleko shine din kuwa damamaki tace yaya Ahmad yauhar kadawo dawuri haka
1⃣1⃣ DAME AKE ADO 3 yakada kai banyi aikiba ne nadawo nayi shirin tafiya ne tafiya kuma ta tambaya dasauri kinga shiga ciki kizauna nayi miki bayani babu musu takoma tazauna shima yasami guri yazauna yafaramata bayanin dalilin tafiyar haryakai karashen bayanin tayi shiru dadamuwa kamar zata fasa kuka amman yaya bazan iya zama nikadai agidannanba katafi dani can dan Allah yakauda kai A a bazanje dakeba anan zaki zauna kefa matar Aurece baikamata kidinga yawo ko inaba abinda bajimawa zanyiba darana saikiyita wasa dasu A'ilo idankuma dare yayi saiki kulle gidan kisanya sakata babu wanda Zaishigo ai tadafe kirji dan Allah yaya kayi hakuri wlh bazan iya kwana nikadaiba saidai idan kayarda nadinga zuwa gidansu mairon gidan kasa nakwana yabata ran wasa gidan kuma fa yakwana shikadai babu kowa banyardaba gaskiya dole kizauna kedaya tayi shiru tarasa mezatace ma amman dai idonta yafara zubo da hawaye dasauri yamike yanafadin lalala kada kiyi kuka yar Amaryata tsokanarki nakeyi tashima kishirya kayanki mutafi gidansu umma acanzaki zauna tamike tadaka wani uban tsalle tana ihu yabude baki yana kallonta lallai yariya zakija afasa tagimtse murnar yi hkr yaya nadaina bari naje nafara hada kayana ko ajikinta batajin komai akan tafiyarsa domin damar komawarta ga ummanta tafi komai yimata dadi yana kallonta tafice yana kallonta yafada kujera ya lumshe ido baison rabuwa da matar tashi ayanzu zaman dasukayi nawatannin nan yashaku da ita fiye da tsammani kobabu komai yakaso sokancinta danya dinga cindariya kawai amman yaya ya iya rabuwa tazama dole Amotar haya taxi suka tafi domin kayan dayayiwa su umma siyayya nakayan abinci da kuma kayan sawar ma'u sunada yawa ma'u kuwa murna takeyi kamar zata shide shidai kawai yake ransa babu dadi Acan gidansu umma ma haka tadinga murna tanajin kamar za asanyata agidan Aljanna umma tana kallonta tana murmushi shikuma jiyake kamar kada yatafi Anan yaci abinci har wajen karfe goma baibar gidanba saida malam yayimasa magana Ahmadu yakamata kaje kakwanta haka domin samun damar tashi dawuri tunda kace sammako zakuyi? Yayi shiru dadamuwa saiyakejin kamar yarabu dasu kenan har abada faduwar gabanshi takaru idonshi yataru da kwalla malam yayi murmushi nason basar dashi Ahmad saikace wani karamin yaro don Allah ka kwantar da hankalinka sai alokacin jikin ma'u yayi sanyi tazubawa Ahmad ido wanda kansa ke kasa itakanta umma kauda kanta tayi gefe don batason ganin fuskar dan nata Cikin rawar baki Ahmad yace naji gabana inazaton babu Alkhairi acikin acikin tafiyar nan tawa gwara nafasa nasamu wani aikin kul nakoma jin wannan maganar Ahmadu tunranda kafadamin maganar tafiyar nan nasanarda yan uwanka mukayita Addu'a saikuma da aski yazo gaban goshi sannan zakace kafasa ban amince dahakan ba sam kaje kayiwa mamanka hajiya Amina sallama tukunna naje dagacan mukayo nan tace agaiaheku muna amsawa maza tashi kawuce ya mike yana kallon ummansa da har lokacin kanta yana kallon wani sashin yace umma zanwuce sai alokacin tawaigo idonta yacika da kwalla tace Allah yakiyaye hanya kakula da kanka Ahmad kakula da Addininka da matsayinka na musulunci aduk inda katsinci kanka Allah yayimaka Albarka kalmarta ta karshe tafi komai dadi agareshi yanzu da agidan marayu yatashi waye zaidinga saiyamasa Albarka kamar haka yayi kokarin goge kwallar data zubomasa yanafadin Amin Umma nagode baba natafi Allah yatsare yakiyaye madinga gaisawa ko awayar yayanka ne
1⃣2⃣ DAME AKE ADO 3 Ma'u tanazaune tamkar andasata gabadaya murnarta takoma ciki saizare idonta takeyi saiyanzu takejin ciwon tafiyar yayanta Ahmad kalamanshi sunsanyayar mata dajiki har kwalla yacika idonta Umma tadubeta tace bazakije kuyi sallama bane? Takalleshi dasauri maganar umma tasanyata mikewa dasauri babu shiri donbin bayan Ahmad dayafice dasauri yana goge idonsa cikin gaggawa tabishi donganin yanufi soro kaitsaye dasauri yaya Ahmad takwalla masa kira sanda ta isa soron taga zaifice yatsaya gami da waigowa da sauri yakalleta ma'u yaya akayine? Cikin dakiya dakokarin boye damuwa yake maganar yaya bamuyi sallama ba zaka tafi naga kamar ranka yabaci yaya dan Allah kayi hakuri idan nayimaka laifi yayi murmushi dajindadi lallai ma'un shi tafara samun hankali da natsuwa ya isa kusa da ita yariko hannunta yanajin kamar yarungumota jikinsa amman gudun abinda zaifaru yasa yadake cikin dakiyar zuciya yace ma'u bakiyiman komaiba amman inajin kewa dakadaicin rabuwa daku naga kamar murna kikeyi domin kidawo gidansu Umma ko? Tasunkuyarda kai kunya tarufeta amman saita girgiza kanta alamar a a bahakabane ba yakura mata ido cikin hasken dayaratso soron yanaci gaba da magana kidinga yiman addu a ma'u naso kamin natafi nasaimiki waya amman banida kudi kudin danasamu nayiwa su umma siyayya nasanyamiki wasu kudi cikin kayanki idan kina bukatar wani abu kidinga siya kada kitambayi umma ko baba kinjiko tadaga kai alamar to yajanye hannunsa daga cikin nata yanadan ja dabaya yace sainadawo ma'u yajuya dasauri yafice ma'u kurawa kofar ido kamar katabishi saiyanzu takejin kaunar mijin nata haka takoma gidan babu kwari balle karsashi ajikinta Gasu Ahmad saidare suka isa garin legas kaitsaye gidan dazasu sauka suka isa dayake amotar kamfaninsu suka tafi gidane irin ginin legas amma babu laifi yanada kyau kowa da dakinsa daban akabashi dakyar suka iya cin dan abinci suka kwanta baccin gajiya washe gari kuma dasafe akakwashesu amotar kamfani akakaisu sabon gidan man maisuna YAN LEMA PETROLEUM & 10 dayake duk sunan gidajen man nasa dayane suntarar da ma aikatan gurin wanda aranar zasu fara aiki babban gidan mai yagina wanda yafi nacan kasancewar shikadai ne dashi alegas kuma nafarko ajahohin kudu kuma ance shine nafarko dayafara ginawa dayake kuma yanada kishin jama arsa HAUSAWA kusan kaso sittin naginin duk hausawane saisauran yarbawa basusha wahalar fara aikinba kasancewar anrage kudin litar dakaso biyu (2%) cikin (100%) saboda gidan man sabone haka yasanya akayita samun masu siya Awannan ranar dakyar Ahmad yasamu dan lokacin yin tunanin ummanshi da ma'unsa kida yakema lokacin dayana aikin mayakan tunodasu jefi jefi kuma aduk yayin dayatuno dasu saiyayi murmushi
1⃣3⃣ DAME AKE ADO 3 KWANAKI sukai tazuwa suna wucewa zuciyoyo nakara shiga cikin damuwa Awannan lokaci ma'u takara fahimta meye Aure meye miji domin yayi nisa acikin karance karance sannan Umma ta ajiye kunya tanayimata bayanin aure meya kunsa menene alfanunsa wannan yake karasanya takara son mijinta idantayi kwance agado saitayita tunaninsa burinta baiwuce yadawoba musamman lokaci da hajiya Amina tazo ta taddata tana karatun littafi tasayomata jaka guda tace ayitayi ananma tasamu abubuwan karuwa dayawa takaicinta daya tunda Ahmad yatafi bata tabakoda jin muryansa ba kullun sai dai yaya Auwalu ko yaya sani yazo yabasu labari yace sunyi waya dashi sungaisa tanaso tace abatashi idanyakira wayar amman vazata iyaba sam sukuma sunkasa karar subata din Ahaka har watanni biyar suka cika zuwa lokacin ma'u takoyi abubuwa masu dama yacika tazama budurwa domin tacika shekaru sha shida kenan gashi kullum umma saita bata kunun daka irin na MUTANEN NIJAR da tukudi tunbata son sha haryazame mata jiki dukkan halittar ta takammala fitowa tazama CIKAKKIYAR MACE Idan tatuno abinda tayiwa mijinta abaya saitayita dariya daganin wautar kanta gaskiya Ahmad tayi kokarin zama da ita shekara daya dawata bakwai amman baiyimata komaiba tatabbatr yayan nata namatukar kaunarta yanzu saidai abinda kedamunta baiwuce rashin dawowarsaba kullum sai umma tayi mita domin ita kanta tagaji amman sai yaya Auwalu yace ba abasu damar dawowabane saidai duk karshen wata yana aikomusu da sako wannan abin shine yake farantawa malam rai kwarai dagaske domin ayanzu kobaifita kasuwaba bairasa abinda yasanya abakinsa Albarkacin darajar iyaye Ahmad yana cikin tsananin damuwa datakura saboda rashin iyalinsa da iyayensa Ayanda Alhaji nura yayi musu Alkawari watanni ukku zasuyi amman gashi harsun shiga watanni shida kuma watan yana neman karewa ba acemusu komaiba hankalinsa duk yatashi haryarasa abinda zaice agayama ummansa da ma'unsa amman dai yasan sunacikin damuwa kwarai da gaske lokacin dasuka cika watanni bakwai yagama fusata baijin komai bayan ya isa ga ahalinsa don haka lokacin da Alhaji nura ya iso gari donya duba yadda abubuwa suke tafiya Ahmad yaji kamar dukkan matsalarsa takare dan haka lokacin da yazauna mitin dasu yakudiri aniyar fadin abinda keransa bayan yayi yabo dajindadin yadda akasamu cigaba da abinda ake bukata ga gidan man yayimusu albishir dasamun karin albashi maitsoka murna dajindadi yacikasu amman banda Ahmad domin yawanci wadanda sukazo kamar basu damu da iyalinsuba dayawa sunsaki jiki suna mu amalarsu harma dasu ajiye daduro! Bayan Alhaji nura yagama bayaninsa Ahmad yadaga hannu yana fadin idan yallabai yabani dama inada maganar da zanyi gabadaya kallo yakoma wurinsa abokinsa isuhu haryadan zunguresa alamar kada yayi magana domin yasan abinda zaice saboda kullum saiyayi masu korafi amman Ahmad baikulashiba Alhaji yakada kai kanada damar yin magana Ahmad yamike tsaye yafara koro bayani yallabai kamar yanda kafada abaya kafin muzo garin nan kace watanni ukku kacal zamuyi amman gashi harmunshiga wata na bakwai kuma watan yanagab da karewa amman babu labarin tafiya gida shine nakeson ayiman bayanin yanda abin yake Rufe mana baki mara kunya kaikadai kake da iyali kobakin magana bakaganin wasu neman aiki sukeyi sun rasa idon su arufe manajan gidan man yafadi haka bayan yakatseshi cikin tsananin bacin rai da masifa Ahmad yace hakane kasan babu wanda ya isa yabaiwa wani aiki idan ba Allah yakaddara ya aminceba
Abdullahi yusuf maitama
09034598552
@whatsapp
Chapter 22 · 0% Book details