← Book details Dame Ake Ado Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 49

Sashe 3

Dame Ake Ado Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

shidin dainakeso idan kuma kaine sama dani sainaji marar kunyar banza ..........2⃣3⃣ irin naka duk wani abu dazaka aikata na Alkhairi saiyazamana kaidashi kake gaba wannan yaron kasan iyakacin baiwar da Allah yayimasa to tsaya nagayamaka daga yau yashiga cikin 'ya'yana zan kuma rubuta wasiyya ko bayan na mutu araba dukiyata kashi shidda Abashi kaso daya don Allah baihalasta Wani yagaji wani bane ba danace yagajeni jibrilu yayi shiru cike da takaici don yasan halin yayan nasa akwai fada idan kataboshi danhaka yamike sumi sumi yang fadin Aishike nan nidaman inaguje maka illar da akace zama da shege yana kawowa ne inji ubanwa aihar yau kakasa kawo mini hadisi ko ayar datace hakan nakuma gayamaka kadaina Ambaton dana Ahmad dashege kajiko yakarasa ficewa yana gunguni babu yanda zaiyi 2⃣4⃣ malam sulaiman yacigaba dafada sokon yaro sai mace ta huroka kazo kana yiwa mutane fiffika daga ganinka wannan bara.ayinka bane ba matarce taroshi shakiyiya kawai deeje takwantar da murya tana fadin karabudashi Lami kam saidai Ayimata Addu.a matar da yaran gidan bata bariba balle wannan mudai Allah yarayamana shi cikin Albarka yakoma gida cikin borin kunya yatadda lami tsaye tana jiransa yana shiga tatareshi yaya kukayi dashi? Yasamu guri yazauna yana dafe kunci yayi tsaki yana fadin bakiji yanda yabalbaleni dafadaba kamar wani ubana harfa cewa yayi bazairike dana kona wani dangi sai wannan shegen ke har doka yakafa min waina kiransa dashege ma tayamutsa fuska tana fadin maganinka kenan mara zuciya saunawa nake gayamaka kadaure kayi gidan kanka muhuta da mulkin mallaka dan wannan dakin biyun dayabamu ke rudinsa dayasanan kana da iko agidan aida baiyimaka haba saikayitayi kada ka mallaki nakanka kayita zaman karoro 2⃣5⃣ Ahmad yataso yaro maicike dakwarjini da hikima da basira wanda kowa ke kauna. Duk inda yazauna zakaga ana sonsa iyayensa suna nuna masa gata kullum yana cikin yan uwansa suje islamiyya da dare kuma suzauna kofar gida saida rake ko mangwaro saidai tunda yatashi ya kula da tsangwama da kyarar da Lami da mijinta ke masa ga wani suna dasuke yawaita kiransa dashi shege amman yakula har sauran yayyansa da kanne Lami bata kauna saidai sanda yayi shekaru ukku yagano azabarta ko ahanya suka hadu saita rankwasheshi musane abokinsa a gidan kuma sa.ansa tasu tazo daya sauda yakanbishi gidansu wasa kamar yanda shima yake biyoshi amman duk sanda yabishi saita azabtar da shi har wuta ta tabawatsomasa wata rana kuwa ta kulle abandaki wai wuni guda mamanshi na nema har kuka tafarayi tadinga zagaye unguwa sai gab da magriba ta hankodoshi yasha kuka majina damiyau lokacin yanada shekaru biyar sanda mamansa tagansa tarungumeshi tanafadin 2⃣6⃣ Ahmad dina inakashiga kaida nasanka bakada yawo cikin muryan kuka yake fadamta innarsu musa ce takulle ni abandaki wai saina shaki kashi namutu narasa abinda nayimata ta tsaneni Ummata kigayawa baba yasake mana gida mana tausayin yaron yakamata tasha bala.i da Lami akan yaron tun yana da wata ukku da Auwalu yashiga dashi tashaka masa ruwan kumfa ahanci har kusan dambe sukayi tundaga tadaina baiwa kowa danta ga tirtsetsen cikin haka zata goya abinta haryayi shekara ukku saita ajiye kaninsa Rabi.u tasungumeshi abaya don haka rigimar tayi sauki yanzu kuwa yawuce goyo duk irin tsakanin mlm dayimusu takiji hakanan dai rayuwa taci gaba da gudana cikin wahala da azabar Lami shidai jibiril baya dukansa Amman baya ko kallonsa don yace masa baffa saiya dokamasa harara yau ummansa tadawo awo abakin Asibiti saita siyowa kowa kayan sanyi da mlm yabata sallahu duk tashi tafi kyau don hoton dan bal din nanne maradona daman shi yana da son bal don haka yasuri tashi yayi waje da gudu kai tsaye gidan jibril yashiga yana kwalawa abokinsa musa kira musa yafito daga daki aguje mahaifiyarsa na kwalamasa kira Amman baitsayaba saida yadangana datsakar gida inda Abokinsa Ahmad ketsaye cikin farin ciki da dariya Ahmad ke daga masa rigar yana fadin kalli yaro babanmu ne yabaiwa umma kudi tasiyowomuna kalli harda maradona ajiki shugaban yan kwallo duk randa zamuje filin bal da ita zani kaikuwa bakada ita musa yatsaya turus cike da takaici saiya saki kuka mahaifiyarsa tafito daga daki dasaurinta tana fadin tsinanne shege dukanka yayi ko? Yagirgiza kai yana fadi a.a badukana yayiba riga babansu yasiyo masa maihoton maradona zai dinga yin ado yanafina kyau nadaina zuwa filin kwalloma adaki zandinga zamana jikin Ahmad yayi sanyi yakalli abokinsa yamika masa rigar yana fadin kada kadaina zuwa don Allah garigar tawa kadinga Ado da ita yamika masa saidai tuni mahaifiyarsa ta warce tana fadin Banza soko aibada riga ake ado ba kaga wannan tanuna rigar ana saidata akasuwa da uba ake ado wanda shikuma ba.asaidashi akasuwa kasha kuriminka wata rana ko rigar gwal da zinare yasanya yafita saiya tsani kanshi don baida rigar Ainihi ta mutunci tawurgawa Ahmad rigar tanacigaba da fadin dauki tsiyarka kawuce shegen banza watarana zakagane Abinda nake nufi hankalin yaran gabadaya yatashi duk basu fahimci komai azance ba yakwasa da gudu ganin tayi kansa da ice gadan gadan saida ta kaishi har babban soro sannan takoma yanufi gidansu jikinsa sanyi kalau yana hawaye Ummansa tafito daga daki dazummar dora girkh taci karo dashi zaune shiru gabanta yafadi don tasan yarone mai kazar kazar da wasa tabbas bashida lfy takara dasauri tana kiran sunansa manya yaya na ganka anan zaune shiru meke damunka yadaga kai yana kallonta idonsa yakada yayi jajir saita kuma rudewa tace gayamini meyake damunka cikin shashshekar kuka yace innarsu musa ce takoroni don naje nunama musa rigar da babanmu yace kisiyomana tayi ajiyar zuciya wato dai bazaka daina shiga gidan nan ba kadaina kajiko yadagamata kai Alamar to sannan yace Amman idan musa yakwalamini kira indan leka amman kada nashi dakinta ko? Abin yaso bata dariya wata irin shakuwa ce tsakaninsa da musa wacce bazata iya rabasuba dan Allah ne yahadasu da daddare suna barbaje atsakar gida suna cin abinci cikin tsakiyar hasken farin wata tuwone da danyar kubewa wacce tasha kifi Ahmad yakai katuwar loma bakinsa yahidiye tadakyar yakalli Ummansu tasu yana fadin Umman wai meye shege ne? Gabanta ya yanke yafadi matuka tawaro idanu waje ........... Cike datashin hankali can kuma saitayi saurin dakewa takwantar da murya tace banace kadaina tambaya irin wannanba Ahmad meye Amfanin wannan tambayar inace a makaranta malaminku yace kudaina tambaya akan duk wani abu dabayada Amfani gabadaya duk tarude jikinta har rawa yake ganin haka yasanya shima hankalinsa yatashi don baya son yabatawa ummansa rai yace kiyi hkr umma nadaina daman innarsu musa ce naji kullum saitace mini shege canake ma suna ne Ashe magana ce mara kyau ma takuma Rudewa tace kadaina damuwa idan tace haka idan akace da mutum shege aiyayi wata gwaninta ne yayi dari.a yana fadin natuna har kika hanasu cewa hakan ko? Tace yauwa yarona ashe kagane ka daina damuwa idanta kuma cemaka kuma kada na kuma jin kalmar abankinka kada kuma ka tambaxi wani ko malaminmu tunda kaga nagaya kako yace to umma bazan kuma tambayaba sannan yacigaba dacin Abincinsa tayi wawiyar Ajiyar zuciya cike dafargaba saitaji duk Abinci yafita daga kanta magabadaya tabbas dole mijinta yadauki mataki akan wannan abin idan bahakaba saidai tabar gidan da yaranta dantayi Alkawarin har abada bazata gayawa Ahmad wayeshiba saboda hakama tunyana dansheka ukku tadaina kaishi gidan rainon yara shugabar makarantar ce kezuwa taganshi har gida har sanda tabar aikin agidan rainon yaran takanzo ganinsa saboda tana masifar sonsa itama hartadinga danasanin barinsa agurinsu din gashi babu damar ta amsheshi a lokacin dadaddare duk yaran sunyi bacci ta tashi maigidan nata wanda shima haryafayin bacci yatashi cike da mamaki da fargaba don tun dayamma yaga ranta abace nakula tunda maraice akwai wani Abu dakike boyemin to kinshiya fada kenan yanzu tafashe da kuka tana fadin aidazun mabakin gaya maka haka kawai ba sai don gudun kada yaransu ji Abinda zamu tattaunawa to wallah nagaji dazaman gidan nan na.amince kakamini haya da masifar da ake shirin kunno mini saita kara fashewa da kuka batunyau ba nake sanarda kai irin azabar da matar nan takeyiwa yaron nan Ahmad ba har Abin yakai nadaina sanarda kai toyau takai har Lami kenunuwa Ahmad shi shege ne bazan yadda ba Allah wannan neman masifa ne dason tozartani Hankalin mlm sulaiman yatashi yadinga fadin subhanallahi garin yaya hakan tafaru tasan kuma doka ce nasanya agidan nan tunba yauba ko mijinta nace yafadi wannan maganar zamuraba gari dashi 2⃣9⃣ DAME AKE ADO ....... ........... Dasassafe yatura yaran makanrata safe kamar yanda suka saba duk Ranar Assabar da lahadi da babu boko saisu tafi daukar darasi amasallacin Unguwar kaitsaye suka shiga gidan jibiril sunyi sa.a kuwa yaran gidan suma sunfice sai matar gidan zaune akan tabarma suna ta hira suna jin sallamar su mlm suka daga kaida mamaki dominsunsan baya shiga gidansu saita baci jibril yamike yana fadin A.a yayane sannu dazuwa zauna mana yadaga hannu yana fadin ba wannan takawoni ba gargadi nashigo yiwa matarka duk da nasan kasan duk abinda take aikatawa to wlh ahir dinta hawainiyarta takiyayi ramata Lami ta dafe kirji tana fadin nikam nashiga ukku nazama shara komai aka kwaso sai ayaba mini yanzu kuma nayi..... Rufemin baki marar kunya banza aikinfi kowa sani Abinda kikayi waike danbakida mutunci harkike tsare yaron nan Ahmadu kina masa habaici dole duk saiyasan shiba mune iyayensaba ko? Lailaha ilallahu nidin wlh sharri akemin yaushe nataba tareshi nagayamasa wannan maganar kuma? Yakalli deeje yana cigaba dafadin gayamata duk abinda tafadi tasan ya dawo kunnenmu deeje tamaimaita duk Abinda Ahmad yasanar da ita har shegen datake cemasa sai lami tayi wuki wuki babu kuma bakin magana dontasan tafada yanda kuma suka tsara sai take tunanin ko deejen taji nema
Chapter 3 · 0% Book details